< 2 Tarihi 19 >
1 Sa’ad da Yehoshafat sarkin Yahuda ya dawo zuwa fadansa a Urushalima lafiya,
2 Yehu mai duba, ɗan Hanani, ya fita don yă tarye shi, ya kuma ce wa sarki, “Ya yi kyau ke nan da ka taimaki mugu ka kuma ƙaunaci waɗanda suke ƙin Ubangiji? Da yake ka yi haka fushin Ubangiji yana a kanka
3 Duk da haka an sami wani abin kirki a wurinka, gama ka kawar da ginshiƙan Ashera a ƙasar, ka kuma sa zuciyarka a kan neman Allah.”
4 Yehoshafat ya zauna a Urushalima, ya kuma fita yana shiga cikin mutane daga Beyersheba zuwa ƙasar tudun Efraim ya kuma juyar da su ga Ubangiji Allah na kakanninsu.
5 Ya naɗa alƙalai a kowanne daga cikin biranen katanga na Yahuda a ƙasar.
6 Ya faɗa musu, “Ku lura da abin da kuke yi, gama shari’ar da kuke yi ba ta mutum ba ce, amma ta Ubangiji ce, yana tare da ku sa’ad da kuke yanke shari’a.
7 Yanzu fa ku ji tsoron Ubangiji. Ku yi hankali a kan abin da kuke yi, gama Ubangiji Allahnmu ba ya sonkai ko nuna wariya ko cin hanci.”
8 A Urushalima kuma, Yehoshafat ya naɗa waɗansu Lawiyawa, firistoci da kawunan iyalan Isra’ilawa don su tabbatar da an bi dokar Ubangiji, su kuma sasanta tsakanin mutane. A Urushalima za su zauna.
9 Ya ba su waɗannan umarnai, “Ku yi aikinku da aminci da tsoron Ubangiji da dukan zuciyarku.
10 Cikin kowane batun da ya zo gabanku daga’yan’uwanku waɗanda suke zama a birane, ko batun na kisa ne ko kuwa waɗansu batuttuwan da suka shafi doka, umarnai, ƙa’idodi ko farillai, dole ku ja musu kunne kada su yi wa Ubangiji zunubi; in ba haka ba fushinsa zai sauko a kanku da’yan’uwanku. Ku yi wannan, ta haka ba za ku kuwa yi zunubi ba.
11 “Amariya, babban firist, shi ne zai shugabance ku a kan dukan al’amuran da suke na wajen Ubangiji, Zebadiya ɗan Ishmayel kuwa, shugabanku a kan dukan al’amuran da suka shafi sarki, Lawiyawa kuma za su zama a matsayin manya a gabanku. Ku yi abubuwa da ƙarfin hali, bari kuma Ubangiji yă kasance tare da masu yin gaskiya.”