< 2 Tarihi 30 >
1 Sai Hezekiya ya aika wa dukan Isra’ila da Yahuda, ya kuma rubuta wasiƙu zuwa Efraim da Manasse, yana gayyatarsu su zo haikalin Ubangiji a Urushalima, su kuma yi Bikin Ƙetarewa ga Ubangiji, Allah na Isra’ila.
Derpå sendte Ezekias Bud til hele Israel og Juda og skrev desuden Breve til Efraim og Manasse om at komme til HERRENs Hus i Jerusalem for at fejre Påsken for HERREN, Israels Gud.
2 Sarki da fadawansa da dukan taro a Urushalima suka yanke shawara su yi Bikin Ƙetarewa a wata na biyu.
Og Kongen, hans Øverster og hele Forsamlingen i Jerusalem rådslog om at fejre Påsken i den anden Måned;
3 Ba su iya yinsa a daidai lokacinsa ba domin babu isashen firistocin da suka tsarkake kansu, mutane kuma ba su taru a Urushalima ba.
thi de kunde ikke fejre den med det samme, da Præsterne ikke havde helliget sig i tilstrækkeligt Tal, og Folket ikke var samlet i Jerusalem.
4 Shirin ya yi kyau ga sarki da kuma dukan taron.
Kongen og hele Forsamlingen fandt det rigtigt;
5 Suka yanke shawara su yi shelar a ko’ina a Isra’ila, daga Beyersheba zuwa Dan, suna kiran mutane su zo Urushalima, suka kuma yi Bikin Ƙetarewa ga Ubangiji Allah na Isra’ila. Ba a yi bikin da mutane masu yawa bisa ga abin da aka rubuta ba.
derfor vedtog de at lade et Opråb udgå i hele Israel fra Be'ersjeba til Dan om at komme og fejre Påsken i Jerusalem for HERREN, Israels Gud, thi man havde ikke fejret den så fuldtalligt som foreskrevet.
6 Bisa ga umarnin sarki, sai’yan aika suka tafi ko’ina a Isra’ila da Yahuda da wasiƙu daga sarki da kuma daga fadawansa, wasiƙar tana cewa, “Mutanen Isra’ila, ku dawo ga Ubangiji Allah na Ibrahim, Ishaku da Isra’ila, domin yă dawo gare ku, ku da kuka tafi, ku da kuka kuɓuce daga hannun sarakuna Assuriya.
Så gik Ilbudene ud i hele Israel og Juda med Breve fra Kongens og hans Øversters Hånd og sagde efter Kongens Befaling: "Israeliter! Vend tilbage til HERREN, Abrahams, Isaks og Israels Gud, at han må vende sig til den Levnin: af eder, der er undsluppet Assyrerkongernes Hånd.
7 Kada ku zama kamar iyayenku da’yan’uwanku, waɗanda suka yi rashin aminci ga Ubangiji Allah na kakanninsu, har ya mai da su abin tsoro, yadda kuke gani.
Vær ikke som eders Fædre og Brødre, der var troløse mod HERREN, deres Fædres Gud, hvorfor han gjorde dem til Rædsel, som I selv kan se.
8 Kada ku yi taurinkai, yadda iyayenku suka yi; ku miƙa kai ga Ubangiji. Ku zo wuri mai tsarki, wanda ya tsarkake har abada. Ku bauta wa Ubangiji Allahnku, domin fushi mai zafi yă juye daga gare ku.
Vær nu ikke halsstarrige som eders Fædre, men ræk HERREN Hånden og kom til hans Helligdom, som han har helliget til evig Tid, og tjen HERREN eders Gud, at hans glødende Vrede må vende sig fra eder.
9 In kuka dawo wurin Ubangiji, sa’an nan waɗanda suka kama’yan’uwanku da’ya’yanku za su nuna musu tausayi, su kuma dawo wannan ƙasa, gama Ubangiji Allahnku mai alheri ne mai jinƙai kuma. Ba zai kau da fuskarsa daga gare ku ba, in kuka dawo gare shi.”
Thi når I omvender eder til HERREN, skal eders Brødre og Sønner finde Barmhjertighed hos dem, der førte dem bort, og vende tilbage til dette Land. Thi HERREN eders Gud er nådig og barmhjertig og vil ikke vende sit Åsyn fra eder, når l omvender eder til ham!"
10 ’Yan aika suka tafi gari-gari a cikin Efraim da Manasse, har zuwa Zebulun, amma mutane suka yi musu dariyar reni, suka kuma yi musu ba’a.
Og Ilbudene gik fra By til By i Efraims og Manasses Land og lige til Zebulon, men man lo dem ud og hånede dem.
11 Duk da haka, waɗansu mutanen Asher, Manasse da Zebulun suka ƙasƙantar da kansu suka tafi Urushalima.
Dog var der nogle i Aser, Manasse og Zebulon, der ydmygede sig og kom til Jerusalem;
12 Haka ma a Yahuda, hannun Allah yana a kan mutane don yă ba su zuciya ɗaya su yi abin da sarki da fadawansa suka umarta, suna bin maganar Ubangiji.
også i Juda virkede Guds Hånd, så at han gav dem et endrægtigt Hjerte til at udføre, hvad Kongen og Øversterne havde påbudt i Kraft af HERRENs Ord.
13 Taron mutane mai girma ya haɗu a Urushalima don Bikin Burodi Marar Yisti a wata na biyu.
Så samlede der sig i Jerusalem en Mængde Mennesker for at fejre de usyrede Brøds Højtid i den anden Måned, en vældig Forsamling.
14 Suka kawar da bagadai a Urushalima suka fid da bagadan turare suka zubar da su a Kwarin Kidron.
De gav sig til at fjerne de Altre, der var i Jerusalem; ligeledes fjernede de alle Røgelsekarrene og kastede dem ned i Kedrons Dal.
