< 2 Tarihi 20 >

1 Bayan wannan, Mowabawa da Ammonawa tare da waɗansu Meyunawa suka zo su yaƙi Yehoshafat.
ויהי אחרי כן באו בני מואב ובני עמון ועמהם מהעמונים על יהושפט--למלחמה
2 Sai waɗansu mutane suka zo suka faɗa wa Yehoshafat, “Ga babban runduna tana zuwa a kanka daga Edom, daga ƙetaren Teku, daga Aram. Ta ma kai Hazazon Tamar” (wato, En Gedi).
ויבאו ויגידו ליהושפט לאמר בא עליך המון רב מעבר לים מארם והנם בחצצון תמר היא עין גדי
3 A firgice, Yehoshafat ya yanke shawara yă nemi nufin Ubangiji, ya kuma yi shelar azumi a dukan Yahuda.
וירא ויתן יהושפט את פניו לדרוש ליהוה ויקרא צום על כל יהודה
4 Mutanen Yahuda suka taru gaba ɗaya don su nemi taimako daga wurin Ubangiji, tabbatacce suka fito daga kowane garin Yahuda don su neme shi.
ויקבצו יהודה לבקש מיהוה גם מכל ערי יהודה באו לבקש את יהוה
5 Sa’an nan Yehoshafat ya miƙe tsaye a taron Yahuda da Urushalima a haikalin Ubangiji a sabon filin
ויעמד יהושפט בקהל יהודה וירושלם--בבית יהוה לפני החצר החדשה
6 ya ce, “Ya Ubangiji Allah na kakanninmu, ba kai ne Allah wanda yake sama ba? Kana mulki a bisa dukan mulkokin ƙasashe. Iko da girma suna a hannunka, kuma ba wanda zai iya tsayayya da kai.
ויאמר יהוה אלהי אבתינו הלא אתה הוא אלהים בשמים ואתה מושל בכל ממלכות הגוים ובידך כח וגבורה ואין עמך להתיצב
7 Ya Allahnmu, ba kai ba ne ka kore mazaunan wannan ƙasa a gaban mutanenka Isra’ila ka kuma ba da ita har abada ga zuriyar Ibrahim abokinka?
הלא אתה אלהינו הורשת את ישבי הארץ הזאת מלפני עמך ישראל ותתנה לזרע אברהם אהבך--לעולם
8 Sun yi zama a cikinta suka kuma yi gina wuri mai tsarki a cikinta domin Sunanka cewa,
וישבו בה ויבנו לך בה מקדש לשמך לאמר
9 ‘In masifa ta zo mana, ko takobin hukunci, ko annoba ko yunwa, za mu tsaya a gabanka a gaban wannan haikalin da yake ɗauke da Sunanka, mu kuma yi kuka gare ka cikin azaba, za ka kuwa ji mu, ka cece mu.’
אם תבוא עלינו רעה חרב שפוט ודבר ורעב נעמדה לפני הבית הזה ולפניך כי שמך בבית הזה ונזעק אליך מצרתנו ותשמע ותושיע
10 “Yanzu kuma ga mutanen Ammon, da na Mowab, da na Dutsen Seyir, waɗanda ka hana Isra’ilawa su kai musu yaƙi sa’ad da suka fito daga ƙasar Masar, su ne mutanen da Isra’ila suka ƙyale, ba su hallaka su ba.
ועתה הנה בני עמון ומואב והר שעיר אשר לא נתתה לישראל לבוא בהם בבאם מארץ מצרים כי סרו מעליהם ולא השמידום
11 Yau ga yadda suke so su biya mu. Su suke so su kore mu daga ƙasar da ka ba mu gādo.
והנה הם--גמלים עלינו לבוא לגרשנו מירשתך אשר הורשתנו
12 Ya Allahnmu, ba za ka hukunta su ba? Gama ba mu da ƙarfin fuskantar wannan babbar rundunar da take so ta yaƙe mu. Ba mu san abin da za mu yi ba, mu dai mun zuba maka ido.”
אלהינו הלא תשפט בם כי אין בנו כח לפני ההמון הרב הזה הבא עלינו ואנחנו לא נדע מה נעשה--כי עליך עינינו
13 Dukan mazan Yahuda, tare da matansu da yaransu da ƙananansu, suka tsaya a gaban Ubangiji.
וכל יהודה--עמדים לפני יהוה גם טפם נשיהם ובניהם
14 Sa’an nan Ruhun Ubangiji ya sauko a kan Yahaziyel ɗan Zakariya, ɗan Benahiya, ɗan Yehiyel, ɗan Mattaniya, wani Balawe kuma zuriyar Asaf, yayinda yake tsaye a cikin taron.
