< 2 Tarihi 8 >
1 A ƙarshen shekaru ashirin, a lokacin da Solomon ya gina haikalin Ubangiji da nasa fadan,
2 Solomon ya sāke gina ƙauyukan da Hiram ya ba shi, ya kuma zaunar da Isra’ilawa a cikinsu.
3 Sa’an nan Solomon ya tafi Hamat-Zoba ya ci ta da yaƙi.
4 Ya kuma gina Tadmor a hamada da kuma dukan biranen ajiyar da ya gina a Hamat.
5 Ya sāke gina Bet-Horon na Bisa da kuma Bet-Horon na Ƙasa a matsayin birane masu katanga, da bangaye da ƙofofi da kuma ƙyamare,
6 haka kuma Ba’alat da dukan biranen ajiyarsa, da kuma dukan birane domin keken yaƙinsa da dawakansa, duk abin da ya so yă gina a Urushalima, a Lebanon da kuma dukan yankin da ya yi mulki, ya gina shi.
7 Dukan mutanen da suka rage daga Hittiyawa, Amoriyawa, Ferizziyawa, Hiwiyawa da Yebusiyawa (waɗannan mutane ba Isra’ilawa ba ne),
8 wato, zuriyarsu da suka ragu a ƙasar, wadda Isra’ilawa ba su hallaka ba, waɗannan ne Solomon ya mai da su bayinsa na aikin dole, kamar yadda yake har wa yau.
9 Amma Solomon bai mai da Isra’ilawa bayi don aikinsa ba; su ne mayaƙansa, shugabannin hafsoshinsa, da shugabannin keken yaƙinsa da kuma mahayan keken yaƙinsa.
10 Su ne kuma manyan ma’aikatan Sarki Solomon, manyan mutane ɗari biyu da hamsin masu lura da mutane.
11 Solomon ya kawo’yar Fir’auna daga Birnin Dawuda zuwa fadan da ya gina mata, gama ya ce, “Matata ba za tă zauna a fadan Dawuda sarkin Isra’ila ba, domin wuraren da akwatin alkawarin Ubangiji ya shiga masu tsarki ne.”
12 A kan bagaden Ubangiji da ya gina a gaban shirayi, Solomon ya miƙa hadayun ƙonawa ga Ubangiji,
13 bisa ga bukace-bukace na kullum don hadayun da Musa ya umarta don Asabbatai, Sabon Wata da kuma bukukkuwa uku na shekara, Bikin Burodi Marar Yisti, Bikin Makoni da Bikin Tabanakul.
14 Bisa ga farillar mahaifinsa Dawuda, ya naɗa ɓangarori na firistoci don ayyukansu da Lawiyawa don su jagoranci yabo su kuma taimaki firistoci bisa ga bukace-bukacen kowace rana. Ya kuma naɗa matsara ƙofofi ɓangarori, ɓangarori don ƙofofi dabam-dabam domin abin da Dawuda mutumin Allah ya umarta ke nan.
15 Ba a kuwa yi rashin biyayya ba game da abin da sarki ya umarta game da firistoci ko Lawiyawa a kan kayan haikalin ba.
16 An yi dukan ayyukan Solomon, daga ranar kafa tushen haikalin Ubangiji har gamawarsa. Ta haka aka gama haikalin Ubangiji.
17 Sa’an nan Solomon ya tafi Eziyon Geber da Elot a bakin tekun Edom.
18 Sai Hiram ya aika masa jiragen ruwan da masu tuƙinsu waɗanda suka san teku sosai. Ma’aikatan Hiram suka tafi da na Solomon zuwa Ofir suka dawo da talentin zinariya ɗari huɗu da hamsin wa Sarki Solomon.