< 2 Tarihi 22 >
1 Mutanen Urushalima suka mai da Ahaziya, autan Yehoram, sarki a madadinsa, da yake’yan hari, waɗanda suka zo tare da Larabawa cikin sansani, sun kashe dukan manyan’ya’yansa. Saboda haka Ahaziya ɗan Yeroham sarkin Yahuda ya fara mulki.
[阿哈齊雅即位行惡]耶路撒冷居民立了約蘭的小兒阿哈齊雅繼位為王,因為與阿剌伯人同來攻營的匪徒,將他的哥哥全都殺了,因此猶大王約蘭的兒子阿哈齊雅即位為王。
2 Ahaziya yana da shekara ashirin da biyu sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara guda. Sunan mahaifiyarsa Ataliya ce, jikanyar Omri.
阿哈齊雅即位年二十二歲,在耶路撒冷作王一年;他的母親名叫阿塔里雅,是敖默黎的孫女。
3 Shi ma ya yi tafiya a hanyoyin gidan Ahab, gama mahaifiyarsa ta ƙarfafa shi yă yi abin da ba shi da kyau.
阿哈齊雅也走了阿哈布家的道路,因為他母親主使他作惡。
4 Ya aikata mugayen ayyuka a gaban Ubangiji, yadda gidan Ahab ta yi, gama bayan mutuwar mahaifinsa, sai gidan Ahab ta zama masu ba shi shawara, shawarar da ta kai shi ga lalacewa.
他行了上主視為惡的事,同阿哈布家一樣,因為自他父親死後,阿哈布家人給他出主意,使他趨於滅亡。
5 Ya kuma bi shawararsu sa’ad da ya tafi tare da Yoram ɗan Ahab sarkin Isra’ila don yă yaƙi Hazayel sarkin Aram a Ramot Gileyad. Sai Arameyawa suka yi wa Yoram rauni;
他隨從了他們的計謀,同以色列王阿哈布的兒子耶曷蘭,往辣摩特基肋阿得與阿蘭王哈匝耳交戰;阿蘭人擊傷了耶曷蘭,
6 saboda haka ya dawo Yezireyel don yă yi jinyar raunin da suka yi masa a Rama cikin yaƙinsa da Hazayel sarkin Aram. Sa’an nan Azariya ɗan Yehoram sarkin Yahuda ya gangara zuwa Yezireyel don yă ga Yoram ɗan Ahab domin ya ji rauni.
耶曷蘭遂回依次勒耳,治療他在辣摩特與阿蘭在哈匝耳交戰時所受的傷。猶大王約蘭的兒子阿哈齊雅因阿哈布的兒子耶曷蘭患病,就下到依次勒耳去探望他。[阿哈齊雅被殺]
7 Ta wurin ziyarar Yoram, Allah ya kawo fāɗuwar Ahaziya. Sa’ad da Ahaziya ya iso, ya tafi tare da Yoram domin yă sadu da Yehu ɗan Nimshi, wanda Ubangiji ya shafe don yă hallaka gidan Ahab.
阿哈齊雅去看望耶曷蘭反而遇害,這原是出於天主;因為他到了以後,便與耶曷蘭出擊尼默史的孫子耶胡,而耶胡即是上主用油所傅,為消滅阿哈布家的。
8 Yayinda Yehu yake hukunta wa gidan Ahab, sai ya sami fadawan Yahuda da kuma’ya’yan dangin Ahaziya maza, waɗanda suke yi wa Ahaziya hidima, sai ya kashe su.
耶胡討伐阿哈布家時,遇到了猶大的一些首領和事奉阿哈齊砑的姪子們,便將他們殺了;
9 Ya kuma sa aka nemi Ahaziya. Aka kamo shi sa’ad da ya ɓuya a Samariya, suka kawo shi wurin Yehu, suka kashe shi, suka binne shi, gama sun ce, “Shi jikan Yehoshafat ne, wanda ya nemi Ubangiji da dukan zuciyarsa.” Ta haka babu wani a gidan Ahaziya da yake da ƙarfin cin gaba da mulkin.
然後去尋找阿哈齊雅;阿哈齊雅當時藏在撒瑪黎雅,人將他拿住,解到耶胡那裏,耶胡也將他殺了,以後人也埋葬了他,因為人說:「他究竟是那一心尋求上主的約沙法特的孫子。」這樣,阿哈齊雅家中沒有一個人能即位為王。[母后篡位]
10 Sa’ad da Ataliya mahaifiyar Ahaziya ta ga cewa ɗanta ya mutu, sai ta tashi ta hallaka dukan’yan gidan sarautar Yahuda.
阿哈齊雅的母親阿塔里雅見自己的兒子死了,便起來殲滅了猶大家中所有的王族後裔。
11 Amma Yehosheba,’yar Sarki Yehoram, ta ɗauki Yowash ɗan Ahaziya ta sace shi daga cikin’ya’yan gidan sarauta waɗanda ake shiri a kashe, ta sa shi tare da mai renonsa a ɗakin kwana. Haka fa, Yehosheba’yar sarki Yoram, matar Yehohiyada firist, ta yi, gama ita’yar’uwar Ahaziya ce, ta ɓoye Yowash don kada Ataliya tă kashe shi.
約蘭王的女兒約舍巴,將阿哈齊雅的兒子約阿士由被殺的太子中偷了出來,將他和他的乳母藏在聖殿的寢室裏。約舍巴─約蘭王的女兒,約雅達大司祭的妻子,阿哈齊雅的姐妹─就這樣藏匿了約阿士,沒有被阿塔里雅殺害。
12 Ya kasance a ɓoye tare da su a haikalin Allah shekara shida, yayinda Ataliya take mulkin ƙasar.
約阿士與她們在天主殿內隱藏了六年,當時由阿塔里雅主持國政。