< 2 Tarihi 21 >
1 Yehoshafat ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi tare da su a Birnin Dawuda. Sai Yehoram ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki.
2 ’Yan’uwan Yehoram,’ya’yan Yehoshafat maza su ne, Azariya, Yehiyel, Zakariya, Azariyahu, Mika’ilu da Shefatiya. Dukan waɗannan su ne’ya’yan Yehoshafat sarkin Isra’ila maza.
3 Mahaifinsu ya ba su kyautai masu yawa na azurfa da zinariya da kayayyaki masu daraja, tare da birane masu katanga a Yahuda, amma ya ba da mulki ga Yehoram domin shi ne ɗan farinsa.
4 Sa’ad da Yehoram ya kafa kansa sosai a bisa mulkin mahaifinsa, sai ya kashe dukan’yan’uwansa da takobi tare da waɗansu sarakunan Isra’ila.
5 Yehoram yana da shekara talatin da biyu sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara takwas.
6 Ya yi tafiya a hanyoyin sarakunan Isra’ila, kamar yadda gidan Ahab ta yi, gama ya auri’yar Ahab. Ya aikata mugayen ayyuka a idon Ubangiji.
7 Duk da haka, domin alkawarin da Ubangiji ya yi wa Dawuda, Ubangiji bai so yă hallaka gidan Dawuda ba. Ubangiji ya riga ya yi alkawari zai ci gaba da riƙe fitila domin Dawuda da zuriyarsa har abada.
8 A zamanin Yehoram, Edom ya tayar wa Yahuda ya kuma naɗa sarkinsa.
9 Saboda haka Yehoram ya tafi can tare da shugabannin sojojinsa da kuma dukan keken yaƙinsa. Mutanen Edom suka kewaye shi da shugabannin keken yaƙinsa, amma ya tashi ya fatattaki su da dare.
10 Har yă zuwa yau Edom na tawaye a kan Yahuda. Libna ya yi tawaye a lokaci guda, domin Yehoram ya yashe Ubangiji Allah na kakanninsa.
11 Ya gina masujadan kan tudu a tuddan Yahuda, ya kuma sa mutanen Urushalima suka yi karuwanci, ya sa Yahuda suka kauce.
12 Yehoram ya sami wasiƙa daga Iliya annabi, wadda ta ce, “Ga abin da Ubangiji Allah na kakanka Dawuda ya ce, ‘Ba ka yi tafiya a hanyoyin mahaifinka Yehoshafat ko Asa sarkin Yahuda ba.
13 Amma ka yi tafiya a hanyoyin sarakunan Isra’ila, ka sa Yahuda ya kauce, ka kuma sa mutanen Urushalima suka yi karuwanci, kamar yadda gidan Ahab ta yi. Ka kuma kashe’yan’uwanka, membobi gidan mahaifinka, mutanen da suka fi ka kirki.
14 Saboda haka a yanzu Ubangiji yana shirin ya bugi mutanenka,’ya’yanka maza, matanka da kuma kome da yake naka, da bugu mai ƙarfi.
15 Kai kuma za ka kamu da ciwon hanji wanda zai yi ta cinka kowace rana sai har hanjinka sun fito.’”
16 Ubangiji ya sa Filistiyawa da Larabawa waɗanda suke zama kusa da Kushawa su yi gāba da Yehoram
17 Suka yaƙi Yahuda, suka kai masa hari, suka kwashe dukan abubuwa masu kyau da suka samu a fadan sarki, tare da’ya’yansa maza da kuma matansa. Ba wanda aka bari, sai dai Ahaziya autansa.
18 Bayan dukan wannan, sai Ubangiji ya sa wa Yehoram cuta marar warkarwa ta ciki.
19 Cikin lokaci, a ƙarshen shekara ta biyu, sai hanjin cikinsa suka fito saboda cutar, ya kuma mutu cikin tsananin zafi. Mutanensa suka hura wuta don girmama shi, kamar yadda suka yi wa kakanninsa.
20 Yehoram yana da shekara talatin da biyu sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara takwas. Ya mutu, ba ma wanda ya kula, aka kuma binne shi a Birnin Dawuda, amma ba a makabartan sarakuna ba.