< 2 Korintiyawa 7 >

1 Da yake muna da waɗannan alkawura, ya ku ƙaunatattu, sai mu tsarkake kanmu daga kowane abu da yake ƙazantar da jiki, da ruhu, mu zama da cikakken tsarki, saboda bangirma ga Allah.
Kaunatattu, da shike muna da wadannan alkawura, bari mu tsaftace kanmu, daga dukan abubuwan da ke kazantar da jikinmu da ruhunmu. Bari mu bidi tsarki cikin tsoron Allah.
2 Ku saki zuciya da mu. Ba mu yi wa kowa laifi ba, ba mu ɓata kowa ba, ba mu cuci kowa ba.
Ku ba mu dama! Bamu bata wa kowa rai ba. Ba mu cutar da kowa ko mu zambaci kowa ba.
3 Ba na faɗin wannan don in sa muku laifi. Na riga na gaya muku yadda muke ƙaunarku ƙwarai cikin zukatanmu, har babu abin da zai iya raba ku da ƙaunarmu, ko a mutuwa ko a rayuwa.
Ba domin in kayar da ku na fadi haka ba. Domin kuwa na riga na fada muku, cewa kuna zuciyar mu, domin mu mutu tare mu kuma rayu tare.
4 Na amince da ku gaya, ina kuma taƙama da ku ƙwarai. Na ƙarfafa sosai. Duk da wahalce wahalcenmu dai ina farin ciki ƙwarai da gaske.
Ina da muhimmin gabagadi a cikin ku, Ina fahariya da ku. Ina cike da ta'aziya. Farincikina ya cika makil duk da wahalhalunmu.
5 Gama sa’ad da muka zo Makidoniya, jikin nan namu bai sami hutu ba, sai ma aka matsa mana a ta kowane gefe, a waje ga rikici, a zukatanmu kuma ga tsoro.
Yayin da muka zo Makidoniya, jikinmu bai samu hutu ba. A maimakon haka, mun shiga matsaloli ta ko wace hanya ta wurin tashin hankali a waje tsoro kuma a ciki.
6 Amma Allah, wanda yakan yi wa masu ɓacin rai ta’aziyya ya yi mana ta’aziyya da zuwan Titus,
Amma Allah, mai ta'azantar da raunana, ya ta'azantar da mu ta wurin zuwan Titus.
7 ba ma don zuwansa kaɗai ba, har ma a game da ƙarfafa zuciyan nan da ya samu a wurinku. Ya gaya mana yadda kuke so ku gan ni sosai, da kuma yadda kuka yi baƙin ciki game da abin da ya faru, da niyyar da kuka yi na goyon bayana. Wannan ne ya sa na ji daɗi ƙwarai.
Ba ta wurin isowar sa kadai Allah ya yi mana ta'aziyya ba. Amma kuma ta wurin ta'aziyyar da Titus ya samu daga wurin ku. Ya gaya mana irin matsananciyar kaunarku, bakincikinku, da zurfin kulawarku a kaina. Na kuwa yi farinciki sosai.
8 Ko da na ɓata muku rai ta wurin wasiƙata, ba na baƙin ciki da haka. Ko da yake dā kam na yi baƙin ciki, don na lura wasiƙata ta ɓata muku rai, amma na ɗan lokaci ne kawai.
Kodashike wasikata, ta bata maku rai, ban yi da na sanin haka ba. Amma sa'adda na ga wasika ta ta bata maku rai, na yi da na sani. Sai dai bacin ranku, na dan lokaci ne.
9 Duk da haka, yanzu ina farin ciki, ba don na sa ku baƙin ciki ba, sai dai domin baƙin cikinku ya kai ku ga tuba. Gama kun yi baƙin ciki kamar yadda Allah ya so, saboda haka, ba ku yi hasarar kome a sanadinmu ba.
Yanzu kuwa, ina farinciki, ba domin bacin ranku ba, amma domin bacin ranku ya kawo ku ga tuba, kun fuskanci bakinciki na ibada, donhaka ba ku yi rashi ba sabili da mu.
10 Baƙin ciki irin na tsoron Allah yana kai ga tuban da yake kawo ceto, ba ya kuma kawo baƙin ciki, amma baƙin ciki irin na duniya yakan kawo mutuwa.
Domin bakinciki daga Allah ya kan kai ga tuba da ke kammala ceto ba tare da-da na sani ba. Bakinciki na duniya kuwa ya kan kai ga mutuwa.
11 Ku dubi abin da wannan baƙin ciki irin na tsoron Allah ya kawo muku mana, ya sa ku marmarin aikatawa, da nuna cewa kun yi kuskure, ya sa kuka yi fushi, kuka kuma ji tsoro, ya sa kuka sa zuciya, kuka kuma sa aniya, ya sa kuna a shirye ku ga an yi horon da ya dace. Game da wannan sha’ani kam, lalle ta kowace hanya kun nuna cewa ba ku da laifi.
Ku dubi irin kyakkyawar niyya da bakincikin nan daga Allah ya haifar a cikin ku. Ina misalin girman niyyar nan taku ta nuna cewa baku da laifi. Ina misalin girman fushinku, tsoronku, da sa zuciyarku, himmar ku, da marmarin ku na ganin cewa an yi adalci! A cikin komai, kun nuna kanku marasa laifi a cikin wannan al'amari.
12 To, ko da yake na rubuta muku, ba musamman a kan wanda ya yi laifin ba ne, ba kuwa a kan wanda aka cutar ba, sai dai domin a bayyana muku a gaban Allah tsananin kula da kuke yi mana.
Kodayake na rubuto maku, ban rubuto saboda mai laifin ba, ko kuma saboda wanda aka yi wa laifin. Na rubuto ne domin himmarku gare mu ta sanu gare ku a gaban Allah.
13 Ta wurin wannan duka, muka sami ƙarfafawa. Ban da ƙarfafawar da muka samu, mun ji daɗi ƙwarai saboda yadda muka ga farin cikin Titus, domin ruhunsa ya sami wartsakewa daga gare ku duka.
Dalilin haka ne muka samu karfafawa. Baya ga ta'aziyyar mu, mun kuma yi murna sosai saboda farin cikin Titus, domin ruhunsa ya wartsake ta wurin ku duka.
14 Na yi taƙama da ku a wurinsa, ba ku kuwa ba ni kunya ba. Kamar dai yadda dukan abin da muka gaya muku gaskiya ne, haka ma taƙamarmu a kanku a gaban Titus ya zama gaskiya.
Domin kuwa idan na yi fahariya da ku a gaban sa, ban ji kunya ba. A sabanin haka, kamar yadda kowane abu da muka fada maku gaskiya ne, fahariyarmu a kan ku ga Titus ta zama gaskiya.
15 Ƙaunar da yake yi muku ya ƙaru ƙwarai, duk sa’ad da yake tunawa da biyayyarku duka, da kuma irin yawan bangirman da kuka nuna masa lokacin da kuka karɓe shi.
Kaunarsa a gare ku tana da girma, kamar yadda ya rika tunawa da biyayyarku duka, yadda kuka karbe shi da tsoro da rawar jiki.
16 Ina farin ciki ne don na amince da ku ƙwarai da gaske.
Ina farinciki matuka domin ina da cikakken gabagadi a cikin ku.

< 2 Korintiyawa 7 >