< 2 Korintiyawa 1 >
1 Bulus, manzon Kiristi Yesu ta wurin nufin Allah, da kuma daga Timoti ɗan’uwanmu, Zuwa ga ikkilisiyar Allah da take a Korint, tare da dukan tsarkaka a ko’ina a Akayya.
Paul, an apostle of Christ Jesus through the will of God, and Timothy our brother, unto the church of God which is at Corinth, with all the saints which are in the whole of Achaia:
2 Alheri da salama daga Allah Ubanmu da kuma Ubangiji Yesu Kiristi, su kasance tare da ku.
Grace to you and peace from God our Father and the Lord Jesus Christ.
3 Yabo ya tabbata ga Allah, da Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi, Uba mai tausayi, da kuma Allah na dukan ta’aziyya,
Blessed [be] the God and Father of our Lord Jesus Christ, the Father of mercies and God of all comfort;
4 wanda yakan yi mana ta’aziyya a cikin dukan wahalolinmu, domin mu kuma mu iya ta’azantar da waɗanda suke cikin kowace irin wahala, da ta’aziyyar da mu kanmu muka samu daga Allah.
who comforteth us in all our affliction, that we may be able to comfort them that are in any affliction, through the comfort wherewith we ourselves are comforted of God.
5 Gama kamar yadda wahalar Kiristi ta cika har tana zuba a cikin rayuwarmu, haka nan kuma ta wurin Kiristi ta’aziyyarmu ta cika har tana zuba.
For as the sufferings of Christ abound unto us, even so our comfort also aboundeth through Christ.
6 In muna shan wahala, ai, muna shanta domin ta’aziyyarku, da cetonku ne, in mun sami ta’aziyya, ai, mun same ta domin ta’aziyyarku ce, wadda take sa ku jure wa irin wahalan nan, da muke sha.
But whether we be afflicted, it is for your comfort and salvation; or whether we be comforted, it is for your comfort, which worketh in the patient enduring of the same sufferings which we also suffer:
7 Begen da muke da shi dominku kuwa, tabbatacce ne, domin mun san cewa kamar yadda kuke tarayya da mu a cikin wahalolinmu, haka kuma kuke tarayya da mu a cikin ta’aziyyarmu.
and our hope for you is stedfast; knowing that, as ye are partakers of the sufferings, so also are ye of the comfort.
8 ’Yan’uwa, ba ma so ku zama da rashin sani, a kan wahalolin da muka sha a lardin Asiya. Mun sha wahaloli sosai, har abin ya fi ƙarfinmu, ya sa muka fid da tsammanin rayuwa.
For we would not have you ignorant, brethren, concerning our affliction which befell [us] in Asia, that we were weighed down exceedingly, beyond our power, insomuch that we despaired even of life:
9 Ba shakka, a zuciyarmu mun ji kamar hukuncin kisa ne aka yi mana. Wannan kuwa ya faru ne domin kada mu dogara da kanmu, sai dai ga Allah, wanda yake tā da matattu.
yea, we ourselves have had the answer of death within ourselves, that we should not trust in ourselves, but in God which raiseth the dead:
10 Shi ya cece mu daga irin wannan hatsari na mutuwa, zai kuwa cece mu. A kansa muka kafa bege cewa zai ci gaba da cetonmu,
who delivered us out of so great a death, and will deliver: on whom we have set our hope that he will also still deliver us;
11 yayinda kuke taimakonmu ta wurin addu’o’inku. Mutane da yawa kuwa za su yi godiya ta dalilinmu, saboda albarkar da aka yi mana, ta amsa addu’o’i masu yawa.
ye also helping together on our behalf by your supplication; that, for the gift bestowed upon us by means of many, thanks may be given by many persons on our behalf.
12 Wannan shi ne taƙamarmu. Lamirinmu yana ba da shaida cewa mun yi zamanmu a duniya, musamman a dangantakarmu da ku cikin tsarki, tsakani da Allah. Mun yi haka ta wurin bishewar alherin Allah, ba bisa ga hikimar duniya ba.
For our glorying is this, the testimony of our conscience, that in holiness and sincerity of God, not in fleshly wisdom but in the grace of God, we behaved ourselves in the world, and more abundantly to you-ward.
13 Gama ba mu rubuta muku abin da ba za ku iya karatu ko ku kāsa fahimta ba. Ina kuma fata cewa,
For we write none other things unto you, than what ye read or even acknowledge, and I hope ye will acknowledge unto the end:
14 kamar yadda kuka ɗan fahimce mu, za ku kai ga cikakkiyar fahimta cewa za ku iya yin taƙama da mu, kamar yadda mu ma za mu yi taƙama da ku a ranar da Ubangiji Yesu zai dawo.
as also ye did acknowledge us in part, that we are your glorying, even as ye also are ours, in the day of our Lord Jesus.
15 Saboda na amince da haka, shi ya sa na so zuwa wurinku da fari, domin ku sami albarka riɓi biyu.
And in this confidence I was minded to come before unto you, that ye might have a second benefit;
16 Na yi shiri in ziyarce ku a kan hanyata zuwa Makidoniya, in kuma sāke dawo wurinku a kan hanyata daga Makidoniya, sa’an nan ku yi mini rakiya a hanyata zuwa Yahudiya.
and by you to pass into Macedonia, and again from Macedonia to come unto you, and of you to be set forward on my journey unto Judaea.
17 Kuna gani na yi wannan shirin ba da sanin abin da nake yi ba ne? Ko kuwa, kuna gani na yi shirin nan da halin mutuntaka ne, don in ce, “I” in koma in ce, “A’a”?
When I therefore was thus minded, did I shew fickleness? or the things that I purpose, do I purpose according to the flesh, that with me there should be the yea yea and the nay nay?
18 Kamar dai yadda ba shakka Allah yake mai aminci, haka ma maganar da muka yi muku, ba “I” da kuma “A’a” ba ce.
But as God is faithful, our word toward you is not yea and nay.
19 Gama Ɗan Allah, Yesu Kiristi, wanda ni da Sila da Timoti muka yi muku wa’azinsa, ai, ba “I” da “A’a” ba ne, amma a cikin Kiristi, “I” ne kullum.
For the Son of God, Jesus Christ, who was preached among you by us, [even] by me and Silvanus and Timothy, was not yea and nay, but in him is yea.
20 Domin dukan alkawaran Allah cikarsu a gare shi suke, ta wurinsa ne kuma muke faɗar “Amin”, domin a ɗaukaka Allah.
For how many soever be the promises of God, in him is the yea: wherefore also through him is the Amen, unto the glory of God through us.
21 Allah ne fa yake sa mu da ku mu tsaya daram cikin Kiristi. Shi ne ya shafe mu,
Now he that stablisheth us with you in Christ, and anointed us, is God;
22 ya buga mana hatiminsa a kan mu nasa ne, ya kuma sa mana Ruhunsa a cikin zukatanmu, domin yă tabbatar da abin da yake zuwa nan gaba.
who also sealed us, and gave [us] the earnest of the Spirit in our hearts.
23 Labudda, Allah shi ne shaidata cewa don kada in ƙara muku wahala ne ya sa ban koma Korint ba.
But I call God for a witness upon my soul, that to spare you I forbare to come unto Corinth.
24 Ba nuna muku iko a kan bangaskiyarku muke yi ba, sai dai muna aiki tare da ku ne saboda farin cikinku, domin bisa ga bangaskiya ce kuke tsaye da ƙarfi.
Not that we have lordship over your faith, but are helpers of your joy: for by faith ye stand.