< 2 Tarihi 24 >

1 Yowash yana da shekara goma sha bakwai sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi sarauta a Urushalima shekara arba’in. Sunan mahaifiyarsa Zibiya ce; ita daga Beyersheba.
בן שבע שנים יאש במלכו וארבעים שנה מלך בירושלם ושם אמו צביה מבאר שבע
2 Yowash ya yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji duka shekarun Yehohiyada firist.
ויעש יואש הישר בעיני יהוה כל ימי יהוידע הכהן
3 Yehohiyada ya zaɓi mata biyu dominsa, yana kuma da’ya’ya maza da’ya’ya mata.
וישא לו יהוידע נשים שתים ויולד בנים ובנות
4 Wani lokaci daga baya Yowash ya yanke shawara yă gyara haikalin Ubangiji.
ויהי אחרי כן היה עם לב יואש לחדש את בית יהוה
5 Ya tara firistoci da Lawiyawa wuri ɗaya ya ce musu, “Ku je garuruwan Yahuda ku karɓa kuɗin da ya kamata a biya shekara-shekara daga dukan Isra’ila, don gyaran haikalin Allahnku. Ku yi haka yanzu.” Amma Lawiyawa ba su yi haka nan da nan ba.
ויקבץ את הכהנים והלוים ויאמר להם צאו לערי יהודה וקבצו מכל ישראל כסף לחזק את בית אלהיכם מדי שנה בשנה ואתם תמהרו לדבר ולא מהרו הלוים
6 Saboda haka sarki ya kira Yehohiyada babban firist ya ce masa, “Me ya sa ba ka bukaci Lawiyawa su kawo harajin da Musa bawan Ubangiji ya ce a biya daga Yahuda da Urushalima da kuma taron Isra’ila domin Tentin Sujada Shaida ba?”
ויקרא המלך ליהוידע הראש ויאמר לו מדוע לא דרשת על הלוים להביא מיהודה ומירושלם את משאת משה עבד יהוה והקהל לישראל--לאהל העדות
7 Yanzu’ya’ya muguwar macen nan Ataliya maza sun fasa zuwa cikin haikalin Allah, suka kuma yi amfani da kayayyaki masu tsarki ma wa Ba’al.
כי עתליהו המרשעת בניה פרצו את בית האלהים וגם כל קדשי בית יהוה עשו לבעלים
8 Bisa ga umarnin sarki, aka yi akwati aka sa a waje, a mashigin haikalin Ubangiji.
ויאמר המלך ויעשו ארון אחד ויתנהו בשער בית יהוה חוצה
9 Aka yi umarni a Yahuda da Urushalima cewa ya kamata suka kawo wa Ubangiji harajin da Musa bawan Allah ya bukaci daga Isra’ila a hamada.
ויתנו קול ביהודה ובירושלם להביא ליהוה משאת משה עבד האלהים על ישראל--במדבר
10 Dukan hafsoshi da dukan mutane suka kawo nasu kuɗin da aka sa musu da farin ciki, suna zuba su cikin akwatin sai da ya cika.
וישמחו כל השרים וכל העם ויביאו וישליכו לארון עד לכלה
11 Duk sa’ad da Lawiyawa suka fito da akwatin zuwa ga hafsoshin sarki, suka kuma ga cewa akwatin yana da kuɗi mai yawa, sai magatakardan fada da hafsan babban firist su zo su juya kuɗin daga akwatin su mai da shi wurinsa. Sun riƙa yin haka kullum suka tara kuɗi mai yawa.
ויהי בעת יביא את הארון אל פקדת המלך ביד הלוים וכראותם כי רב הכסף ובא סופר המלך ופקיד כהן הראש ויערו את הארון וישאהו וישיבהו אל מקמו כה עשו ליום ביום ויאספו כסף לרב
12 Sarki da Yehohiyada suka ba da shi ga mutanen da suka yi aikin da ake bukata don haikalin Ubangiji. Suka ɗauki masu gini da kafintoci don su gyara haikalin Ubangiji, da kuma ma’aikatan ƙarafa da tagulla don su gyara haikalin.
ויתנהו המלך ויהוידע אל עושה מלאכת עבודת בית יהוה ויהיו שכרים חצבים וחרשים לחדש בית יהוה וגם לחרשי ברזל ונחשת לחזק את בית יהוה
13 Mutanen da suke lura da aikin natsattsu ne, kuma gyare-gyaren suka ci gaba a ƙarƙashinsu. Suka sāke gina haikalin Allah bisa ga ainihin fasalinsa suka ƙara masa ƙarfi.
ויעשו עשי המלאכה ותעל ארוכה למלאכה בידם ויעמידו את בית האלהים על מתכנתו--ויאמצהו
14 Da suka gama, suka kawo sauran kuɗin wa sarki da Yehohiyada, da su ne kuwa aka yi kayayyaki domin hidima da kuma domin hadayun ƙonawa, haka kuma kwanoni da sauran kayayyakin zinariya da azurfa. Muddin Yehohiyada yana raye, aka riƙa kawo hadayun ƙonawa a haikalin Ubangiji.
