< 2 Tarihi 29 >

1 Hezekiya yana da shekara ashirin da biyar sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara ashirin da tara. Sunan mahaifiyarsa Abiya,’yar Zakariya.
ヒゼキヤは二十五歳の時位に即きヱルサレムにて二十九年の間世を治めたりその母はゼカリヤの女にして名をアビヤといふ
2 Ya yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji, kamar dai yadda kakansa Dawuda ya yi.
ヒゼキヤはその父ダビデの凡てなしたる如くヱホバの目に善と視たまふ事をなせり
3 A wata na farkon a farkon shekarar mulkinsa, ya buɗe ƙofofin haikalin Ubangiji ya gyara su.
即ち彼その治世の第一年一月にヱホバの室の戸を開きかつ之を修繕ひ
4 Ya kawo firistoci da Lawiyawa, ya tattara su a filin da yake a gefen gabas
祭司およびレビ人を携さへいりて東の廣場にこれを集め
5 ya kuma ce musu, “Ku saurare ni, Lawiyawa! Ku tsarkake kanku yanzu, ku kuma tsarkake haikalin Ubangiji Allah na kakanninku. Ku fid da ƙazanta daga wuri mai tsarki.
而して之にいひけるはレビ人よ我に聽け汝等いま身を潔めて汝等の先祖の神ヱホバの室を潔め汚穢を聖所より除きされ
6 Kakanninku ba su yi aminci ba; suka aikata abin da yake mugu a gaban Ubangiji Allahnmu, suka kuma yashe shi. Suka juya fuskokinsu daga mazaunin Ubangiji suka kuma juya masa baya.
夫我らの先祖は罪を犯し我らの神ヱホバの目に惡しと見たまふことを行ひてヱホバを棄てヱホバの住所に面を背けて後をこれに向け
7 Suka kulle ƙofofin shirayi, suka kuma kashe fitilu. Ba su ƙone turare ko su miƙa hadayun ƙonawa a wuri mai tsarki ga Allah na Isra’ila ba.
また廊の戸を閉ぢ燈火を消し聖所にてイスラエルの神に香を焚ず燔祭を献けざりし
8 Saboda haka, fushin Ubangiji ya fāɗo a kan Yahuda da Urushalima; ya mai da su abin tsoro da abin banrazana da kuma abin ba’a, kamar yadda kuke gani da idanunku.
是をもてヱホバの忿怒ユダとヱルサレムに臨みヱホバ彼等をして打ただよはされしめ詑異とならしめ胡盧とならしめたまへり汝らが目に覩るごとし
9 Abin da ya sa ke nan kakanninmu suka fāɗi ta takobi, kuma shi ya sa aka kai’ya’yanmu maza da’ya’yanmu mata da matanmu bauta.
即ち我儕の父は劍に斃れ我らの男子女子及び妻等はこれがために俘擄となれり
10 Yanzu ina niyya in yi alkawari da Ubangiji, Allah na Isra’ila, domin fushinsa yă kauce daga gare mu.
今我イスラエルの神ヱホバと契約を結ばんとする意志ありその烈しき怒我らを離るることあらん
11 ’Ya’yana maza, kada ku yi sakaci yanzu, gama Ubangiji ya zaɓe ku don ku tsaya a gabansa ku kuma yi masa hidima, don ku yi hidima a gabansa ku kuma ƙone turare.”
我子等よ今は怠たる勿れヱホバ汝らを擇びて己の前に立て事へしめ己に事ふる者となし香を焚く者となしたまひたればなりと
12 Sai waɗannan Lawiyawa suka shiga aiki, daga Kohatawa Mahat ɗan Amasai da Yowel ɗan Azariya. Daga Kabilar Merari, Kish ɗan Abdi da Azariya ɗan Yahallelel. Daga Gershonawa, Yowa ɗan Zimma da Eden ɗan Yowa.
是においてレビ人起り即ちコハテの子孫の中にてはアマサイの子マハテおよびアザリヤの子ヨエル、メラリの子孫の中にてはアブデの子キシおよびヱハレレルの子アザリヤ、ゲルシヨン人の中にてはジンマの子ヨアおよびヨアの子エデン
13 Daga zuriyar Elizafan, Shimri da Yehiyel. Daga zuriyar Asaf, Zakariya da Mattaniya.
エリザパンの子孫の中にてはシムリおよびヱイエル、アサフの子孫の中にてはゼカリヤおよびマツタニヤ
14 Daga iyalin Heman, Yehiyel da Shimeyi. Daga zuriyar Yedutun, Shemahiya da Uzziyel.
ヘマンの子孫の中にてはヱヒエルおよびシメイ、ヱドトンの子孫の中にてはシマヤおよびウジエル
15 Da suka tattara’yan’uwansu suka kuma tsarkake kansu, sai suka shiga ciki suka tsarkake haikalin Ubangiji, kamar yadda sarki ya umarta, suna bin maganar Ubangiji.
