< 2 Korintiyawa 13 >
1 Wannan za tă zama ziyarata ta uku a wurinku ke nan. “Dole a tabbatar da kowace magana ta bakin shaidu biyu ko uku.”
这是我第三次到你们那里去,“各样事情必须凭两三个证人的口,才能确定。”
2 Na riga na yi muku gargaɗi sa’ad da nake tare da ku a zuwana na biyu. Yanzu da ba na nan tare da ku, ina maimaita irin gargaɗin nan domin in na zo ba wanda zai kuɓuce wa horon nan,
尽管我不在那里,但还是要再次警告他们,还有你们所有人——当我造访时,会毫不犹豫地对他们采取行动,
3 da yake kuna neman tabbaci cewa Kiristi yana magana ta wurina ne. To, ai, shi ba rarrauna ba ne a gare ku, amma ƙaƙƙarfa ne a cikinku.
因为你们在找基督借着我说话的凭据。基督对你们并非软弱,相反,他对你们是有能力的。
4 Ko da yake tabbatacce an gicciye shi cikin rashin ƙarfi, duk da haka, yana rayuwa bisa ga ikon Allah. Haka mu ma marasa ƙarfi ne a cikinsa, amma ta wurin ikon Allah za mu rayu tare da shi don mu yi muku hidima.
他因软弱被钉死了,却靠着上帝的大能活着。我们在他里面也是软弱的,但靠着上帝向你们所显的大能,也必与他一同活着。
5 Ku gwada kanku ku gani ko kuna cikin bangaskiya; ku auna kanku. Ashe, ba ku san cewa Kiristi Yesu yana cikinku ba? Sai ko in kun fāɗi gwajin.
你们应当察验自己是不是坚守信仰,也应当考验自己。难道不晓得基督耶稣就是与你们同在吗?(除非你们经不起考验。)
6 Ina fata za ku gane cewa ba mu fāɗi gwajin ba.
我盼望你们知晓,我们并非经不起考验的人。
7 Muna addu’a ga Allah kada ku aikata wani laifi. Ba don mutane su gani cewa mun ci gwajin ba ne, a’a, sai dai don ku yi abin da yake daidai, ko da yake zai zama kamar mun fāɗi gwajin ne.
我们祈求上帝,让你们不要做什么恶事。这并不是要显示我们经得起考验,而是要你们行善。至于我们,就让我们做经不起考验的人好了!
8 Kai, ba dama mu saɓa wa gaskiya, sai dai mu bi bayan gaskiyar.
我们不能做什么违背真理的事,只能维护真理。
9 Murna muke sa’ad da ba mu da ƙarfi, ku kuwa kuna da ƙarfi. Addu’armu ita ce, ku zama cikakku.
当我们软弱、你们刚强的时候,我们就欢喜。我们所求的,就是要你们完整。
10 Shi ya sa nake rubuta waɗannan abubuwa, sa’ad da ba na nan tare da ku, domin sa’ad da na zo, kada yă zama mini tilas in yi muku tsanani a game da nuna ikon nan da Ubangiji ya ba ni saboda ingantawa, ba saboda rushewa ba.
因此,我趁着不在你们那里的时候,把这些话写给你们,这样当我去了你们那里,就不必凭着主所给我的权力严厉地对待你们。这权力不是为了拆毁你们,而是要建立你们。
11 A ƙarshe’yan’uwa, sai wata rana. Ku yi ƙoƙari ku zama cikakku. Ku saurari roƙona, ku zama da tunani ɗaya, ku yi zaman salama. Allah na ƙauna da salama kuwa zai kasance tare da ku.
最后,兄弟姐妹们,你们要欢喜,要圆满,要获得安慰,要同心,要和睦。这样,恩典赐予平安的上帝必与你们同在。
12 Ku gaggai da juna da sumba mai tsarki.
你们要用圣洁的亲吻彼此问安。
13 Dukan tsarkaka suna gaishe ku.
众圣徒问候你们。
14 Alherin Ubangiji Yesu Kiristi, da ƙaunar Allah, da zumuntar Ruhu Mai Tsarki su kasance tare da ku duka.
愿主耶稣基督的恩惠,上帝的慈爱,圣灵的交流,常与你们众人同在。