< 2 Tarihi 4 >

1 Ya yi bagaden tagulla mai tsawo kamu ashirin, fāɗinsa kamu ashirin, tsayinsa kuma kamu goma.
Moreover he made an altar of brass, twenty cubits the length thereof, and twenty cubits the breadth thereof, and ten cubits the height thereof.
2 Ya yi ƙaton kwano mai suna Teku na zubin ƙarfe, mai siffar da’ira, awonsa kamu goma ne daga da’ira zuwa da’ira tsayinsa kuma kamu biyar. Ya ɗauki magwaji mai tsawo kamu talatin ya auna shi kewaye.
Also he made the molten sea of ten cubits from brim to brim, round in compass, and the height thereof was five cubits; and a line of thirty cubits did compass it round about.
3 Ƙasa da da’ira kuwa, akwai siffofin bijimai kewaye da ita, goma ga kowane kamu guda. An yi zubin bijiman a jeri biyu a gefe guda na kwatarniya.
And under it was the similitude of oxen, which did compass it round about, for ten cubits, compassing the sea round about. The oxen were in two rows, cast when it was cast.
4 Tekun ya tsaya a kan bijimai goma sha biyu, uku na fuskantar arewa, uku na fuskantar yamma, uku na fuskantar kudu, uku kuma na fuskantar gabas. Tekun ya zauna a kansu, kuma ƙarfafun bayansu suna wajen tsakiya.
It stood upon twelve oxen, three looking toward the north, and three looking toward the west, and three looking toward the south, and three looking toward the east; and the sea was set upon them above, and all their hinder parts were inward.
5 Kaurin ya kai tafin hannu, kuma da’iransa ya yi kama da’irar kwaf, kama furen da ya tohu. Ya riƙe randuna dubu uku.
And it was a handbreadth thick; and the brim thereof was wrought like the brim of a cup, like the flower of a lily: it received and held three thousand baths.
6 Sa’an nan ya yi daruna goma don wanki ya sa biyar a gefen kudu, biyar kuma a gefen arewa. A cikinsu kayan da za a yi amfani don ɗauraye hadayun ƙonawa, amma firistoci suna amfani da ƙaton kwano mai suna Teku don wanki.
He made also ten lavers, and put five on the right hand, and five on the left, to wash in them; such things as belonged to the burnt-offering they washed in them; but the sea was for the priests to wash in.
7 Ya yi wurin ajiye fitila goma na zinariya bisa ga tsari dominsu ya kuma sa su a haikali, biyar a gefen kudu, biyar kuma a gefen arewa.
And he made the ten candlesticks of gold according to the ordinance concerning them; and he set them in the temple, five on the right hand, and five on the left.
8 Ya yi tebur goma ya kuma sa su cikin haikalin, biyar a gefen kudu, biyar kuma a gefen arewa. Ya kuma yi kwanonin yayyafawa guda ɗari.
He made also ten tables, and placed them in the temple, five on the right side, and five on the left. And he made a hundred basins of gold.
9 Ya yi fili na firistoci da kuma babban fili da ƙofofi domin filin, ya shafe ƙofofin da tagulla.
Furthermore he made the court of the priests, and the great court, and doors for the court, and overlaid the doors of them with brass.
10 Ya sa ƙaton kwano mai suna Teku a gefen kudu, a kusurwa kudu maso gabas.
And he set the sea on the right side of the house eastward, toward the south.
11 Ya kuma yi tukwane da manyan cokula da kwanonin yayyafawa. Ta haka Huram ya gama aikin da ya yi wa Sarki Solomon a cikin haikalin Allah.
And Huram made the pots, and the shovels, and the basins. So Huram made an end of doing the work that he wrought for king Solomon in the house of God:
12 Ginshiƙai biyu; kwanoni biyu masu siffar kwartaniya a bisa ginshiƙai; jeri biyu na tuƙaƙƙen adon kwanonin yayyafawa masu siffar kwartaniya a bisa ginshiƙai;
the two pillars, and the bowls, and the two capitals which were on the top of the pillars; and the two networks to cover the two bowls of the capitals that were on the top of the pillars;
13 rumman ɗari huɗu don jeri biyu na tuƙaƙƙe (layi biyu na rumman don kowane tuƙaƙƙe, mai adon kwano mai siffar kwartaniya a bisan ginshiƙai);
and the four hundred pomegranates for the two networks: two rows of pomegranates for each network, to cover the two bowls of the capitals that were upon the top of the pillars.
14 dakalai da darunansu;
He made also the bases, and the lavers made he upon the bases;
15 ya yi kwanon da ya kira Teku, da bijimai goma sha biyu a ƙarƙashinsa;
one sea, and the twelve oxen under it.
16 tukwane, manyan cokula, cokula masu yatsu don nama da dukan kayayyakin da suka shafi wannan. Dukan kayayyakin da Huram-Abi ya yi domin Sarki Solomon saboda haikalin Ubangiji an yi su da gogaggen tagulla ne.
The pots also, and the shovels, and the flesh-hooks, and all the vessels thereof, did Huram his master craftsman make for king Solomon for the house of the LORD of bright brass.
17 Sarki ya sa aka yi zubinsu a katakon yin tubali a filin Urdun tsakanin Sukkot da Zereda.
In the plain of the Jordan did the king cast them, in the clay ground between Succoth and Zeredah.
18 Dukan waɗannan abubuwa da Solomon ya yi suna da tsada ƙwarai har suka kai nauyin tagullar da ya fi misali.
Thus Solomon made all these vessels in great abundance; for the weight of the brass could not be found out.
19 Solomon ya kuma yi dukan kayayyakin da suke a cikin haikalin Allah. Bagaden zinariya; teburin da ake ajiye burodin Kasancewa;
And Solomon made all the vessels that were in the house of God, the golden altar also, and the tables whereon was the showbread;
20 wurin ajiye fitila na zinariya zalla tare da fitilunsu, don ƙonawa a gaban wuri mai tsarki na ciki kamar yadda aka tsara;
and the candlesticks with their lamps, that they should burn according to the ordinance before the Sanctuary, of pure gold;
21 aikin zānen furannin zinariya da fitilu da abin ɗiban wuta (an yi su da zinariya zalla);
and the flowers, and the lamps, and the tongs, of gold, and that perfect gold;
22 arautaki; kwanonin yayyafawa, kwanoni da hantsuka; da kuma ƙofofin zinariya na haikali, ƙofofi na ciki zuwa Wuri Mafi Tsarki da kuma ƙofofin babban zaure.
and the snuffers, and the basins, and the pans, and the fire-pans, of pure gold. And as for the entry of the house, the inner doors thereof for the most holy place, and the doors of the house, that is, of the temple, were of gold.

< 2 Tarihi 4 >