かれらその兄弟を集へて身を潔めヱホバの言に依りて王の傳へし命令にしたがひてヱホバの室を潔めんとて入きたり
16 Firistoci suka shiga cikin wuri mai tsarki na Ubangiji suka tsarkake shi. Suka fitar da dukan abin da yake marar tsabta da suka samu a haikalin Ubangiji zuwa filin haikalin Ubangiji. Lawiyawa suka ɗauke su suka kai su Kwarin Kidron.
祭司等ヱホバの室の奧に入りてこれを潔めヱホバの殿にありし汚穢をことごとくヱホバの室の庭に携へいだせばレビ人それを受て外にいだしキデロン河に持いたる
17 Suka fara tsarkakewar a rana ta farko na farkon wata, a rana ta takwas na watan kuwa suka kai shirayin Ubangiji. Karin kwana takwas kuma suka tsarkake haikalin Ubangiji kansa, suka gama a rana ta goma sha shida na farkon wata.
彼ら正月の元日に潔むることを始めてその月の八日にヱホバの廊におよびまたヱホバの家を潔むるに八日を費し正月の十六日にいたりて之を終れり
18 Sa’an nan suka tafi wurin Sarki Hezekiya suka faɗa masa, “Mun tsarkake haikalin Ubangiji gaba ɗaya, bagaden ƙone hadaya tare da dukan kayayyakinsa, da tebur don shirya tsarkaken burodi, tare da dukan kayayyakinsa.
かくて彼らヒゼキヤ王の處に入て言ふ我らヱホバの室をことごとく潔めまた燔祭の壇とその一切の器具および供前のパンの案とその一切の器皿とを潔めたり
19 Mun shirya muka kuma tsarkake dukan kayayyakin da Sarki Ahaz ya cire cikin rashin amincinsa yayinda yake sarki. Yanzu suna a gaban bagaden Ubangiji.”
またアハズ王がその治世に罪を犯して棄たりし一切の器皿をも整へてこれを潔めヱホバの壇の前にこれを据置りと
20 Da sassafe kashegari Sarki Hezekiya ya tattara manyan birni wuri ɗaya, suka haura zuwa haikalin Ubangiji.
是においてヒゼキヤ王蚤に起いで邑の牧伯等をあつめてヱホバの家にのぼり往き
21 Suka kawo bijimai bakwai, raguna bakwai, bunsurai bakwai da kuma awaki mata bakwai a matsayin hadaya don zunubi domin masarauta, domin wuri mai tsarki da kuma domin Yahuda. Sarki ya umarce firistoci, zuriyar Haruna, su miƙa waɗannan a bagaden Ubangiji.
牡牛七匹牡羊七匹羔羊七匹牡山羊七匹を牽きたらしめ國と聖所とユダのためにこれを罪祭となしアロンの子孫たる祭司等に命じてこれをヱホバの壇の上に献げしむ
22 Saboda haka suka yayyanka bijiman, firistoci suka karɓi jinin suka yayyafa a kan bagade. Suka kuma yanka ragunan suka yayyafa jinin a bagaden. Haka kuma suka yanka’yan ragunan suka yayyafa jinin a bagaden.
即ち牡牛を宰れば祭司等その血を受て壇に灑ぎまた牡羊を宰ればその血を壇に灑ぎまた羔羊を宰ればその血を壇に灑げり
23 Aka kawo awaki domin hadaya don zunubi a gaban sarki da taron, suka kuwa ɗibiya hannuwansu a kansu.
かくて人々罪祭の牡山羊を王と會衆の前に牽きたりければ彼らその上に手を按り
24 Sa’an nan firistoci suka yayyanka awakin suka miƙa jininsu a bagade domin hadaya don zunubi don kafara saboda dukan Isra’ila, domin sarki ya umarta a yi hadaya ta ƙonawa da hadaya don zunubi domin dukan Isra’ila.
而して祭司これを宰りその血を罪祭として壇の上に献げてイスラエル全國のために贖罪をなせり是は王イスラエル全國の爲に燔祭および罪祭を献ぐることを命じたるに因る
25 Sarki Hezekiya ya ajiye Lawiyawa a cikin haikalin Ubangiji tare da ganguna, garayu da molaye, yadda Dawuda da Gad mai duba na sarki da kuma annabi Natan suka tsara. Ubangiji ne ya umarta wannan ta wurin annabawansa.
