< 2 Tarihi 33 >

1 Manasse yana da shekara ashirin sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara hamsin da biyar.
ὢν δέκα δύο ἐτῶν Μανασσης ἐν τῷ βασιλεῦσαι αὐτὸν καὶ πεντήκοντα πέντε ἔτη ἐβασίλευσεν ἐν Ιερουσαλημ
2 Ya yi abin da yake mugu a gaban Ubangiji, yana bin ayyukan banƙyama na al’umman da Ubangiji ya kora a gaban Isra’ilawa.
καὶ ἐποίησεν τὸ πονηρὸν ἐναντίον κυρίου ἀπὸ πάντων τῶν βδελυγμάτων τῶν ἐθνῶν οὓς ἐξωλέθρευσεν κύριος ἀπὸ προσώπου τῶν υἱῶν Ισραηλ
3 Ya sāke gina masujadan kan tudun da mahaifinsa Hezekiya ya rurrushe; ya tā da bagadan Ba’al, ya kuma gina ginshiƙan Ashera. Ya rusuna wa dukan rundunonin taurari, ya kuma yi musu sujada.
καὶ ἐπέστρεψεν καὶ ᾠκοδόμησεν τὰ ὑψηλά ἃ κατέσπασεν Εζεκιας ὁ πατὴρ αὐτοῦ καὶ ἔστησεν στήλας ταῖς Βααλιμ καὶ ἐποίησεν ἄλση καὶ προσεκύνησεν πάσῃ τῇ στρατιᾷ τοῦ οὐρανοῦ καὶ ἐδούλευσεν αὐτοῖς
4 Ya gina bagadai cikin haikalin Ubangiji, waɗanda Ubangiji ya ce, “Sunana zai kasance cikin Urushalima har abada.”
καὶ ᾠκοδόμησεν θυσιαστήρια ἐν οἴκῳ κυρίου οὗ εἶπεν κύριος ἐν Ιερουσαλημ ἔσται τὸ ὄνομά μου εἰς τὸν αἰῶνα
5 Cikin filayen haikalin Ubangiji, ya gina bagadai ga dukan rundunonin taurari.
καὶ ᾠκοδόμησεν θυσιαστήρια πάσῃ τῇ στρατιᾷ τοῦ οὐρανοῦ ἐν ταῖς δυσὶν αὐλαῖς οἴκου κυρίου
6 Ya miƙa’ya’yansa maza hadaya a wuta cikin Kwarin Ben Hinnom, ya yi bokanci, ya yi duba, ya kuma yi maitanci, ya nemi shawarar mabiya da masu ruhohi. Ya yi abin da yake mugu ƙwarai a gaban Ubangiji, yana tsokanarsa yă yi fushi.
καὶ αὐτὸς διήγαγεν τὰ τέκνα αὐτοῦ ἐν πυρὶ ἐν Γαι‐βαναι‐εννομ καὶ ἐκληδονίζετο καὶ οἰωνίζετο καὶ ἐφαρμακεύετο καὶ ἐποίησεν ἐγγαστριμύθους καὶ ἐπαοιδούς ἐπλήθυνεν τοῦ ποιῆσαι τὸ πονηρὸν ἐναντίον κυρίου τοῦ παροργίσαι αὐτόν
7 Ya ɗauki siffar da aka sassaƙa wadda ya yi, ya sa ta a cikin haikalin Allah, wanda Allah ya ce wa Dawuda da kuma ɗansa Solomon, “Cikin wannan haikali da kuma cikin Urushalima, wanda na zaɓa daga cikin kabilan Isra’ila, zan sa Sunana har abada.
καὶ ἔθηκεν τὸ γλυπτὸν καὶ τὸ χωνευτόν εἰκόνα ἣν ἐποίησεν ἐν οἴκῳ θεοῦ οὗ εἶπεν ὁ θεὸς πρὸς Δαυιδ καὶ πρὸς Σαλωμων υἱὸν αὐτοῦ ἐν τῷ οἴκῳ τούτῳ καὶ Ιερουσαλημ ἣν ἐξελεξάμην ἐκ πασῶν φυλῶν Ισραηλ θήσω τὸ ὄνομά μου εἰς τὸν αἰῶνα
8 Ba zan ƙara bari ƙafafun Isra’ilawa su bar ƙasar da na ba wa kakanninku ba, in dai suka yi hankali ga yin kome da na umarce su game da duka dokoki, ƙa’idodi da kuma farillai da na bayar ta wurin Musa.”
καὶ οὐ προσθήσω σαλεῦσαι τὸν πόδα Ισραηλ ἀπὸ τῆς γῆς ἧς ἔδωκα τοῖς πατράσιν αὐτῶν πλὴν ἐὰν φυλάσσωνται τοῦ ποιῆσαι πάντα ἃ ἐνετειλάμην αὐτοῖς κατὰ πάντα τὸν νόμον καὶ τὰ προστάγματα καὶ τὰ κρίματα ἐν χειρὶ Μωυσῆ
9 Amma Manasse ya sa Yahuda da mutanen Urushalima suka kauce, har suka aikata mugunta fiye da al’umman da Ubangiji ya hallaka a gaban Isra’ilawa.