ויחזיאל בן זכריהו בן בניה בן יעיאל בן מתניה הלוי--מן בני אסף היתה עליו רוח יהוה בתוך הקהל
15 Ya ce, “Saurara, Sarki Yehoshafat da dukan waɗanda suke zama a Yahuda da Urushalima! Ga abin da Ubangiji ya ce muku, ‘Kada ku ji tsoro ko ku fid da zuciya saboda wannan babbar runduna. Gama yaƙin ba naku ba ne, amma na Allah.
ויאמר הקשיבו כל יהודה וישבי ירושלם והמלך יהושפט כה אמר יהוה לכם אתם אל תיראו ואל תחתו מפני ההמון הרב הזה--כי לא לכם המלחמה כי לאלהים
16 Gobe ku fito ku gangara ku yaƙe su. Za su yi ta haurawa ta Mashigin Ziz, ku kuwa za ku same su a ƙarshen kwari a Hamadan Yeruwel.
מחר רדו עליהם הנם עלים במעלה הציץ ומצאתם אתם בסוף הנחל פני מדבר ירואל
17 Ba lalle ba ne ku yi wannan yaƙi. Ku dai, ku ja dāgā, ku tsaya kurum ku ga nasarar da Ubangiji zai ba ku, ya Yahuda da Urushalima. Kada ku ji tsoro; kada ku karai. Ku fito don ku fuskance su gobe, Ubangiji kuwa zai kasance tare ku.’”
לא לכם להלחם בזאת התיצבו עמדו וראו את ישועת יהוה עמכם יהודה וירושלם אל תיראו ואל תחתו--מחר צאו לפניהם ויהוה עמכם
18 Yehoshafat ya rusuna da fuskarsa har ƙasa, dukan mutanen Yahuda da Urushalima suka fāɗi rubda ciki suka yi sujada a gaban Ubangiji.
ויקד יהושפט אפים ארצה וכל יהודה וישבי ירושלם נפלו לפני יהוה להשתחות ליהוה
19 Sa’an nan waɗansu Lawiyawa daga Kohatawa da Korayawa suka tashi tsaye suka yabe Ubangiji, Allah na Isra’ila, da babbar murya sosai.
ויקמו הלוים מן בני הקהתים ומן בני הקרחים--להלל ליהוה אלהי ישראל בקול גדול למעלה
20 Da sassafe suka tashi suka nufi Hamadan Tekowa. Yayinda suka kama hanya, Yehoshafat ya tsaya ya ce, “Ku saurare ni, Yahuda da mutanen Urushalima! Ku amince da Ubangiji Allahnku za a kuwa kafa ku; ku amince da annabawansa za ku kuwa yi nasara.”
וישכימו בבקר ויצאו למדבר תקוע ובצאתם עמד יהושפט ויאמר שמעוני יהודה וישבי ירושלם--האמינו ביהוה אלהיכם ותאמנו האמינו בנביאיו והצליחו
21 Bayan suka yi shawara tare da shugabanni, sai ya zaɓi mutanen da za su ja gaban sojoji suna waƙa ga Ubangiji suna yabonsa saboda tsarkinsa suna cewa, “Ku yi godiya ga Ubangiji, gama ƙaunarsa dawwammamiya ce har abada.”
ויועץ אל העם ויעמד משררים ליהוה ומהללים להדרת קדש--בצאת לפני החלוץ ואמרים הודו ליהוה כי לעולם חסדו
22 Da suka fara waƙa, suna kuma yabo, sai Ubangiji ya kai hari a kan mutanen Ammon da Mowab da Dutsen Seyir, waɗanda suka kawo hari a Yahuda, aka kuwa ci su da yaƙi.
ובעת החלו ברנה ותהלה נתן יהוה מארבים על בני עמון מואב והר שעיר הבאים ליהודה--וינגפו
23 Mutanen Ammon da Mowab suka tasar wa mazaunan Dutsen Seyir, suka hallaka su ƙaƙaf. Sa’ad da suka karkashe mazaunan Seyir sai suka fāɗa wa juna, suka yi ta hallaka juna.
ויעמדו בני עמון ומואב על ישבי הר שעיר--להחרים ולהשמיד וככלותם ביושבי שעיר עזרו איש ברעהו למשחית
24 Sa’ad da mutanen Yahuda suka zo wurin da yake fuskantar hamada, suka duba ta wajen babban rundunar, sai suka ga gawawwaki birjik a ƙasa; babu wani wanda ya kuɓuta.
