< 2 Korintiyawa 11 >

1 Ina fata za ku yi haƙuri da’yar wautata. Amma, ai, kun riga kun yi haƙuri.
I could wish that you would tolerate a little folly in me! But indeed you do tolerate me.
2 Ina kishinku da kishi irin na Allah. Na yi muku alkawarin aure ga miji ɗaya, Kiristi, domin in miƙa ku a gare shi kamar budurwa zalla.
I am jealous over you with the jealousy of God. For I promised you in marriage as a pure bride, to one husband – the Christ.
3 Sai dai ina tsoro kada yă zama, kamar yadda maciji ya yaudari Hawwa’u da makircinsa, ku ma a bauɗar da hankalinku daga sahihiyar biyayya amintacciya ga Kiristi.
Yet I fear that it may turn out that, just as the snake by his craftiness deceived Eve, so your minds may have lost the loyalty and purity due from you to the Christ.
4 Gama in wani ya zo wurinku yana wa’azin wani Yesu dabam da wanda muka yi wa’azinsa, ko kuma in kun karɓi wani ruhu dabam da wanda kuka karɓa, ko wata bishara dabam da wadda kuka karɓa, ya nuna kun yarda da su ke nan cikin sauƙinkai.
For, if some newcomer is proclaiming a Jesus other than him whom we proclaimed, or if you are receiving a Spirit different from the Spirit which you received, or a good news different from that which you welcomed, then you are marvellously tolerant!
5 Amma a ganina waɗancan da kuke ce da su “manyan manzanni” ba su fi ni da wani abu ba.
I do not regard myself as in any way inferior to the most eminent apostles!
6 Mai yiwuwa ni ba horarre ba ne a magana, amma ina da sani. Mun kuwa bayyana muku wannan a sarari, ta kowace hanya.
Though I am no trained orator, yet I am not without knowledge; indeed we made this perfectly clear to you in every way.
7 Laifi ke nan ne na yi da na ƙasƙantar da kaina, don a ɗaga ku zuwa babban matsayi ta wurin yin muku wa’azin bisharar Allah kyauta?
Perhaps you say that I did wrong in humbling myself that you might be exalted – I mean because I told you God’s good news without payment.
8 Na yi wa waɗansu ikkilisiyoyi ƙwace ta wurin karɓar taimako daga wurinsu, domin in yi muku hidima.
I robbed other churches by taking pay from them, so that I might serve you!
9 Sa’ad da nake tare da ku kuma nake zaman rashi, ban nawaita wa kowa ba, gama’yan’uwan da suka zo daga Makidoniya sun biya bukata. Na kiyaye kaina daga nawaita muku ta kowace hanya, zan kuma ci gaba da yin haka.
And, when I was with you in need, I did not become a burden to any of you; for our friends, on coming from Macedonia, supplied my needs. I kept myself, and will keep myself from being an expense to you in any way.
10 Ba shakka, kamar yadda gaskiyar Kiristi take a cikina, babu wani a yankunan Akayya da zai iya hana yin taƙaman nan tawa.
As surely as I know anything of the truth of Christ, this boast, as far as I am concerned, will not be stopped in any part of Greece.
11 Don me? Don ba na ƙaunar ku ne? Allah dai ya sani ina ƙaunarku!
Why? Because I do not love you? God knows that I do!
12 Zan kuma ci gaba da yin abin da nake yi, domin in toshe kafar mutanen nan da suke fariya, suna nema mu daidaita da su.
What I am doing now I will continue to do in order to cut away the ground from under those who are wishing for some ground for attacking me, so that as regards the thing of which they boast they may appear in their true characters, just as we do.
13 Gama irin waɗannan mutane manzannin ƙarya ne, ma’aikata ne masu ruɗi, sun ɓad da kamanni kamar su manzannin Kiristi ne.
Such people are false apostles, treacherous workers, disguising themselves as apostles of Christ!
14 Ba abin mamaki ba ne, gama Shaiɗan kansa ma yana ɓad da kamanni kamar shi mala’ikan haske ne.
And no wonder; for even Satan disguises himself as an angel of light.
15 Don haka, ba abin mamaki ba ne, in bayin Shaiɗan sun ɓad da kamanni kamar su bayin adalci ne. A ƙarshe, za a sāka musu gwargwadon ayyukansu.
It is not surprising, therefore, if his servants also disguise themselves as servants of righteousness. But their end will be in accordance with their actions.
16 Ina sāke faɗa, kada wani yă ɗauka ni wawa ne. Amma in kun ɗauke ni haka, to, sai ku karɓe ni kamar yadda kuke karɓan wawa, domin in ɗan in yi taƙama.
I say again – Let no one think me a fool! Yet, if you do, at least welcome me as you would a fool, so that I, too may indulge in a little boasting.
