< 2 Tarihi 23 >
1 A shekara ta bakwai Yehohiyada ya nuna ƙarfinsa. Ya yi alkawari da shugabanni na ɗari-ɗari, Azariya ɗan Yeroham, Ishmayel ɗan Yehohanan, Azariya ɗan Obed, Ma’asehiya ɗan Adahiya, da Elishafat ɗan Zikri.
2 Suka ratsa cikin Yahuda suka tattara Lawiyawa da shugabannin iyalan Isra’ilawa daga dukan garuruwa. Sa’ad da suka zo Urushalima,
3 dukan taron suka yi alkawari da sarki a haikalin Allah. Yehohiyada ya ce musu, “Ɗan sarki zai yi mulki yadda Ubangiji ya yi alkawari game da zuriyar Dawuda.
4 Yanzu ga abin da za ku yi, shi ne, kashi ɗaya bisa uku na firistoci da Lawiyawa waɗanda za su yi aiki a Asabbaci su yi tsaro a ƙofofi,
5 kashi ɗaya bisa ukunku a fadan sarki, kashi ɗaya bisa uku kuma, a Ƙofar Harsashi, sai kuma dukan sauran mutane su kasance a filayen haikalin Ubangiji.
6 Babu wanda zai shiga haikalin Ubangiji sai firistoci da Lawiyawan da suke a aiki; za su iya shiga domin su tsarkaku ne, amma sauran mutane za su kiyaye abin da Ubangiji ya sa su yi.
7 Lawiyawa za su tsaya kewaye da sarki, kowane mutum da makamansa a hannunsa. Duk wanda ya shiga haikali sai a kashe shi. Ku tsaya kusa da sarki a duk inda ya tafi.”
8 Lawiyawa da dukan mutanen Yahuda suka yi yadda Yehohiyada firist ya umarta. Kowanne ya ɗauki mutanensa, waɗanda suke aiki a Asabbaci da waɗanda suka gama aiki, gama Yehohiyada firist bai bar waɗansu ɓangarori ba.
9 Sa’an nan ya ba shugabannin māsu da garkuwoyi manya da ƙanana na sarki Dawuda, waɗanda suke cikin haikalin Allah.
10 Ya kuma sa dukan mutane, kowanne da makaminsa a hannunsa, kewaye da sarki, kusa da bagade da kuma haikali, daga gefen kudu zuwa gefen arewa na haikali.
11 Yehohiyada da’ya’yansa maza suka fitar da ɗan sarki suka sa rawani a kansa; suka miƙa masa alkawarin, suka kuma yi shelarsa a matsayin sarki. Suka shafe shi suka kuma tā da murya suna cewa, “Ran sarki yă daɗe!”
12 Sa’ad da Ataliya ta ji surutun mutane suna gudu suna yabon sarki, sai ta tafi wurinsu a haikalin Ubangiji.
13 Ta duba, a can kuwa ga sarki, tsaye kusa da ginshiƙinsa a mashigi. Manyan sojoji da masu bushe-bushe suna kusa da sarki, dukan mutanen ƙasar kuwa suna farin ciki suna busa ƙahoni, mawaƙa kuma da kayan kiɗi suna bi da yabo. Sai Ataliya ta yage rigunanta ta yi ihu tana cewa, “Cin amanar ƙasa! Cin amanar ƙasa!”
14 Yehohiyada firist ya fito da shugabanni waɗanda suke shugabancin rundunar sojoji, ya ce musu, “Ku fitar da ita tsakanin sojoji ku kuma kashe duk wanda ya bi ta da takobi.” Gama firist ya ce, “Kada ku kashe ta a haikalin Ubangiji.”
15 Saboda haka suka kama ta yayinda take kaiwa mashigin Ƙofar Doki a filin fada, a can suka kashe ta.
16 Sa’an nan Yehohiyada ya yi alkawari cewa shi da mutane da kuma sarki za su zama mutanen Ubangiji.
17 Dukan mutane suka tafi haikalin Ba’al suka rurrushe shi. Suka farfashe bagadan da gumakan, suka kuma kashe Mattan firist na Ba’al a gaban bagadan.
18 Sa’an nan Yehohiyada ya sa aikin lura da haikalin Ubangiji a hannuwan firistoci, waɗanda suke Lawiyawan da Dawuda ya ba su aikin haikali don su miƙa hadayun ƙonawa na Ubangiji kamar yadda yake a rubuce a Dokar Musa, da farin ciki da kuma rerawa, kamar yadda Dawuda ya umarta.
19 Ya kuma sa matsaran ƙofofi a ƙofofin haikalin Ubangiji don kada wani da ba shi da tsarki yă shiga.
20 Ya ɗauki shugabannin ɗari-ɗari, manyan gari, shugabannin mutane da dukan mutanen ƙasar tare da shi ya saukar da sarki daga haikalin Ubangiji. Suka shiga fada ta Ƙofar Bisa suka kuma zaunar da sarki a kujerar sarauta,
21 sai dukan mutanen ƙasar suka yi farin ciki. Birnin kuwa ya samu zaman lafiya domin an kashe Ataliya da takobi.