וככלותם הביאו לפני המלך ויהוידע את שאר הכסף ויעשהו כלים לבית יהוה כלי שרת והעלות וכפות וכלי זהב וכסף ויהיו מעלים עלות בבית יהוה תמיד כל ימי יהוידע
15 Yanzu Yehohiyada ya tsufa kuma cike da shekaru, ya kuwa mutu yana da shekara ɗari da talatin.
ויזקן יהוידע וישבע ימים וימת--בן מאה ושלשים שנה במותו
16 Aka binne shi tare da sarakuna a cikin Birnin Dawuda, saboda kirkin da ya yi a Isra’ila wa Allah da haikalinsa.
ויקברהו בעיר דויד עם המלכים כי עשה טובה בישראל ועם האלהים וביתו
17 Bayan mutuwar Yehohiyada, hafsoshin Yahuda suka zo suka yi mubaya’a wa sarki, ya kuma saurare su.
ואחרי מות יהוידע באו שרי יהודה וישתחוו למלך אז שמע המלך אליהם
18 Suka yashe haikalin Ubangiji Allah na kakanninsu, suka bauta wa ginshiƙan Ashera da kuma gumaka. Saboda laifinsu, fushin Allah ya sauko a kan Yahuda da Urushalima.
ויעזבו את בית יהוה אלהי אבותיהם ויעבדו את האשרים ואת העצבים ויהי קצף על יהודה וירושלם באשמתם זאת
19 Ko da yake Ubangiji ya aiki annabawa zuwa wurin mutane don su dawo da su gare shi, kuma ko da yake sun ba da shaida a kansu, ba su saurara ba.
וישלח בהם נבאים להשיבם אל יהוה ויעידו בם ולא האזינו
20 Sai Ruhun Allah ya sauko a kan Zakariya ɗan Yehohiyada firist. Ya tsaya a gaban mutane ya ce, “Ga abin da Allah ya ce, ‘Me ya sa ba ku yi biyayya da umarnan Ubangiji ba? Ba za ku yi nasara ba. Domin kun yashe Ubangiji, shi ma ya yashe ku.’”
ורוח אלהים לבשה את זכריה בן יהוידע הכהן ויעמד מעל לעם ויאמר להם כה אמר האלהים למה אתם עברים את מצות יהוה ולא תצליחו--כי עזבתם את יהוה ויעזב אתכם
21 Amma suka yi masa maƙarƙashiya, kuma ta wurin umarnin sarki suka jajjefe shi da duwatsu har ya mutu a filin haikalin Ubangiji.
ויקשרו עליו וירגמהו אבן במצות המלך בחצר בית יהוה
22 Sarki Yowash bai tuna da alherin da Yehohiyada mahaifin Zakariya ya nuna masa ba, sai ya kashe ɗansa, wanda ya ce yayinda yake mutuwa, “Bari Ubangiji yă dubi wannan yă kuma sāka maka.”
ולא זכר יואש המלך החסד אשר עשה יהוידע אביו עמו ויהרג את בנו וכמותו אמר ירא יהוה וידרש
23 Da shekara ta kewaye, mayaƙan Aram suka yi gāba da Yowash suka kai hari wa Yahuda da Urushalima suka kuma kashe dukan shugabannin mutane, suka aika da dukan ganima zuwa ga sarkinsu a Damaskus.
ויהי לתקופת השנה עלה עליו חיל ארם ויבאו אל יהודה וירושלם וישחיתו את כל שרי העם מעם וכל שללם שלחו למלך דרמשק
24 Ko da yake mayaƙan Arameyawa sun zo da mutane kaɗan kawai, Ubangiji ya sa suka ci nasara a kan sojojin Yahuda mafi yawa, don mutanen Yahuda sun rabu da Ubangiji Allah na kakanninsu, aka kuma hukunta Yowash.
כי במצער אנשים באו חיל ארם ויהוה נתן בידם חיל לרב מאד--כי עזבו את יהוה אלהי אבותיהם ואת יואש עשו שפטים
25 Sa’ad da Arameyawa suka janye, suka bar Yowash da mummunan rauni. Hafsoshinsa suka haɗa baki a kansa saboda kisan ɗan Yehohiyada firist da ya yi, suka kashe shi a kan gadonsa. Ta haka ya mutu aka kuma binne shi makabartan sarakuna.
ובלכתם ממנו כי עזבו אתו במחליים רבים התקשרו עליו עבדיו בדמי בני יהוידע הכהן ויהרגהו על מטתו וימת ויקברהו בעיר דויד ולא קברהו בקברות המלכים
26 Waɗanda suka haɗa bakin kuwa su ne Zabad ɗan Shimeyat wata mutuniyar Ammon da Yehozabad ɗan Shimrit wata mutuniyar Mowab.
ואלה המתקשרים עליו זבד בן שמעת העמונית ויהוזבד בן שמרית המואבית
27 Labarin’ya’yansa maza, annabce-annabce masu yawa game da shi, da tarihin gyaran haikalin Allah suna a rubuce a rubuce-rubuce a littafin sarakuna. Amaziya ɗansa kuwa ya gāje shi a matsayin sarki.
ובניו ורב (ירב) המשא עליו ויסוד בית האלהים--הנם כתובים על מדרש ספר המלכים וימלך אמציהו בנו תחתיו

< 2 Tarihi 24 >