καὶ ἐπλάνησεν Μανασσης τὸν Ιουδαν καὶ τοὺς κατοικοῦντας ἐν Ιερουσαλημ τοῦ ποιῆσαι τὸ πονηρὸν ὑπὲρ πάντα τὰ ἔθνη ἃ ἐξῆρεν κύριος ἀπὸ προσώπου υἱῶν Ισραηλ
10 Ubangiji ya yi magana da Manasse da mutanensa, amma ba su kula ba.
καὶ ἐλάλησεν κύριος ἐπὶ Μανασση καὶ ἐπὶ τὸν λαὸν αὐτοῦ καὶ οὐκ ἐπήκουσαν
11 Saboda haka Ubangiji ya kawo manyan hafsoshin mayaƙan sarkin Assuriya a kansu, waɗanda suka ɗauki Manasse a matsayi ɗan kurkuku, suka sa ƙugiya a hancinsa, suka daure shi da sarƙoƙin tagulla suka kuma kai shi Babilon.
καὶ ἤγαγεν κύριος ἐπ’ αὐτοὺς τοὺς ἄρχοντας τῆς δυνάμεως βασιλέως Ασσουρ καὶ κατέλαβον τὸν Μανασση ἐν δεσμοῖς καὶ ἔδησαν αὐτὸν ἐν πέδαις καὶ ἤγαγον εἰς Βαβυλῶνα
12 Cikin wahalarsa ya nemi tagomashin Ubangiji Allahnsa ya kuma ƙasƙantar da kansa sosai a gaban Allah na kakanninsa.
καὶ ὡς ἐθλίβη ἐζήτησεν τὸ πρόσωπον κυρίου τοῦ θεοῦ αὐτοῦ καὶ ἐταπεινώθη σφόδρα ἀπὸ προσώπου θεοῦ τῶν πατέρων αὐτοῦ
13 Da ya yi addu’a gare shi, sai Ubangiji ya taɓu da tubansa, ya kuma saurari roƙonsa; saboda haka ya dawo da shi Urushalima da kuma zuwa mulkinsa. Sa’an nan Manasse ya san cewa Ubangiji shi ne Allah.
καὶ προσηύξατο πρὸς αὐτόν καὶ ἐπήκουσεν αὐτοῦ καὶ ἐπήκουσεν τῆς βοῆς αὐτοῦ καὶ ἐπέστρεψεν αὐτὸν εἰς Ιερουσαλημ ἐπὶ τὴν βασιλείαν αὐτοῦ καὶ ἔγνω Μανασσης ὅτι κύριος αὐτός ἐστιν ὁ θεός
14 Daga baya ya sāke gina katangar waje na Birnin Dawuda, yamma da maɓulɓular Gihon a cikin kwari, har zuwa mashigin Ƙofar Kifi, ya kuma kewaye tudun Ofel; ya yi ta da tsayi sosai. Ya sa hafsoshin mayaƙa cikin dukan biranen katanga a Yahuda.
καὶ μετὰ ταῦτα ᾠκοδόμησεν τεῖχος ἔξω τῆς πόλεως Δαυιδ ἀπὸ λιβὸς κατὰ Γιων ἐν τῷ χειμάρρῳ καὶ ἐκπορευομένων τὴν πύλην τὴν κυκλόθεν καὶ εἰς τὸ Οφλα καὶ ὕψωσεν σφόδρα καὶ κατέστησεν ἄρχοντας τῆς δυνάμεως ἐν πάσαις ταῖς πόλεσιν ταῖς τειχήρεσιν ἐν Ιουδα
15 Ya fid da baƙin alloli, ya kuma fid da siffofi daga haikalin Ubangiji, haka ma dukan bagadan da ya gina a kan tudun haikali da kuma cikin Urushalima, ya zubar da su a bayan birni.
καὶ περιεῖλεν τοὺς θεοὺς τοὺς ἀλλοτρίους καὶ τὸ γλυπτὸν ἐξ οἴκου κυρίου καὶ πάντα τὰ θυσιαστήρια ἃ ᾠκοδόμησεν ἐν ὄρει οἴκου κυρίου καὶ ἐν Ιερουσαλημ καὶ ἔξω τῆς πόλεως
16 Sa’an nan ya gyara bagaden Ubangiji ya kuma miƙa hadayun salama da kuma hadayun godiya a bagaden, ya kuma faɗa wa Yahuda su bauta wa Ubangiji, Allah na Isra’ila.