王レビ人をヱホバの室に置きダビデおよび王の先見者ガデと預言者ナタンの命令にしたがひて之に鐃鈸瑟および琴を執しむ是はヱホバがその預言者によりて命じたまひし所なり
26 Saboda haka Lawiyawa suka tsaya a shirye tare da kayan kiɗin Dawuda, firistoci kuma tare da ƙahoninsu.
是においてレビ人はダビデの樂器をとり祭司は喇叭をとりて立つ
27 Hezekiya ya ba da umarni a miƙa hadaya ta ƙonawa a kan bagade. Yayinda aka fara miƙawa, ana rerawa ga Ubangiji, tare da bushe-bushe da kiɗe-kiɗen kayan waƙa na Dawuda sarkin Isra’ila.
時にヒゼキヤ燔祭を壇の上に献ぐることを命ぜり燔祭をささげ始むるときヱホバの歌をうたひ喇叭を吹きイスラエルの王ダビデの樂器をならしはじめたり
28 Dukan taron suka durƙusa suka yi sujada, yayinda mawaƙa suke rerawa, ana kuma busa ƙahoni, dukan wannan ya ci gaba sai da aka gama miƙa hadaya ta ƙonawa.
しかして會衆みな禮拝をなし謳歌者歌をうたひ喇叭手喇叭を吹ならし燔祭の終るまで凡て斯ありしが
29 Sa’ad da aka gama miƙawa, sai sarki da mutanen da suke tare da shi suka durƙusa suka yi sujada.
献ぐる事の終るにおよびて王および之と偕に在る者皆身をかがめて禮拝をなせり
30 Sarki Hezekiya da fadawansa suka umarci Lawiyawa su yabi Ubangiji da kalmomin Dawuda da na Asaf mai duba. Saboda haka suka rera yabai da murna, suka sunkuyar da kawunansu suka yi sujada.
かくて又ヒゼキヤ王および牧伯等レビ人に命じダビデと先見者アサフの詞をもてヱホバを讃美せしむ彼等喜樂をもて讃美し首をさげて禮拝す
31 Sa’an nan Hezekiya ya ce, “Yanzu kun keɓe kanku ga Ubangiji. Ku zo ku kuma kawo hadayu da hadayun godiya zuwa ga haikalin Ubangiji.” Saboda haka taron suka kawo hadayu da hadayun godiya, da kuma dukan waɗanda suke da niyya suka kawo hadayun ƙonawa.
時にヒゼキヤこたへて言けるは汝らすでにヱホバに事へんために身を潔めたれば進みよりてヱホバの室に犠牲および感謝祭を携へきたれと會衆すなはち犠牲および感謝祭を携へきたる又志ある者はみな燔祭を携ふ
32 Yawan hadayun ƙonawan da taron suka kawo, bijimai saba’in ne, raguna ɗari da kuma bunsurai ɗari biyu, dukansu kuwa domin hadayun ƙonawa ga Ubangiji ne.
會衆の携へきたりし燔祭の數は牡牛七十牡羊一百羔羊二百是みなヱホバに燔祭として奉つる者なり
33 Dabbobin da aka tsarkake a matsayi hadayu sun kai bijimai ɗari shida da tumaki da kuma awaki dubu uku.
また奉納物は牛六百羊三千なりき
34 Firistoci fa, suka kāsa sosai don fiɗan dukan dabbobin da za a miƙa don hadayun ƙonawa; saboda haka’yan’uwansu Lawiyawa suka taimake su har aka gama aiki kafin sauran firistoci su sami damar tsarkake kansu. Gama Lawiyawa sun fi firistoci himma wajen tsarkakewar kansu.
然るに祭司寡くしてその燔祭の物の皮を剥つくすこと能はざりければその兄弟たるレビ人これを助けてその工を終ふ斯る間に他の祭司等も身を潔むレビ人は祭司よりも心正しくして身を潔めたり
35 Aka kasance da hadayun ƙonawa a yalwace, tare da kitsen hadayun salama da hadayun sha da suke tafe da hadayun ƙonawa. Saboda haka aka sāke kafa hidimar haikalin Ubangiji.
燔祭夥多しくあり酬恩祭の脂及びすべての燔祭の酒も然り斯ヱホバの室の奉事備はれり
36 Hezekiya da dukan mutane suka yi farin ciki game da abin da Allah ya yi wa mutanensa, domin ya faru farat ɗaya.
この事俄なりしかども神かく民の爲に備をなしたまひしに因てヒゼキヤおよび一切の民喜べり

< 2 Tarihi 29 >