< 2 Tarihi 18 >

1 Yanzu fa Yehoshafat ya wadace ƙwarai yana kuma da girma, ya kuma haɗa kansa da Ahab ta wurin aure.
ויהי ליהושפט עשר וכבוד לרב ויתחתן לאחאב׃
2 Bayan’yan shekaru sai ya gangara don yă ziyarci Ahab a Samariya. Ahab kuwa ya yanka tumaki da shanu masu yawa dominsa da kuma mutanen da suke tare da shi, ya kuma lallashe shi yă yaƙi Ramot Gileyad.
וירד לקץ שנים אל אחאב לשמרון ויזבח לו אחאב צאן ובקר לרב ולעם אשר עמו ויסיתהו לעלות אל רמות גלעד׃
3 Ahab sarkin Isra’ila ya tambayi Yehoshafat sarkin Yahuda ya ce, “Za ka tafi tare da ni mu yaƙi Ramot Gileyad?” Yehoshafat ya amsa ya ce, “Ni kamar kai ne, kuma mutanena kamar naka ne; za mu tafi tare da kai a yaƙin.”
ויאמר אחאב מלך ישראל אל יהושפט מלך יהודה התלך עמי רמת גלעד ויאמר לו כמוני כמוך וכעמך עמי ועמך במלחמה׃
4 Amma Yehoshafat ya kuma ce wa sarkin Isra’ila, “Da fari mu nemi bishewar Ubangiji.”
ויאמר יהושפט אל מלך ישראל דרש נא כיום את דבר יהוה׃
5 Saboda haka sarkin Isra’ila ya tattara annabawa duka, mutane ɗari huɗu, ya kuma tambaye su, “Mu tafi yaƙi a kan Ramot Gileyad ko kada mu tafi?” Suka amsa “Tafi, gama Allah zai ba da shi cikin hannun sarki.”
ויקבץ מלך ישראל את הנבאים ארבע מאות איש ויאמר אלהם הנלך אל רמת גלעד למלחמה אם אחדל ויאמרו עלה ויתן האלהים ביד המלך׃
6 Amma Yehoshafat ya yi tambaya ya ce, “Babu wani annabin Ubangiji a nan da za mu tambaya?”
ויאמר יהושפט האין פה נביא ליהוה עוד ונדרשה מאתו׃
7 Sarki Isra’ila ya amsa wa Yehoshafat, “Akwai guda har yanzu mai suna Mikahiya ɗan Imla, za mu iya nemi nufin Ubangiji daga gare shi, sai dai ba na sonsa domin bai taɓa yin annabci wani abu mai kyau game da ni ba, sai kullum masifa.” Yehoshafat ya amsa ya ce, “Kada sarki yă faɗa haka.”
ויאמר מלך ישראל אל יהושפט עוד איש אחד לדרוש את יהוה מאתו ואני שנאתיהו כי איננו מתנבא עלי לטובה כי כל ימיו לרעה הוא מיכיהו בן ימלא ויאמר יהושפט אל יאמר המלך כן׃
8 Saboda haka sarkin Isra’ila ya kira ɗaya daga cikin ma’aikatansa ya ce, “A kawo Mikahiya ɗan Imla nan da nan.”
ויקרא מלך ישראל אל סריס אחד ויאמר מהר מיכהו בן ימלא׃
9 Saye da rigunan sarakuna, sarki Isra’ila da Yehoshafat sarkin Yahuda suna zaune a kan kujerunsu na mulki a masussuka ta ƙofar shigar Samariya, tare da dukan annabawa suna ta annabci a gabansu.
ומלך ישראל ויהושפט מלך יהודה יושבים איש על כסאו מלבשים בגדים וישבים בגרן פתח שער שמרון וכל הנביאים מתנבאים לפניהם׃
10 To, fa, Zedekiya ɗan Kena’ana ya yi ƙahonin ƙarfe, ya kuma furta, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Da waɗannan za ka sassoki Arameyawa sai sun hallaka.’”
ויעש לו צדקיהו בן כנענה קרני ברזל ויאמר כה אמר יהוה באלה תנגח את ארם עד כלותם׃
11 Dukan sauran annabawan suka yi irin annabcin nan. Suka ce, “A haura zuwa Ramot Gileyad a yi nasara, gama Ubangiji zai ba da shi cikin hannun sarki.”
