< 2 Korintiyawa 10 >
1 Ni Bulus da kaina, ina roƙonku albarkacin tawali’u da sanyin hali na Kiristi, ni da ake yi wa kirari “marar tsanani” a cikinku, amma “mai matsawa” sa’ad da nake rabe da ku!
2 Ina roƙonku cewa sa’ad da na zo kada ku tilasta ni in matsa muku, gama na tabbata zan iya tsaya wa waɗanda suka ce abin da muke yi sha’anin duniya ne.
3 Ko da yake muna cikin duniya, ba ma yaƙi kamar yadda duniya take yi.
4 Makaman da muke yaƙi da su, ba makamai na duniya ba ne. Sai dai na ikon Allah ne, masu rushe wuraren mafaka masu ƙarfi.
5 Muna ka da masu gardama da kowane tunanin ɗaga kai da yake kafa kansa gāba da sanin Allah, muna kuma jan hankalin kowa ga bautar Kiristi.
6 A shirye muke mu hori kowane rashin biyayya, sa’ad da biyayyarku ta cika.
7 Kuna duban abubuwa bisa-bisa ne kawai. In wani ya ganin cewa shi na Kiristi ne, ya kamata yă sāke lura cewa kamar yadda yake na Kiristi, haka mu ma muke.
8 Ko da zan yi gadara fiye da kima a game da izinin nan namu, wanda Ubangiji ya bayar saboda inganta ku, ba don rushe ku ba, ba ni da abin jin kunya a ciki.
9 Ba na so yă zama kamar ina ƙoƙari in tsorata ku ne da wasiƙuna.
10 Gama waɗansu suna cewa, “Wasiƙunsa suna da nauyi da kuma ƙarfi, amma kuwa in ka gan shi, ba shi da wani kwarjini, maganarsa kuma ba kome ba ce.”
11 Ya kamata irin waɗannan mutane su gane cewa abin da muke faɗa a cikin wasiƙunmu sa’ad da ba ma nan tare da ku, shi muke aikatawa sa’ad da muke nan.
12 Ba za mu yi ƙarfin halin lissafta kanmu, ko mu kwatanta kanmu da waɗansu masu yabon kansu ba. Sa’ad da suke gwada kansu da kansu, da kuma kwatanta kansu da kansu, ba su da hikima.
13 Amma mu kam, ba za mu yi taƙama mu zarce iyakarmu ba, sai dai za mu yi taƙama cikin filin da Allah ya ƙayyade mana, filin kuwa ya kai har zuwa wurinku.
14 Ba mu wuce gona da iri a taƙamarmu ba, kamar yadda zai zama, da a ce ba mu zo wurinku ba, gama mun kai har wurinku da bisharar Kiristi.
15 Fahariyarmu ba fiye da yadda ya kamata take ba, ba tă kuma shafi aikin waɗansu ba. Sai dai muna sa zuciya bangaskiyarku ta riƙa ƙaruwa, ta haka kuma fagen aikinmu a cikinku yă riƙa ƙaruwa ƙwarai da gaske.
16 Saboda mu iya yin wa’azin bishara a yankunan da suke gaba da ku. Gama ba ma so mu yi taƙama game da aikin da aka riga aka yi a sashen wani.
17 Amma, “Duk mai yin taƙama, sai ya yi taƙama da Ubangiji.”
18 Ai, ba mai yabon kansa ake amincewa da shi ba, sai dai wanda Ubangiji ya yaba wa.