< 2 Tarihi 25 >

1 Amaziya yana da shekara ashirin da biyar sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara ashirin da tara. Sunan mahaifiyarsa Yehoyaddin ce; ita daga Urushalima ne.
בן עשרים וחמש שנה מלך אמציהו ועשרים ותשע שנה מלך בירושלם ושם אמו יהועדן מירושלים
2 Ya yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji, amma ba da dukan zuciyarsa ba.
ויעש הישר בעיני יהוה רק לא בלבב שלם
3 Bayan sarauta ta kahu a ƙarƙashinsa, sai ya kashe hafsoshin da suka kashe mahaifinsa sarki.
ויהי כאשר חזקה הממלכה עליו ויהרג את עבדיו המכים את המלך אביו
4 Duk da haka bai kashe’ya’yansu maza ba amma ya yi bisa ga abin da yake a rubuce a cikin Doka, a cikin Littafin Musa, inda Ubangiji ya umarta, “Ba za a kashe iyaye saboda’ya’yansu ba; ba kuwa za a kashe’ya’ya saboda iyayensu ba; kowa zai mutu saboda zunubansa ne.”
ואת בניהם לא המית כי ככתוב בתורה בספר משה אשר צוה יהוה לאמר לא ימותו אבות על בנים ובנים לא ימותו על אבות--כי איש בחטאו ימותו
5 Amaziya ya tattara mutanen Yahuda ya kuma ba su aiki bisa ga iyalansu, ya ba da aiki ga shugabannin dubu-dubu da shugabannin ɗari-ɗari, a dukan Yahuda da Benyamin. Ya kuma tattara waɗanda suke’yan shekara ashirin da haihuwa ko fiye ya sami mutane dubu ɗari uku da suke a shirye don aikin soja, da suka isa riƙe māshi da garkuwa.
ויקבץ אמציהו את יהודה ויעמידם לבית אבות לשרי האלפים ולשרי המאות לכל יהודה ובנימן ויפקדם למבן עשרים שנה ומעלה וימצאם שלש מאות אלף בחור יוצא צבא אחז רמח וצנה
6 Ya kuma ɗauko sojan haya jarumawa dubu ɗari ɗaya daga Isra’ila a kan talenti ɗari na azurfa.
וישכר מישראל מאה אלף גבור חיל--במאה ככר כסף
7 Amma mutumin Allah ya zo wurinsa ya ce, “Ya sarki, waɗannan runduna daga Isra’ila ba za su tafi tare da kai ba, gama Ubangiji ba ya tare da Isra’ila, ba ya nan da wani cikin mutanen Efraim.
ואיש האלהים בא אליו לאמר המלך אל יבוא עמך צבא ישראל כי אין יהוה עם ישראל כל בני אפרים
8 Ko da ma ya tafi ya yi faɗa da ƙwazo a cikin yaƙi, Allah zai tumɓuke shi a gaban abokan gāba, gama Allah yana da iko yă taimaka ko yă tumɓuke.”
כי אם בא אתה עשה חזק למלחמה--יכשילך האלהים לפני אויב כי יש כח באלהים לעזור ולהכשיל
9 Amaziya ya tambayi mutumin Allah ya ce, “Amma game da talenti ɗarin da na biya saboda waɗannan rundunonin Isra’ila fa?” Mutumin Allah ya amsa, “Ubangiji zai ba ka fiye da wannan.”
ויאמר אמציהו לאיש האלהים ומה לעשות למאת הככר אשר נתתי לגדוד ישראל ויאמר איש האלהים יש ליהוה לתת לך הרבה מזה
10 Saboda haka Amaziya ya sallame rundunonin da suka zo daga Efraim, ya kuma mayar da su gida. Suka husata da Yahuda suka koma gida da fushi sosai.
ויבדילם אמציהו להגדוד אשר בא אליו מאפרים ללכת למקומם ויחר אפם מאד ביהודה וישובו למקומם בחרי אף
11 Sa’an nan Amaziya ya yi ƙarfin hali ya jagoranci mayaƙansa zuwa Kwarin Gishiri, inda ya kashe mutanen Seyir dubu goma.
ואמציהו התחזק וינהג את עמו וילך גיא המלח ויך את בני שעיר עשרת אלפים
12 Mayaƙan Yahuda suka kuma kama mutane dubu goma da rai, suka ɗauke su zuwa ƙwanƙolin dutsen, suka yi ta tunkuɗa su ƙasa suka yi kaca-kaca.
ועשרת אלפים חיים שבו בני יהודה ויביאום לראש הסלע וישליכום מראש הסלע וכלם נבקעו
13 Ana cikin haka, sai rundunar da Amaziya ya mai da su gida, waɗanda ba a bari suka tafi yaƙin ba, suka kai wa garuruwan Yahuda daga Samariya zuwa Bet-Horon hari. Suka kashe mutane dubu uku suka kwashe ganima mai yawan gaske.
ובני הגדוד אשר השיב אמציהו מלכת עמו למלחמה ויפשטו בערי יהודה משמרון ועד בית חורון ויכו מהם שלשת אלפים ויבזו בזה רבה
14 Da Amaziya ya dawo daga kisan mutanen Edom, sai ya dawo da allolin mutanen Seyir. Ya kafa su a matsayin allolinsa, ya rusuna musu, ya kuma miƙa musu hadayun ƙonawa.
ויהי אחרי בוא אמציהו מהכות את אדומים ויבא את אלהי בני שעיר ויעמידם לו לאלהים ולפניהם ישתחוה ולהם יקטר
15 Fushin Ubangiji ya yi ƙuna a kan Amaziya, sai ya aiki wani annabi wurinsa wanda ya ce, “Me ya sa ka nemi shawarar allolin mutanen nan, waɗanda ba za su cece mutanensu daga hannunka ba?”
