< 2 Yohanna 1 >

1 Dattijon nan, Zuwa ga uwargida zaɓaɓɓiya da kuma’ya’yanta, waɗanda nake ƙauna ƙwarai da gaske kuma ba ni kaɗai ba, amma har da dukan waɗanda suka san gaskiya.
The elder, to the chosen lady and her children, whom I love in truth; and not I only, but also all those who know the truth;
2 Muna ƙaunarku saboda gaskiyan nan, wadda take cikinmu za tă kuma kasance tare da mu har abada. (aiōn g165)
for the truth's sake, which remains in us, and it will be with us forever: (aiōn g165)
3 Alheri, jinƙai da kuma salama daga Allah Uba da kuma Yesu Kiristi, Ɗan Uba, su kasance tare da mu cikin gaskiya da ƙauna.
Grace, mercy, and peace will be with us, from God the Father, and from Jesus Christ, the Son of the Father, in truth and love.
4 Na yi farin ciki ƙwarai, da na sami waɗansu’ya’yanki suna tafiya cikin gaskiya, kamar yadda Uba ya umarce mu.
I rejoice greatly that I have found some of your children walking in truth, even as we have been commanded by the Father.
5 Yanzu kuma, uwargida ƙaunatacciya, ba sabon umarni nake rubuta miki ba sai dai wanda muke da shi tun farko. Ina roƙo cewa mu ƙaunaci juna.
And now I ask you, dear lady, not as though I wrote to you a new commandment, but that which we had from the beginning, that we love one another.
6 Ƙauna, ita ce mu yi biyayya ga umarnansa. Kamar yadda kuka ji tun da fari, umarninsa shi ne ku yi zaman ƙauna.
This is love, that we should walk according to his commandments. This is the commandment, even as you heard from the beginning, that you should walk in it.
7 Masu ruɗi da yawa, waɗanda ba su yarda da zuwan Yesu Kiristi cikin jiki ba, sun riga sun fito a duniya. Duk irin mutumin nan mai ruɗi ne kuma magabcin Kiristi.
For many deceivers have gone out into the world, those who do not confess that Jesus Christ came in the flesh. This is the deceiver and the antichrist.
8 Ku lura don kada ku yi hasarar aikin da kuka yi, sai dai ku sami cikakken lada.
Watch yourselves, that you do not lose the things which we have accomplished, but that you receive a full reward.
9 Duk mutumin da bai tsaya a kan koyarwar Kiristi ba, amma ya yi ƙari a kanta, mutumin nan ba shi da Allah. Amma wanda ya tsaya a kan koyarwar Kiristi, yana da Uban da kuma Ɗan.
Whoever goes on and does not remain in the teaching of Christ, does not have God. He who remains in the teaching, the same has both the Father and the Son.
10 Duk wanda ya zo wurinku bai kuma kawo koyarwan nan ba, kada ku karɓe shi a gidanku ko ku marabce shi.
If anyone comes to you, and does not bring this teaching, do not receive him into your house, and do not welcome him,
11 Duk wanda ya karɓe shi yana tarayya da mugun aikinsa ke nan.
for he who welcomes him participates in his evil works.
12 Ina da abubuwa da dama da zan rubuta muku, sai dai ba na so in yi amfani da takarda da inki in rubuta. A maimako, ina fata in ziyarce ku in kuma yi magana da ku fuska da fuska, domin farin cikinmu yă zama cikakke.
Having many things to write to you, I do not want to do so with paper and ink, but I hope to come to you, and to speak face to face, that our joy may be made full.
13 ’Ya’yan’yar’uwarki wadda Allah ya keɓe, suna gaishe ku.
The children of your chosen sister greet you.

< 2 Yohanna 1 >