< 2 Korintiyawa 5 >

1 Yanzu mun san cewa in an hallaka tentin duniyan nan da muke ciki, muna da wani gini daga Allah, madawwamin gida a sama, wanda ba da hannuwan mutum ne suka gina shi ba. (aiōnios g166)
Знаємо бо, коли зе́мний мешка́льний наме́т наш зруйнується, то маємо будівлю від Бога на небі, - дім нерукотво́рний та вічний. (aiōnios g166)
2 Kafin nan muna nishi, da marmari a yi mana sutura da gidanmu na sama,
Тому́ то й зідхаємо, бажаючи приодягти́ся будівлею нашею, що з неба,
3 don sa’ad da aka yi mana sutura, ba za a same mu tsirara ba.
коли б тільки й одя́гнені ми не знайшлися нагі́!
4 Sa’ad da muke zaune a cikin jikin nan na duniya, nishi muke domin matsuwar da muke sha, ba domin muna so mu rabu da jikinmu na wannan duniya ba ne, sai dai don so muke yi a suturta mu da na Sama, domin mai rai ya shafe mai mutuwa.
Бо ми, знахо́дячися в цьому наметі, зідхаємо під тягаре́м, бо не хочемо роздягти́ся, але одягти́ся, щоб смертне поже́рлось життям.
5 Allah ne ya yi mu domin wannan, ya kuma ba mu Ruhu a matsayin abin ajiya, yana kuma tabbatar da abin da zai zo nan gaba.
А Той, Хто на це саме й створив нас, то Бог, що й дав нам завда́ток Духа.
6 Saboda haka, kullum muna da tabbaci mun kuma san cewa, muddin muna a duniya cikin jikin nan, ana raba mu da Ubangiji.
Отож, бувши відважні постійно, та знаючи, що, мавши дім у тілі, ми не перебуваємо в домі Господньому,
7 Rayuwa bangaskiya muke, ba ta ganin ido ba.
бо хо́димо вірою, а не виді́нням,
8 Ina cewa muna da tabbaci, za mu fi so mu rabu da jikin nan, mu kuma kasance a sama tare da Ubangiji.
ми ж відважні, і бажаємо краще покинути дім тіла й мати дім у Господа.
9 Saboda haka, niyyarmu ita ce, mu gamshe shi, ko muna a duniya cikin jikin nan, ko ba mu nan.
Тому́ ми й пильнуємо, - чи зостаємося в домі тіла, чи вихо́димо з дому, - бути Йому лю́бими.
10 Gama dole dukanmu mu bayyana a gaban kujerar shari’ar Kiristi, domin kowannenmu yă karɓi ladan aikin da ya yi a wannan jiki, ko mai kyau ne ko marar kyau.
Бо мусимо всі ми з'явитися перед судо́вим престолом Христовим, щоб кожен прийняв згідно з тим, що́ в тілі робив він, - чи добре, чи лихе́.
11 To, da yake mun san ko mene tsoron Ubangiji yake, muna ƙoƙari mu rinjaye mutane. Yadda muke kuwa, yana sane a sarari ga Allah, ina kuma fata yana nan a sarari a lamirinku.
Отже, відаючи страх Господній, ми людей переконуємо, а Богові явні; але маю надію, що й у ваших сумліннях ми явні.
12 Ba ƙoƙari muke mu yabe kanmu a gare ku ba ne, sai dai muna ba ku damar yin taƙama da mu ne, don ku sami amsar da za ku ba wa waɗanda suke taƙama da abin da ake gani ne, a maimakon abin da yake cikin zuciya.
Бо не зно́ву себе ми дору́чуємо вам, але даємо вам привід хвали́тися нами, щоб мали ви що проти тих, що хва́ляться обличчям, а не серцем.
13 In hankalinmu a taɓe yake, ai, saboda Allah ne, in kuwa cikin hankalinmu muke, ai, saboda ku ne.
Коли бо ми з розуму сходимо, - то Богові, коли ж при здоровому розумі, - то для вас.
14 Ƙaunar Kiristi a gare mu, ita take mallakarmu, saboda haka mun tabbata, da yake wani ya mutu saboda dukan mutane, ashe kuwa, mutuwarsu ce dukansu.
Бо Христова любов спону́кує нас, що ду́мають так, що коли вмер Один за всіх, то всі померли.
15 Ya kuwa mutu ne saboda dukan mutane, domin kada waɗanda suke rayuwa kada su yi zaman ganin dama a nan gaba, sai dai su yi zaman wannan da ya mutu saboda su, aka kuma tashe shi saboda su.
А вмер Він за всіх, щоб ті, хто живе, не жили вже для себе самих, а для Того, Хто за них був умер і воскрес.
16 Saboda haka, daga yanzu zuwa nan gaba, ba mu ƙara ɗaukan wani mutum bisa ga ganin duniya ba. Ko da yake a dā, mun ɗauki Kiristi haka, amma yanzu mun daina yin haka.
Через те відтепе́р ми ніко́го не знаємо за тілом; коли ж і знали за тілом Христа, то тепер ми не знаємо вже!
17 Saboda haka, duk wanda yake cikin Kiristi, sabuwar halitta ce, tsohon al’amari ya shuɗe, sabon ya zo!
Тому́ то, коли хто в Христі, той створі́ння нове́, - стародавнє минуло, ото сталось нове́!
18 Duk wannan kuwa daga Allah ne, wanda ya sulhunta mu da kansa ta wurin Kiristi, ya kuma ba mu hidimar sulhu,
Усе ж від Бога, що нас примирив із Собою Ісусом Христом і дав нам служі́ння прими́рення,
19 wato, Allah ya sulhunta duniya zuwa kansa ta wurin Kiristi, ba ya lissafta zunuban mutane a kansu. Ya kuma danƙa mana saƙon sulhu.
бо Бог у Христі примирив світ із Собою Самим, не зважа́вши на їхні провини, і поклав у нас слово прими́рення.
20 Saboda haka, mu jakadu ne na Kiristi, sai ka ce Allah kansa yake magana ta wurinmu. Muna roƙonku a madadin Kiristi. Ku sulhuntu da Allah.
Оце ми як посли замість Христа, ніби Бог благає через нас, благаємо замість Христа: примиріться з Богом!
21 Shi da bai san zunubi ba, Allah ya mai da shi kamar hadayar zunubi saboda mu, domin mu sami adalcin Allah ta wurinsa.
Бо Того́, Хто не відав гріха, Він учинив за нас гріхом, щоб стали ми Божою праведністю в Нім!

< 2 Korintiyawa 5 >