וכל הנבאים נבאים כן לאמר עלה רמת גלעד והצלח ונתן יהוה ביד המלך׃
12 Ɗan saƙon da ya tafi don yă kawo Mikahiya kuwa ya ce masa, “Duba, kowannen a cikin annabawa ya yi faɗin nasara wa sarki. Don haka kai ma ka yi maganar da za tă gamshi sarki kamar yadda suka yi.”
והמלאך אשר הלך לקרא למיכיהו דבר אליו לאמר הנה דברי הנבאים פה אחד טוב אל המלך ויהי נא דברך כאחד מהם ודברת טוב׃
13 Amma Mikahiya ya ce, “Na rantse da ran Ubangiji, zan faɗa masa kawai abin da Allahna ya faɗa.”
ויאמר מיכיהו חי יהוה כי את אשר יאמר אלהי אתו אדבר׃
14 Da suka iso, sarki ya tambaye shi, “Mika, mu tafi mu yaƙi Ramot Gileyad, ko kada mu tafi?” Ya amsa, “Kai masa yaƙi za ka kuwa yi nasara, gama za a ba da su a hannunka.”
ויבא אל המלך ויאמר המלך אליו מיכה הנלך אל רמת גלעד למלחמה אם אחדל ויאמר עלו והצליחו וינתנו בידכם׃
15 Sarki ya ce masa, “Sau nawa zan sa ka rantse don ka faɗa gaskiya a cikin sunan Ubangiji?”
ויאמר אליו המלך עד כמה פעמים אני משביעך אשר לא תדבר אלי רק אמת בשם יהוה׃
16 Sa’an nan Mikahiya ya amsa, “Na ga dukan Isra’ila sun warwatsu a kan tuddai kamar tumakin da ba su da makiyaya, kuma Ubangiji ya ce, ‘Waɗannan mutane ba su da maigida. Bari kowanne yă tafi gida cikin salama.’”
ויאמר ראיתי את כל ישראל נפוצים על ההרים כצאן אשר אין להן רעה ויאמר יהוה לא אדנים לאלה ישובו איש לביתו בשלום׃
17 Sarkin Isra’ila ya ce wa Yehoshafat, “Ban faɗa maka cewa bai taɓa yin annabci wani abu mai kyau game da ni, in ba masifa ba?”
ויאמר מלך ישראל אל יהושפט הלא אמרתי אליך לא יתנבא עלי טוב כי אם לרע׃
18 Mikahiya ya ci gaba, “Saboda haka sai ka ji maganar Ubangiji. Na ga Ubangiji yana zama a kan kursiyinsa tare da dukan rundunar sama tsaye a damansa da hagunsa.
ויאמר לכן שמעו דבר יהוה ראיתי את יהוה יושב על כסאו וכל צבא השמים עמדים על ימינו ושמאלו׃
19 Ubangiji kuwa ya ce, ‘Wa zai ruɗe Ahab sarki Isra’ila zuwa yaƙi da Ramot Gileyad da kuma zuwa mutuwarsa a can?’ “Wani ya ba da wata shawara, wani kuma wata dabam.
ויאמר יהוה מי יפתה את אחאב מלך ישראל ויעל ויפל ברמות גלעד ויאמר זה אמר ככה וזה אמר ככה׃
20 A ƙarshe, wani ruhu ya zo gaba, ya tsaya a gaban Ubangiji ya ce, ‘Zan ruɗe shi.’ “Ubangiji ya yi tambaya, ‘Ta wace hanya?’
ויצא הרוח ויעמד לפני יהוה ויאמר אני אפתנו ויאמר יהוה אליו במה׃
21 “Ya ce, ‘Zan tafi in zama ruhun ƙarya a bakunan dukan annabawansa.’ “Ubangiji ya ce, ‘Za ka yi nasara a ruɗinsa. Ka tafi, ka yi haka.’
ויאמר אצא והייתי לרוח שקר בפי כל נביאיו ויאמר תפתה וגם תוכל צא ועשה כן׃
22 “To yanzu, Ubangiji ya sa ruhun ruɗu a bakunan waɗannan annabawanka. Ubangiji ya ƙayyade masifa dominka.”
ועתה הנה נתן יהוה רוח שקר בפי נביאיך אלה ויהוה דבר עליך רעה׃
23 Sai Zedekiya ɗan Kena’ana ya haura ya mari Mikahiya a fuska. Ya ce, “Ta wace hanya ce ruhun Ubangiji ya fita daga gare ni ya zo ya yi magana da kai?”
