< 2 Tarihi 16 >

1 A shekara ta talatin da shida ta mulkin Asa, Ba’asha sarkin Isra’ila ya haura don yă yaƙi Yahuda da Rama mai katanga, don kuma yă hana wani daga fita ko shiga yankin Asa sarkin Yahuda.
בשנת שלשים ושש למלכות אסא עלה בעשא מלך ישראל על יהודה ויבן את הרמה--לבלתי תת יוצא ובא לאסא מלך יהודה
2 Sai Asa ya ɗauki azurfa da zinariya daga ma’ajin haikalin Ubangiji da kuma na fadansa ya aika wa Ben-Hadad sarkin Aram, wanda yake mulki a Damaskus.
ויצא אסא כסף וזהב מאצרות בית יהוה--ובית המלך וישלח אל בן הדד מלך ארם היושב בדרמשק לאמר
3 Ya ce, “Bari yarjejjeniya ta kasance tsakani na da kai kamar yadda ya kasance tsakanin mahaifina da mahaifinka. Dubi ina aika maka azurfa da zinariya. Yanzu ka yanke yarjejjeniya da Ba’asha sarkin Isra’ila domin yă janye daga gare ni.”
ברית ביני ובינך ובין אבי ובין אביך הנה שלחתי לך כסף וזהב--לך הפר בריתך את בעשא מלך ישראל ויעלה מעלי
4 Ben-Hadad ya yarda da Sarki Asa ya kuma aika da manyan hafsoshin mayaƙansa a kan garuruwan Isra’ila. Suka ci Iyon, Dan, Abel-Mayim da kuma dukan biranen ajiya na Naftali.
וישמע בן הדד אל המלך אסא וישלח את שרי החילים אשר לו אל ערי ישראל ויכו את עיון ואת דן ואת אבל מים ואת כל מסכנות ערי נפתלי
5 Da Ba’asha ya ji wannan, ya daina ginin Rama ya yashe aikinsa.
ויהי כשמע בעשא ויחדל מבנות את הרמה וישבת את מלאכתו
6 Sa’an nan Sarki Asa ya kawo dukan mutanen Yahuda, suka kuma kwashe duwatsu da katako daga Rama waɗanda Ba’asha yake amfani da su. Da su ne Asa ya gina Geba da Mizfa.
ואסא המלך לקח את כל יהודה וישאו את אבני הרמה ואת עציה אשר בנה בעשא ויבן בהם את גבע ואת המצפה
7 A lokacin Hanani mai duba ya zo wurin Asa sarkin Yahuda ya ce masa, “Don ka dogara ga sarkin Aram, ba kuwa ga Ubangiji Allahnka ba ne mayaƙan sarkin Aram sun kuɓuce daga hannunka.
ובעת ההיא בא חנני הראה אל אסא מלך יהודה ויאמר אליו בהשענך על מלך ארם ולא נשענת על יהוה אלהיך על כן נמלט חיל מלך ארם מידך
8 Ai, Kushawa da Libiyawa rundunar sojoji ne masu yawan gaske, suna kuma da kekunan yaƙi da mahayan dawakai masu yawa ƙwarai. Amma duk da haka, saboda ka dogara ga Ubangiji, ya kuwa ba da su cikin hannunka.
הלא הכושים והלובים היו לחיל לרב לרכב ולפרשים--להרבה מאד ובהשענך על יהוה נתנם בידך
9 Gama gaban Ubangiji yana ko’ina a duniya don yă ƙarfafa waɗanda zukatansu suke binsa cikin aminci. Ka yi wauta, daga yanzu nan gaba za ka yi ta yaƙi.”
כי יהוה עיניו משטטות בכל הארץ להתחזק עם לבבם שלם אליו--נסכלת על זאת כי מעתה יש עמך מלחמות
10 Sai Asa ya yi fushi sosai da mai duban saboda wannan; ya yi fushi ƙwarai har ya sa aka jefa shi a kurkuku. A lokaci guda kuma Asa ya fara gwada wa mutane azaba.
ויכעס אסא אל הראה ויתנהו בית המהפכת--כי בזעף עמו על זאת וירצץ אסא מן העם בעת ההיא
11 Ayyukan mulkin Asa, daga farko zuwa ƙarshe, suna a rubuce a littafin sarakunan Yahuda da Isra’ila.
והנה דברי אסא הראשונים והאחרונים--הנם כתובים על ספר המלכים ליהודה וישראל
12 A shekara ta talatin da tara ta mulkinsa, Asa ya kamu da wata cuta a ƙafarsa. Ko da yake cutar ta yi tsanani, duk d haka ma a cikin ciwonsa bai nemi taimako daga Ubangiji ba, sai dai daga likitoci.
ויחלא אסא בשנת שלושים ותשע למלכותו ברגליו עד למעלה חליו וגם בחליו לא דרש את יהוה כי ברפאים
13 Sa’an nan a shekara ta arba’in da ɗaya ta mulkinsa, Asa ya mutu ya kuma huta tare da kakanninsa.
וישכב אסא עם אבתיו וימת בשנת ארבעים ואחת למלכו
14 Suka binne shi a kabarin da ya fafe wa kansa a Birnin Dawuda. Suka sa shi a makara wadda aka rufe da kayan yaji da kuma turare dabam-dabam da aka niƙa, suka kuma ƙuna babbar wuta don girmama shi.
ויקברהו בקברתיו אשר כרה לו בעיר דויד וישכיבהו במשכב אשר מלא בשמים וזנים מרקחים במרקחת מעשה וישרפו לו שרפה גדולה עד למאד

< 2 Tarihi 16 >