< 2 Tarihi 5 >
1 Sa’ad da dukan aikin da Solomon ya yi domin haikalin Ubangiji ya gama, sai ya kawo abubuwan da mahaifinsa Dawuda ya keɓe a ciki, azurfa da zinariya da kuma dukan kayayyaki, ya kuwa sa su a cikin ma’ajin haikalin Allah.
2 Sa’an nan Solomon ya tattara zuwa Urushalima dattawan Isra’ila, dukan kawunan kabilu da manyan iyalan Isra’ilawa, don su haura da akwatin alkawarin Ubangiji daga Sihiyona, Birnin Dawuda.
3 Dukan mutanen Isra’ila kuwa suka tattaru gaba ɗaya suka zo wurin sarki a lokacin biki a wata na bakwai.
4 Sa’ad da dukan dattawan Isra’ila suka iso, Lawiyawa suka ɗauki akwatin alkawarin,
5 suka haura da akwatin alkawarin da kuma Tentin Sujada da dukan kayayyaki masu tsarkin da yake cikinta. Firistoci, waɗanda suke Lawiyawa, suka ɗauke su;
6 Sarki Solomon kuwa da taron Isra’ila gaba ɗaya da suka taru kewaye da shi suna a gaban akwatin alkawarin, suna miƙa tumaki da shanu masu yawa da suka wuce ƙirge ko lissafi.
7 Sa’an nan firistoci suka kawo akwatin alkawarin Ubangiji zuwa wurinsa a ciki cikin wuri mai tsarki na haikali, Wuri Mafi Tsarki, suka sa shi ƙarƙashin fikafikan kerubobin.
8 Kerubobin suka buɗe fikafikansu a bisa wurin akwatin alkawari suka kuma rufe akwatin alkawarin da sandunan ɗaukonsa.
9 Waɗannan sanduna sun yi tsawo ƙwarai har ƙarshensu sun nausa daga akwatin alkawarin, ana iya ganinsu daga gaban ciki wuri mai tsarki na can ciki amma ba daga waje Wuri Mai Tsarki ba; kuma suna nan a can har wa yau.
10 Babu wani abu a cikin akwatin alkawarin sai alluna biyu da Musa ya sa a cikinsa a Horeb, inda Ubangiji ya yi alkawari da Isra’ilawa bayan sun fito Masar.
11 Sa’an nan firistoci suka janye daga Wuri Mai Tsarki. Dukan firistocin da suke can sun tsarkake kansu, ko daga wace ɓangarori suka fito.
12 Dukan Lawiyawa waɗanda suke mawaƙa, Asaf, Heman, Yedutun da’ya’yansu maza da dangoginsu, suka tsaya a gefen gabas na bagaden, saye da lilin mai kyau suna kuma kaɗa ganguna, garayu da molaye. Tare da su akwai firistoci 120 masu busan ƙahoni.
13 Masu busan ƙahonin da mawaƙa suka haɗu da baki ɗaya sai ka ce murya guda ce, don su yabi su kuma yi godiya ga Ubangiji. Haɗe da busan ƙahoni, ganguna da sauran kayayyaki, suka tā da muryoyinsu cikin yabo ga Ubangiji suka rera, “Yana da kyau; ƙaunarsa dawwammamiya ce har abada.” Sai haikalin Ubangiji ya cika da girgije,
14 Firistoci ba su iya yin hidimarsu ba saboda girgijen, gama ɗaukakar Ubangiji ta cika haikalin Allah.