καὶ κατώρθωσεν τὸ θυσιαστήριον κυρίου καὶ ἐθυσίασεν ἐπ’ αὐτὸ θυσίαν σωτηρίου καὶ αἰνέσεως καὶ εἶπεν τῷ Ιουδα τοῦ δουλεύειν κυρίῳ θεῷ Ισραηλ
17 Mutane dai suka ci gaba da miƙa hadayu a masujadai kan tudu, amma wa Ubangiji Allahnsu kaɗai.
πλὴν ὁ λαὸς ἔτι ἐπὶ τῶν ὑψηλῶν πλὴν κύριος ὁ θεὸς αὐτῶν
18 Sauran ayyukan mulkin Manasse, haɗe da addu’arsa ga Allahnsa da kuma kalmomin da mai duba ya yi masa cikin sunan Ubangiji, Allah na Isra’ila, suna a rubuce cikin tarihin sarakunan Isra’ila.
καὶ τὰ λοιπὰ τῶν λόγων Μανασση καὶ ἡ προσευχὴ αὐτοῦ ἡ πρὸς τὸν θεὸν καὶ λόγοι τῶν ὁρώντων λαλούντων πρὸς αὐτὸν ἐπ’ ὀνόματι κυρίου θεοῦ Ισραηλ ἰδοὺ ἐπὶ λόγων
19 Addu’arsa da yadda Allah ya taɓu ta wurin tubansa, da kuma dukan zunubansa da rashin biyayyarsa, da wuraren da ya gina masujadan kan tudu ya kuma kafa ginshiƙan Ashera da gumaka kafin ya ƙasƙantar da kansa, duka suna a rubuce cikin tarihin mai duba.
προσευχῆς αὐτοῦ καὶ ὡς ἐπήκουσεν αὐτοῦ καὶ πᾶσαι αἱ ἁμαρτίαι αὐτοῦ καὶ αἱ ἀποστάσεις αὐτοῦ καὶ οἱ τόποι ἐφ’ οἷς ᾠκοδόμησεν τὰ ὑψηλὰ καὶ ἔστησεν ἐκεῖ ἄλση καὶ γλυπτὰ πρὸ τοῦ ἐπιστρέψαι ἰδοὺ γέγραπται ἐπὶ τῶν λόγων τῶν ὁρώντων
20 Manasse ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi a fadansa. Sai Amon ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki.
καὶ ἐκοιμήθη Μανασσης μετὰ τῶν πατέρων αὐτοῦ καὶ ἔθαψαν αὐτὸν ἐν παραδείσῳ οἴκου αὐτοῦ καὶ ἐβασίλευσεν ἀντ’ αὐτοῦ Αμων υἱὸς αὐτοῦ
21 Amon yana da shekara ashirin da biyu sa’ad da ya zama sarki, ya yi mulki a Urushalima shekara biyu.
ὢν εἴκοσι καὶ δύο ἐτῶν Αμων ἐν τῷ βασιλεύειν αὐτὸν καὶ δύο ἔτη ἐβασίλευσεν ἐν Ιερουσαλημ
22 Ya yi abin da yake mugu a gaban Ubangiji kamar yadda mahaifinsa Manasse ya yi. Amon ya bauta ya kuma miƙa hadayu ga dukan gumakan da Manasse ya yi.
καὶ ἐποίησεν τὸ πονηρὸν ἐνώπιον κυρίου ὡς ἐποίησεν Μανασσης ὁ πατὴρ αὐτοῦ καὶ πᾶσιν τοῖς εἰδώλοις οἷς ἐποίησεν Μανασσης ὁ πατὴρ αὐτοῦ ἔθυεν Αμων καὶ ἐδούλευσεν αὐτοῖς
23 Amma ba kamar mahaifinsa Manasse ba, bai ƙasƙantar da kansa a gaban Ubangiji ba; Amon ya ƙara laifinsa.
καὶ οὐκ ἐταπεινώθη ἐναντίον κυρίου ὡς ἐταπεινώθη Μανασσης ὁ πατὴρ αὐτοῦ ὅτι υἱὸς αὐτοῦ Αμων ἐπλήθυνεν πλημμέλειαν
24 Fadawan Amon sukan yi masa maƙarƙashiya, suka kashe shi a fadansa.
καὶ ἐπέθεντο αὐτῷ οἱ παῖδες αὐτοῦ καὶ ἐπάταξαν αὐτὸν ἐν οἴκῳ αὐτοῦ
25 Sa’an nan mutanen ƙasar suka kashe dukan waɗanda suka yi wa Sarki Amon maƙarƙashiya, suka naɗa Yosiya ɗansa sarki a maimakonsa.
καὶ ἐπάταξεν ὁ λαὸς τῆς γῆς τοὺς ἐπιθεμένους ἐπὶ τὸν βασιλέα Αμων καὶ ἐβασίλευσεν ὁ λαὸς τῆς γῆς τὸν Ιωσιαν υἱὸν αὐτοῦ ἀντ’ αὐτοῦ

< 2 Tarihi 33 >