< 2 Korintiyawa 8 >
1 To,’yan’uwa, muna so ku san abin da alherin Allah ya ba wa ikkilisiyoyin Makidoniya.
Now we make known to you, brethren, the grace of God conferred on the churches of Macedonia:
2 Gama sun sha wuya sosai saboda tsananin wahalar da suka shiga, har yawan farin cikinsu ya kai su ga yin alheri ta bayarwa ga waɗansu, ko da yake suna cikin tsananin talauci.
how in a great trial of affliction, their abundant chearfulness and their deep poverty, hath munificently shewn the riches of their bounty.
3 Gama ina shaida cewa sun bayar daidai gwargwadon iyawarsu, har ma fiye da ƙarfinsu. Su kansu,
For to their power, I bear them witness, yea and beyond their power, they contributed of their own accord:
4 sun roƙe mu sosai don su sami damar yin bayarwa a wannan hidima ga tsarkaka.
intreating us with much importunity, that we would convey the gift, and so take upon us a part of the ministration to the saints.
5 Ba su yi yadda muka za tă ba, sai ma suka fara ba da kansu ga Ubangiji, sa’an nan sai suka ba da kansu gare mu bisa ga nufin Allah.
And this they did not merely as we hoped, but first gave themselves unto the Lord, and to us by the will of God.
6 Ganin haka sai muka roƙi Titus, da yake shi ne ya riga ya tsiro da wannan aikin alheri a cikinku, sai yă ƙarasa shi.
Insomuch that we desired Titus, that as he had already begun, so he would also complete this grace among you.
7 To, da yake kun fiffita a kowane abu cikin bangaskiya, cikin magana, cikin sani, cikin dukan ƙwazo, da kuma cikin ƙaunarku dominmu, sai ku fiffita a wannan aikin alheri ma.
And as ye abound in every other grace, in faith, and utterance, and knowledge, and in all diligence, and in your love to us, that ye may abound in this grace also.
8 Ba umarni nake ba ku ba, sai dai ina so in gwada gaskiyar ƙaunarku ne, ta wurin kwatanta ta da aniyar waɗansu.
I speak not by way of command, but to prove the sincerity of your love also, by means of the forwardness of others.
9 Gama kun san alherin Ubangijinmu Yesu Kiristi cewa ko da yake shi mawadaci ne, duk da haka, ya zama matalauci saboda ku, domin ta wurin talaucinsa, ku zama mawadata.
For ye know the grace of our Lord Jesus Christ, that though He was rich, yet for your sakes He became poor, that ye by his poverty might be rich.
10 Ga shawarata a kan abin da ya fi muku kyau a wannan al’amari. Bara ku kuka fara bayarwa, kuka kuma zama na farko wajen niyyar yin haka.
And herein I give my opinion: for this is to your advantage, who not only began to act, but also to be forward to it above a year ago.
11 Yanzu sai ku ƙarasa aikin da irin niyyar da kuka fara, ku yi haka gwargwadon ƙarfinku.
Now therefore perfect also the doing it; that as there was a readiness of will, so there may be also a performance according to your ability.
12 Gama in da niyyar bayarwa, za a karɓi bayarwa bisa ga abin da mutum yake da shi, ba bisa ga abin da ba shi da shi ba.
For if there be first a willing mind, any me is accepted according to what he hath, not according to what he hath not.
13 Ba nufi nake yi a sawwaƙe wa waɗansu, ku kuwa a jibga muku nauyin ba. Amma ya yi kyau dai
For I do not mean that others should have relief, and you be burdened:
14 a raba daidai wa daida, sai ku taimake su a yanzu da yalwarku saboda rashinsu. Wata rana su ma su taimake ku da yalwarsu saboda rashinku, don a daidaita al’amari,
but by an equality, that your abundance may at this time be a supply to their want; and their abundance may be the like to your want, if need be: that there may be an equality:
15 kamar yadda yake a rubuce cewa, “Wanda ya tara da yawa, bai tara fiye da bukatarsa ba, wanda kuma ya tara kaɗan, bai kāsa masa ba.”
as it is written, "He that gathered much had nothing over, and he that gathered little had no lack."
16 Ina gode wa Allah, wanda ya sa a zuciyar Titus, irin kula da nake da shi dominku.
But thanks be to God, who put the same concern for you into the heart of Titus:
17 Ba kawai ya yarda yă je wurinku kamar yadda muka roƙe shi yă yi ba, amma ya so yă zo kamar yadda ya riga ya yi niyya.
for he not only complied with the exhortation, but being more forward he went to you of his own accord.
18 Ga shi mun aiko ɗan’uwanmu nan tare da shi, wanda ikkilisiyoyi duka suna yabo saboda hidimarsa ga bishara.
And we have sent along with him the brother, whose praise in the gospel is spread through all the churches:
19 Ba kuwa haka kaɗai ba, har ma ikkilisiyoyi sun zaɓe shi yă riƙa tafiya tare da mu kan wannan aikin alheri da muke yi saboda ɗaukakar Ubangiji, da kuma nuna kyakkyawar niyyarmu.
(and not only so, but he was also chosen by the churches to accompany us with this grace, which is administered by us for the glory of the same Lord, and to shew your readiness of mind: )
20 Muna gudu kada wani yă zarge mu, a kan yadda muke gudanar da wannan kyautar da aka bayar hannu sake.
hereby taking care that no one might blame us in the disposal of this large sum which is administered by us:
21 Gama muna iya ƙoƙari mu yi abin da yake daidai, ba a gaban Ubangiji kaɗai ba, amma a gaban mutane ma.
looking to things that are right not only in the sight of the Lord, but also in the sight of men.
22 Ban da wannan kuma, mun aiko da ɗan’uwanmu tare da su, wanda ya sha tabbatar mana da ƙwazonsa ta hanyoyi iri-iri, musamman yanzu, domin ya amince da ku da gaske.
And we have sent with them another brother of ours, whom we have often proved diligent in many things, and now I doubt not much more on account of his great confidence in you.
23 Game da Titus kuma, shi abokin tarayyata ne, da kuma abokin aikina a cikinku; game da’yan’uwanmu kuwa, su wakilai ne na ikkilisiyoyi, kuma su masu ɗaukaka Kiristi ne.
If then there be any inquiry about Titus, he is my collegue and fellow-laborer among you: and if our brethren be inquired after, they are the messengers of the churches, and the glory of Christ.
24 Saboda haka, ku nuna wa waɗannan mutane shaidar ƙaunarku, da kuma dalilin taƙamarmu da ku, domin ikkilisiyoyi su gani.
Therefore shew to them, and before the churches, the proof of your love, and the justness of our boasting concerning you.