ויגש צדקיהו בן כנענה ויך את מיכיהו על הלחי ויאמר אי זה הדרך עבר רוח יהוה מאתי לדבר אתך׃
24 Mikahiya ya amsa ya ce, “Za ka gane a ranar da ka je ka ɓuya a can cikin ɗaki.”
ויאמר מיכיהו הנך ראה ביום ההוא אשר תבוא חדר בחדר להחבא׃
25 Sa’an nan sarkin Isra’ila ya umarta, “Ɗauki Mikahiya ku aika da shi zuwa ga Amon mai mulkin birni da kuma ga Yowash ɗan sarki,
ויאמר מלך ישראל קחו את מיכיהו והשיבהו אל אמון שר העיר ואל יואש בן המלך׃
26 ku ce ga abin da sarki ya ce, ‘Ku jefa wannan mutum a kurkuku kada kuma ku ba shi wani abu sai dai burodi da ruwa har sai na dawo lafiya.’”
ואמרתם כה אמר המלך שימו זה בית הכלא והאכלהו לחם לחץ ומים לחץ עד שובי בשלום׃
27 Mikahiya ya furta ya ce, “Idan har ka dawo lafiya, to, Ubangiji bai yi magana ta wurina ba.” Ya kuma ƙara da cewa, “Dukanku mutane, ku lura da maganata!”
ויאמר מיכיהו אם שוב תשוב בשלום לא דבר יהוה בי ויאמר שמעו עמים כלם׃
28 Saboda haka sarkin Isra’ila da Yehoshafat sarkin Yahuda suka haura zuwa Ramot Gileyad.
ויעל מלך ישראל ויהושפט מלך יהודה אל רמת גלעד׃
29 Sarkin Isra’ila ya ce wa Yehoshafat, “Zan ɓad da kama in shiga yaƙin, amma ka sa kayanka na sarauta.” Saboda haka sarkin Isra’ila ya ɓad da kama ya shiga cikin yaƙin.
ויאמר מלך ישראל אל יהושפט התחפש ובוא במלחמה ואתה לבש בגדיך ויתחפש מלך ישראל ויבאו במלחמה׃
30 To, fa, sarkin Aram ya umarce shugabannin keken yaƙinsa ya ce, “Kada ku yaƙi kowa, ƙarami ko babba, sai dai sarkin Isra’ila.”
ומלך ארם צוה את שרי הרכב אשר לו לאמר לא תלחמו את הקטן את הגדול כי אם את מלך ישראל לבדו׃
31 Sa’ad da shugabannin kekunan yaƙi suka ga Yehoshafat, sai suka yi tsammani, “Wannan ne sarkin Isra’ila.” Saboda haka suka juya don su yaƙe shi, amma Yehoshafat ya yi ihu, Ubangiji kuma ya taimake shi. Allah ya janye su daga gare shi,
ויהי כראות שרי הרכב את יהושפט והמה אמרו מלך ישראל הוא ויסבו עליו להלחם ויזעק יהושפט ויהוה עזרו ויסיתם אלהים ממנו׃
32 gama sa’ad da shugabannin keken yaƙi suka ga cewa ba shi ne sarkin Isra’ila ba, sai suka daina binsa.
ויהי כראות שרי הרכב כי לא היה מלך ישראל וישבו מאחריו׃
33 Amma wani ya harba kibiya haka kawai, sai kibiyar ta sami sarki Ahab na Isra’ila a kafaɗa tsakanin rigar yaƙinsa na ƙarfe da ƙarfen ƙirjinsa. Sai sarki ya ce wa mai tuƙan keken yaƙi, “Juya ka fitar da ni daga wurin yaƙin. An ji mini rauni.”
ואיש משך בקשת לתמו ויך את מלך ישראל בין הדבקים ובין השרין ויאמר לרכב הפך ידיך והוצאתני מן המחנה כי החליתי׃
34 Duk yini yaƙi ya yi ta cin gaba, sarkin Isra’ila kuwa ya jingina kansa a cikin keken yaƙinsa yana duban Arameyawa har yamma. Sa’an nan a fāɗuwar rana sai ya mutu.
ותעל המלחמה ביום ההוא ומלך ישראל היה מעמיד במרכבה נכח ארם עד הערב וימת לעת בוא השמש׃

< 2 Tarihi 18 >