15 Suka yanka ɗan ragon Bikin Ƙetarewa a rana ta goma sha huɗu na wata na biyu. Firistoci da Lawiyawa suka ji kunya suka tsarkake kansu, suka kawo hadayun ƙonawa a haikalin Ubangiji.
Derpå slagtede de Påskelammet på den fjortende Dag i den anden Måned. Præsterne og Leviterne skammede sig og helligede sig og bragte Brændofre til HERRENs Hus;
16 Sa’an nan suka ɗauki matsayinsu na kullum yadda yake a Dokar Musa mutumin Allah. Firistoci suka yayyafa jinin da Lawiyawa suka ba su.
og de stillede sig på deres Plads, som deres Pligt var efter den Guds Mand Moses's Lov; Præsterne sprængte Blodet, som de modtog af Leviterne.
17 Da yake da yawa cikin taron ba su tsarkake kansu ba, dole Lawiyawa su yanka’yan ragunan Bikin Ƙetarewa domin dukan waɗanda ba su da tsarki, ba su kuma iya tsarkake ragunansu ga Ubangiji ba.
Thi mange i Forsamlingen havde ikke helliget sig; derfor slagtede Leviterne Påskelammene for alle dem, der ikke var rene, for således at hellige HERREN dem.
18 Ko da yake yawancin mutanen da suka zo daga Efraim, Manasse, Issakar da Zebulun ba su tsarkake kansu ba, duk da haka suka ci Bikin Ƙetarewa, ba tare da bin abin da yake a rubuce ba. Amma Hezekiya ya yi addu’a dominsu cewa, “Bari Ubangiji, wanda yake nagari, yă gafarta wa kowa
Thi de flesfe af Folket, især mange fra Efraim, Manasse, Issakar og Zebulon, havde ikke renset sig, men spiste Påskelammet anderledes end foreskrevet. Men Ezekias giki Forbøn for dem og sagde: "HERREN, den gode, tilgive
19 wanda ya sa zuciyarsa ga neman Allah, Ubangiji Allah na kakanninsa, ko da shi marar tsarki ne bisa ga dokokin wuri mai tsarki.”
enhver, som har vendt sit Hjerte til at søge Gud HERREN, hans Fædres Gud, selv om han ikke er ren, som Helligdommen kræver det!"
20 Ubangiji kuwa ya ji Hezekiya ya kuma warkar da mutane.
Og HERREN bønhørte Ezekias og lod Folket uskadt.
21 Isra’ilawan da suka kasance a Urushalima suka yi Bikin Burodi Marar Yisti kwana bakwai da farin ciki mai girma, yayinda Lawiyawa da firistoci suke rera ga Ubangiji kowace rana, haɗe da kayan kiɗin yabon Ubangiji.
Så fejrede de Israeliter, der var til Stede i Jerusalem, de usyrede Brøds Højtid med stor Glæde i syv Dage; og Leviterne og Præsterne sang af alle Kræfter dagligt Lovsange for HERREN.
22 Hezekiya ya yi magana mai ƙarfafawa ga dukan Lawiyawa waɗanda suka nuna ganewar fasaha a hidimar Ubangiji. Kwana bakwai suka ci rabonsu da aka tsara, suka miƙa hadayun salama, suka kuma yabi Ubangiji Allah na kakanninsu.
Og Ezekias talte venlige Ord til alle de Leviter, der havde udvist særlig Dygtighed i HERRENs Tjeneste; og de fejrede Højtiden til Ende de syv Dage, idet de ofrede Takofre og lovpriste HERREN, deres Pædres Gud.
23 Dukan mutanen suka yarda su ƙara kwana bakwai kuma, sai suka ci gaba da bikin cikin farin ciki har waɗansu kwana bakwai kuma.
Men derefter vedtog hele Forsamlingen at holde Højtid syv Dage til, og det gjorde de så med Glæde,
24 Hezekiya sarkin Yahuda ya tanada bijimai dubu ɗaya da tumaki da kuma awaki dubu bakwai wa taron, fadawa kuma suka tanada musu bijimai dubu da kuma tumaki da awaki dubu goma. Firistoci masu yawa suka tsarkake kansu.
thi Kong Ezekias af Juda gav Forsamlingen en Ydelse af 1.000 Tyre og 7.000 Stykker Småkvæg, og Øversterne gav Forsamlingen 1.000 Tyre og 10.000 Stykker Småkvæg; og en Mængde Præster helligede sig.
25 Taron gaba ɗaya na Yahuda suka yi farin ciki, tare da firistoci da kuma Lawiyawa da dukan waɗanda suka taru daga Isra’ila, har ma da baƙi waɗanda suka zo daga Isra’ila da waɗanda suke zama a Yahuda.
Da frydede hele Judas Forsamling sig, ligeledes Præsterne og Leviterne og hele den Forsamling, der var kommet fra Israel, og de fremmede, der var kommet fra Israels Land eller boede i Juda;
26 Aka yi farin ciki mai girma a Urushalima, gama tun zamanin Solomon ɗan Dawuda sarkin Isra’ila, ba a taɓa yin wani abu kamar haka a Urushalima ba.
og der var stor Glæde i Jerusalem, thi siden Davids Søns, Kong Salomo af Israels, Dage var sligt ikke sket i Jerusalem;
27 Firistoci da Lawiyawa suka tsaya suka albarkace mutane, Allah kuma ya ji su, gama addu’arsu ya kai sama, mazauninsa mai tsarki.
og Præsterne og Leviterne stod op og velsignede Folket, og deres Røst hørtes, og deres Bøn nåede Himmelen, hans hellige Bolig.