ויהודה בא על המצפה למדבר ויפנו אל ההמון והנם פגרים נפלים ארצה ואין פליטה
25 Sa’ad da Yehoshafat da jama’arsa suka je kwasar ganima, sai suka sami shanu masu yawan gaske, da kayayyaki, da tufafi, da abubuwa masu daraja, waɗanda suka yi ta kwasa har suka gaji. Kwana uku suka yi suna kwasar ganimar saboda yawanta.
ויבא יהושפט ועמו לבז את שללם וימצאו בהם לרב ורכוש ופגרים וכלי חמדות וינצלו להם לאין משא ויהיו ימים שלושה בזזים את השלל--כי רב הוא
26 A rana ta huɗu sai suka taru a Kwarin Beraka, inda suka yabi Ubangiji. Wannan ne ya sa ake kiransa Kwarin Beraka har wa yau.
וביום הרבעי נקהלו לעמק ברכה--כי שם ברכו את יהוה על כן קראו את שם המקום ההוא עמק ברכה--עד היום
27 Sa’an nan Yehoshafat ya jagoranci dukan mutanen Yahuda da Urushalima suka dawo da farin ciki zuwa Urushalima, gama Ubangiji ya ba su dalilin farin ciki a kan abokan gābansu.
וישבו כל איש יהודה וירושלם ויהושפט בראשם לשוב אל ירושלם בשמחה כי שמחם יהוה מאויביהם
28 Suka shiga Urushalima suka shiga haikalin Ubangiji da kiɗin molaye da sarewa da kuma garayu.
ויבאו ירושלם בנבלים ובכנרות ובחצצרות--אל בית יהוה
29 Tsoron Allah ya kama dukan mulkokin ƙasashe sa’ad da suka ji yadda Ubangiji ya yi yaƙi a kan abokan gāban Isra’ila.
ויהי פחד אלהים על כל ממלכות הארצות בשמעם--כי נלחם יהוה עם אויבי ישראל
30 Mulkin Yehoshafat kuwa ya zauna lafiya, gama Allahnsa ya ba shi hutu a kowane gefe.
ותשקט מלכות יהושפט וינח לו אלהיו מסביב
31 Ta haka Yehoshafat ya yi mulki a bisa Yahuda. Yana da shekara talatin da biyar sa’ad da ya zama sarkin Yahuda, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara ashirin da biyar. Sunan mahaifiyarsa Azuba ce,’yar Shilhi.
וימלך יהושפט על יהודה--בן שלשים וחמש שנה במלכו ועשרים וחמש שנה מלך בירושלם ושם אמו עזובה בת שלחי
32 Ya yi tafiya a hanyoyin mahaifinsa Asa bai kuwa kauce daga gare su ba; ya yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji.
וילך בדרך אביו אסא--ולא סר ממנה לעשות הישר בעיני יהוה
33 Duk da haka ba a kawar da masujadai kan tudu ba, domin har yanzu mutanen ba su tsayar da zukatansu ga Allahn kakanninsu ba.
אך הבמות לא סרו ועוד העם לא הכינו לבבם לאלהי אבתיהם
34 Sauran ayyukan mulkin Yehoshafat, daga farko zuwa ƙarshe, an rubuta su a tarihin Yehu ɗan Hanani, waɗanda aka rubuta a littafin sarakunan Isra’ila.
ויתר דברי יהושפט הראשנים והאחרנים--הנם כתובים בדברי יהוא בן חנני אשר העלה על ספר מלכי ישראל
35 Daga baya, Yehoshafat sarkin Yahuda ya haɗa kai da Ahaziya sarkin Isra’ila, wanda yake da laifin mugunta.
ואחרי כן אתחבר יהושפט מלך יהודה עם אחזיה מלך ישראל הוא הרשיע לעשות
36 Ya yarda da shi su gina jiragen ruwan kasuwanci. Bayan aka gina waɗannan a Eziyon Geber,
ויחברהו עמו לעשות אניות ללכת תרשיש ויעשו אניות בעציון גבר
37 Eliyezer ɗan Dodabahu na Maresha ya yi annabci a kan Yehoshafat cewa, “Domin ka haɗa kai da Ahaziya, Ubangiji zai hallaka abin da ka yi.” Jiragen ruwan kuwa suka farfashe, ba a kuwa iya sa su je kasuwanci ba.
ויתנבא אליעזר בן דדוהו ממרשה על יהושפט לאמר כהתחברך עם אחזיהו פרץ יהוה את מעשיך וישברו אניות ולא עצרו ללכת אל תרשיש

< 2 Tarihi 20 >