< 2 Korintiyawa 4 >

1 Saboda haka, da yake ta wurin jinƙan Allah ne muke da wannan hidima, ba za mu fid da zuciya ba.
Therefore, seeing we have this ministration, according as we have obtained mercy, we faint not;
2 Ba ruwanmu da ɓoye-ɓoye na munafuncin da suke abubuwan kunya. Ba ruwanmu da ruɗu, ko yin ƙarya da kalmar Allah. Sai dai muna faɗin gaskiya a fili. Ta haka ne kowa zai yi shaidar gaskiyarmu a gaban Allah cikin zuciyarsa.
But we renounce the hidden things of dishonesty, not walking in craftiness, nor adulterating the word of God; but by manifestation of the truth commending ourselves to every man’s conscience, in the sight of God.
3 Ko da bishararmu a rufe take, tana a rufe ne ga waɗanda suke hallaka.
And if our gospel be also hid, it is hid to them that are lost,
4 Allahn zamanin nan ya makanta hankulan marasa ba da gaskiya, yadda har ba za su iya ganin hasken bishara ta ɗaukakar Kiristi ba, wanda yake kamannin Allah. (aiōn g165)
In whom the god of this world hath blinded the minds of unbelievers, that the light of the gospel of the glory of Christ, who is the image of God, should not shine unto them. (aiōn g165)
5 Gama ba wa’azin kanmu muke yi ba, sai dai na Yesu Kiristi, a kan shi ne Ubangiji, mu kuma bayinku saboda Yesu.
For we preach not ourselves, but Jesus Christ our Lord; and ourselves your servants through Jesus.
6 Domin shi Allah wanda ya ce, “Bari haske yă haskaka daga duhu,” ya sa haskensa ya haskaka a cikin zukatanmu, don yă ba mu hasken sanin ɗaukakar Allah a fuskar Kiristi.
For God, who commanded the light to shine out of darkness, hath shined in our hearts, to give the light of the knowledge of the glory of God, in the face of Christ Jesus.
7 Amma muna da wannan dukiya a cikin tulunan yumɓu, don a nuna wannan mafificin ikon nan daga Allah ne, ba daga gare mu ba.
But we have this treasure in earthen vessels, that the excellency may be of the power of God, and not of us.
8 A matse muke a kowane gefe, sai dai ba a gurgunta mu ba. An rikitar da mu, amma ba mu fid da zuciya ba.
In all things we suffer tribulation, but are not distressed; we are straitened, but are not destitute;
9 An tsananta mana, amma ba a yashe mu ba, an fyaɗe mu da ƙasa, amma ba a hallaka mu ba.
We suffer persecution, but are not forsaken; we are cast down, but we perish not:
10 Kullum muna ɗauke da mutuwar Yesu a jikinmu, domin ran Yesu yă bayyana a jikinmu.
Always bearing about in our body the mortification of Jesus, that the life also of Jesus may be made manifest in our bodies.
11 Muddin muna a raye, kullum zaman mutuwa muke yi saboda Yesu, don a bayyana ran Yesu ta wurin jikin nan namu mai mutuwa.
For we who live are always delivered unto death for Jesus’ sake; that the life also of Jesus may be made manifest in our mortal flesh.
12 Ta haka, mutuwa tana aiki a cikinmu, ku kuwa rai a cikinku.
So then death worketh in us, but life in you.
13 A rubuce yake cewa, “Na gaskata; saboda haka na yi magana.” Da wannan ruhun bangaskiya ne mu ma muka gaskata, saboda haka muke magana.
But having the same spirit of faith, as it is written: I believed, for which cause I have spoken; we also believe, for which cause we speak also:
14 Domin mun san cewa shi da ya tā da Ubangiji Yesu daga matattu, zai tashe mu mu ma tare da Kiristi, yă kuma miƙa mu a gabansa tare da ku.
Knowing that he who raised up Jesus, will raise us up also with Jesus, and place us with you.
15 Duk wannan fa don amfaninku ne, domin alherin nan da yake bazuwa zuwa ga mutane masu yawa, yă zama dalilin godiya mai yawa ga ɗaukakar Allah.
For all things are for your sakes; that the grace abounding through many, may abound in thanksgiving unto the glory of God.
16 Saboda haka, ba mu fid da zuciya ba. Ko da yake a waje, jikinmu mai mutuwa yana lalacewa, amma can ciki, ana sabunta mu kowace rana.
For which cause we faint not; but though our outward man is corrupted, yet the inward man is renewed day by day.
17 Don wannan’yar wahalar tamu mai saurin wucewa, ita take tanadar mana madawwamiyar ɗaukaka mai yawa, fiye da kwatanci. (aiōnios g166)
For that which is at present momentary and light of our tribulation, worketh for us above measure exceedingly an eternal weight of glory. (aiōnios g166)
18 Domin ba abubuwan da ido yake gani ne muke dubawa ba, sai dai marasa ganuwa. Gama abubuwan da ake gani masu saurin wucewa ne, marasa ganuwa kuwa, madawwama ne. (aiōnios g166)
While we look not at the things which are seen, but at the things which are not seen. For the things which are seen, are temporal; but the things which are not seen, are eternal. (aiōnios g166)

< 2 Korintiyawa 4 >