ויחר אף יהוה באמציהו וישלח אליו נביא ויאמר לו למה דרשת את אלהי העם אשר לא הצילו את עמם מידך
16 Tun yana cikin magana, sai sarki ya ce masa, “Yaushe muka naɗa ka mai ba sarki shawara? Rufe mana baki! Me zai hana a kashe ka?” Sai annabin ya yi shiru, amma ya ce, “Na dai sani Allah ya riga ya shirya zai hallaka ka, saboda ka aikata wannan, ba ka kuma saurari shawarata ba.”
ויהי בדברו אליו ויאמר לו הליועץ למלך נתנוך--חדל לך למה יכוך ויחדל הנביא ויאמר ידעתי כי יעץ אלהים להשחיתך--כי עשית זאת ולא שמעת לעצתי
17 Bayan Amaziya sarkin Yahuda ya nemi shawara mashawartansa, sai ya kalubalanci Yowash ɗan Yehoyahaz, ɗan Yehu, sarkin Isra’ila, “Zo mu gamu fuska da fuska.”
ויועץ אמציהו מלך יהודה וישלח אל יואש בן יהואחז בן יהוא מלך ישראל לאמר לך נתראה פנים
18 Amma Yowash sarkin Isra’ila ya amsa wa Amaziya sarkin Yahuda ya ce, “Wata ƙaya ce a Lebanon, ta aika da saƙo wa itacen al’ul na Lebanon cewa, ‘Ka ba ɗana’yarka aure.’ Sai wani naman jeji na Lebanon ya zo ya tattake ƙayar.
וישלח יואש מלך ישראל אל אמציהו מלך יהודה לאמר החוח אשר בלבנון שלח אל הארז אשר בלבנון לאמר תנה את בתך לבני לאשה ותעבר חית השדה אשר בלבנון ותרמס את החוח
19 Ka ce wa kanka cewa ka ci Edom da yaƙi, yanzu kuwa kana fariya da ɗaga kai. Amma tsaya dai a gida! Me ya sa kake neman faɗa kana neman fāɗuwarka da ta Yahuda?”
אמרת הנה הכית את אדום ונשאך לבך להכביד עתה שבה בביתך--למה תתגרה ברעה ונפלת אתה ויהודה עמך
20 Amma Amaziya bai saurara ba gama Allah ya yi haka domin yă miƙa su ga Yehowash, domin sun nemi shawarar allolin Edom.
ולא שמע אמציהו--כי מהאלהים היא למען תתם ביד כי דרשו את אלהי אדום
21 Saboda haka Yowash sarkin Isra’ila ya kai yaƙi. Shi da Amaziya sarkin Yahuda suka fuskanci juna a Bet-Shemesh a Yahuda.
ויעל יואש מלך ישראל ויתראו פנים הוא ואמציהו מלך יהודה בבית שמש אשר ליהודה
22 Isra’ila ta fatattaki Yahuda, sai kowane mutum ya gudu zuwa gidansa.
וינגף יהודה לפני ישראל וינסו איש לאהליו
23 Yehowash sarkin Isra’ila ya kama Amaziya sarkin Yahuda, ɗan Yowash, ɗan Ahaziya a Bet-Shemesh. Sa’an nan Yehowash ya kawo shi Urushalima ya farfasa katangar Urushalima daga Ƙofar Efraim har zuwa Ƙofar Kusurwa, wani sashe mai tsawon ƙafa ɗari shida.
ואת אמציהו מלך יהודה בן יואש בן יהואחז תפש יואש מלך ישראל--בבית שמש ויביאהו ירושלם ויפרץ בחומת ירושלם משער אפרים עד שער הפונה ארבע מאות אמה
24 Ya kwashe dukan zinariya da azurfa da dukan kayayyakin da aka samu a haikalin Allah waɗanda suke a ƙarƙashin kulawar Obed-Edom, da kaya masu daraja na gidan sarki, da waɗanda aka kamo cikin yaƙi, ya kawo Samariya.
וכל הזהב והכסף ואת כל הכלים הנמצאים בבית האלהים עם עבד אדום ואת אוצרות בית המלך ואת בני התערבות וישב שמרון
25 Amaziya ɗan Yowash sarkin Yahuda ya rayu shekara goma sha biyar bayan mutuwar Yehowash ɗan Yehoyahaz sarkin Isra’ila.
ויחי אמציהו בן יואש מלך יהודה אחרי מות יואש בן יהואחז מלך ישראל--חמש עשרה שנה
26 Game da sauran ayyukan mulkin Amaziya, daga farko zuwa ƙarshe, an rubuta su a littafin sarakunan Yahuda da Isra’ila.
ויתר דברי אמציהו הראשנים והאחרונים--הלא הנם כתובים על ספר מלכי יהודה וישראל
27 Sa’ad da Amaziya ya bar bin Ubangiji, aka shirya masa maƙarƙashiya a Urushalima, sai ya gudu zuwa Lakish, amma suka aiki mutane suka bi shi zuwa Lakish, a can suka kashe shi.
ומעת אשר סר אמציהו מאחרי יהוה ויקשרו עליו קשר בירושלם וינס לכישה וישלחו אחריו לכישה וימיתהו שם
28 Aka dawo da shi a kan doki, aka binne shi tare da kakanninsa a Birnin Yahuda.
וישאהו על הסוסים ויקברו אתו עם אבתיו בעיר יהודה

< 2 Tarihi 25 >