17 A wannan taƙamata ba na magana yadda Ubangiji zai yi ba ne, sai dai magana ce irin ta wawa.
When I speak like this, I am not speaking as the Master would, but as a fool might, in boasting so confidently.
18 Da yake mutane da yawa suna taƙama irin ta duniya, ni ma haka zan yi.
As so many are boasting of earthly things, I, too, will boast.
19 Ku kam kuna da wayo sosai, har kuna jimre wa wawaye da murna!
For all your cleverness, you tolerate fools willingly enough!
20 Gaskiyar ita ce, kuna haƙuri da duk wanda ya sa ku bauta ko ya cuce ku ko ya more ku ko ya nuna muku isa ko kuma ya mare ku a fuska.
You tolerate a person even when they enslave you, when they plunder you, when they get you into their power, when they put on airs of superiority, when they strike you in the face!
21 Ina jin kunya in ce mun nuna kāsawa da ba mu yi waɗannan abubuwan ba! Abin da wani yake da ƙarfin hali yin taƙama a kai, shi ne ni ma nake ƙarfin hali yin taƙama a kai. Ina magana kamar wawa ne.
I admit, to my shame, that we have been weak. But whatever the subject on which others are not afraid to boast – though it is foolish to say so – I am not afraid either!
22 In su Ibraniyawa ne, ni ma haka. In su Isra’ilawa ne, ni ma haka. In su zuriyar Ibrahim ne, ni ma haka.
Are they Hebrews? So am I! Are they Israelites? So am I! Are they descendants of Abraham? So am I!
23 In su bayin Kiristi ne, ni na fi su ma, ina magana kamar ruɗaɗɗe ne fa! Ai, na fi su shan fama ƙwarai da gaske, da shan dauri, na sha dūka marar iyaka, na sha hatsarin mutuwa iri-iri.
Are they “Servants of Christ”? Though it is madness to talk like this, I am more so than they! I have had more of toil, more of imprisonment! I have been flogged times without number. I have been often at death’s door.
24 Sau biyar Yahudawa suka yi mini bulala arba’in ɗaya babu.
Five times I received at the hands of my own people forty lashes, all but one.
25 Sau uku aka bulale ni da bulalar ƙarfe, sau ɗaya aka jajjefe ni da duwatsu, sau uku jirgin ruwa ya ragargaje ina ciki, na kwana na kuma yini ruwan teku yana tafiya da ni.
Three times I was beaten with rods. Once I was stoned. Three times I was shipwrecked. I have spent a whole day and night in the deep.
26 Na yi tafiye-tafiye da yawa, na sha hatsari a koguna, na sha hatsarin’yan fashi, na sha hatsari a hannun kabilarmu, na sha hatsari a hannun al’ummai, na sha hatsari a birane, na sha hatsari a jeji, na sha hatsari a teku, na kuma sha hatsarin’yan’uwa na ƙarya.
My journeys have been many. I have been through dangers from rivers, dangers from robbers, dangers from my own people, dangers from the Gentiles, dangers in towns, dangers in the country, dangers on the sea, dangers among people pretending to be followers of the Lord.
27 Na yi fama, na shan wuya, ga kuma rashin barci sau da yawa. Na san abin da ake nufin da jin yunwa da ƙishirwa, sau da yawa kuwa na kasance da rashin abinci, na sha sanyi da zaman tsirara.
I have been through toil and hardship. I have passed many a sleepless night; I have endured hunger and thirst; I have often been without food; I have known cold and nakedness.
28 Ban da waɗannan abubuwa, kowace rana ina ɗauke da nauyin kula da dukan ikkilisiyoyi.
And, not to speak of other things, there is my daily burden of anxiety about all the churches.
29 Wane ne ya rasa ƙarfi, da ban ji shi a jikina ba? Wane ne ya fāɗi cikin zunubi, da ban ji zafin wannan ba?
Who is weak without my being weak? Who is led astray without my burning with indignation?
30 In ma lalle ne in yi taƙama, to, sai in yi taƙama da abubuwan da suka nuna rashin ƙarfina.
If I must boast, I will boast of things which show my weakness!
31 Allah Uban Ubangiji Yesu Kiristi, wanda yabo ta tabbata a gare shi har abada, ya san cewa ba ƙarya nake yi ba. (aiōn g165)
The God and Father of the Lord Jesus – he who is for ever blessed – knows that I am speaking the truth. (aiōn g165)
32 A Damaskus, gwamnan da yake ƙarƙashin Sarki Aretas, ya sa tsare ƙofofin birnin Damaskus, don yă kama ni.
When I was in Damascus, the Governor under King Aretas had the gates of that city guarded, so as to arrest me,
33 Amma aka saukar da ni cikin kwando ta tagar katanga, na kuɓuce masa.
but I was let down in a basket through a window in the wall, and so escaped his hands.

< 2 Korintiyawa 11 >