< 2 Sarakuna 13 >
1 A shekara ta ashirin da uku ta Yowash ɗan Ahaziya, sarkin Yahuda, Yehoyahaz ɗan Yehu, ya zama sarkin Isra’ila a Samariya, ya kuwa yi mulki shekaru goma sha bakwai.
2 Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji ta wurin bin zunuban Yerobowam ɗan Nebat, wanda ya sa Isra’ila ta aikata, bai kuwa guje musu ba.
3 Saboda haka fushin Ubangiji ya ƙuna a kan Isra’ila, kuma da daɗewa ya sa su a ƙarƙashin ikon Hazayel sarkin Aram da Ben-Hadad ɗansa.
4 Sai Yehoyahaz ya nemi tagomashin Ubangiji, Ubangiji kuwa ya saurare shi, domin ya gan irin matsin da sarkin Aram yake yi wa Isra’ila.
5 Sai Ubangiji ya tā da mai ceto wa Isra’ila, suka kuma kuɓuta daga ikon Aram. Ta haka Isra’ilawa suka yi zama a gidajensu yadda suka yi a dā.
6 Sai dai ba su bar yin zunuban gidan Yerobowam ba, wanda ya sa Isra’ila ta aikata; suka ci gaba da yinsu. Haka ma, ginshiƙin Ashera ta kasance a tsaye a cikin Samariya.
7 Ba abin da ya rage na rundunar Yehoyahaz sai mahayan dawakai hamsin, kekunan yaƙi goma da kuma sojoji ƙasa dubu goma. Gama sarkin Aram ya hallaka sauran, ya kuma yi kaca-kaca da su kamar ƙura a masussuka.
8 Game da sauran ayyukan mulkin Yehoyahaz, dukan abubuwan da ya yi da kuma nasarorinsa, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Isra’ila.
9 Yehoyahaz ya huta da kakanninsa, aka binne shi a Samariya, Yehowash ɗansa kuma ya gāje shi.
10 A shekaru talatin da bakwai ta Yowash sarkin Yahuda, Yehowash ɗan Yehoyahaz ya zama sarkin Isra’ila a Samariya, ya kuma yi mulki shekaru goma sha shida.
11 Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji, bai juya ga barin zunuban Yerobowam ɗan Nebat ba, wanda ya sa Isra’ila ta aikata, ya ci gaba da yinsu.
12 Game da sauran ayyukan mulkin Yowash, da dukan abubuwan da ya yi, da kuma nasarorinsa, haɗe da yaƙin da ya yi da Amaziya sarkin Yahuda, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Isra’ila.
13 Yowash ya huta da kakanninsa, Yerobowam kuwa ya gāje shi. Aka binne Yehowash a Samariya tare da sarakunan Isra’ila.
14 To, Elisha ya kamu da ciwon da ya kashe shi. Yowash sarkin Isra’ila ya gangara don yă gan shi, ya kuma yi kuka dominsa. Ya yi kuka yana cewa, “Babana! Babana, keken yaƙin Isra’ila da mahayan dawakanta!”
15 Elisha ya ce wa Yehowash, “Ka samo baka da kibiyoyi,” ya kuwa yi haka.
16 Sai ya ce wa Yehowash sarkin Isra’ila, “Ka ɗauki baka a hannunka.” Da ya ɗauka, sai Elisha ya sa hannunsa a hannuwan sarki.
17 Ya ce masa, “Ka buɗe taga wajen gabas,” sai ya buɗe. Sai Elisha ya ce, “Ka harba!” Sai ya harba. Elisha ya ce, “Kibiyar nasara ta Ubangiji, kibiyar nasara a kan Aram! Za ka hallaka Arameyawa sarai a Afek.”
18 Sa’an nan ya ce, “Ka ɗauki kibiyoyi,” sai sarkin ya ɗauko. Sai Elisha ya ce, “Ka caki ƙasa.” Sai ya caka sau uku sa’an nan ya daina.
19 Sai mutumin Allah ya yi fushi da shi ya ce, “Da a ce ka caki ƙasar sau biyar ko shida; da za ka yi nasara a kan Aram ka kuma hallaka ta sarai. Amma yanzu za ka yi nasara a kanta sau uku ne kawai.”
20 Elisha ya mutu, aka kuma binne shi. To, mahara Mowabawa sun saba kawo hari a ƙasar Isra’ila a kowace bazara.
21 Wata rana yayinda waɗansu Isra’ilawa suke binne wani mutum, farat ɗaya sai ga mahara; saboda haka suka jefar da gawar mutumin a kabarin Elisha. Da gawar ta taɓa ƙasusuwan Elisha, sai mutumin ya farka, ya tashi ya tsaya da ƙafafunsa.
22 Hazayel sarkin Aram ya musguna wa Isra’ila a duk tsawon mulkin Yehoyahaz.
23 Amma Ubangiji ya nuna musu alheri, ya ji tausayinsu, ya kuma damu da su saboda alkawarinsa da Ibrahim, Ishaku da Yaƙub. Har yă zuwa yau bai yarda yă hallaka su ko yă shafe su daga gabansa ba.
24 Hazayel sarkin Aram ya mutu, sai Ben-Hadad ɗansa ya gāje shi.
25 Sa’an nan Yowash ya sāke ƙwato garuruwan da Ben-Hadad ya ci da yaƙi a hannun mahaifinsa Yehoyahaz. Sau uku Yehowash ya yi nasara a kansa, ta haka kuwa ya ƙwace garuruwan Isra’ilawa.