< 2 Tarihi 15 >

1 Sai Ruhun Allah ya sauko a kan Azariya ɗan Oded.
上帝的靈感動俄德的兒子亞撒利雅。
2 Ya fita ya je ya sadu da Asa ya kuma faɗa masa, “Ka saurare ni, Asa da kuma dukan Yahuda da Benyamin. Ubangiji yana tare da ku sa’ad da kuke tare da shi. In kuka neme shi, za ku same shi, amma in kuka yashe shi, zai yashe ku.
他出來迎接亞撒,對他說:「亞撒和猶大、便雅憫眾人哪,要聽我說:你們若順從耶和華,耶和華必與你們同在;你們若尋求他,就必尋見;你們若離棄他,他必離棄你們。
3 Tun da daɗewa Isra’ila ba su da Allah na gaskiya, babu firist da zai koyar, kuma babu doka.
以色列人不信真神,沒有訓誨的祭司,也沒有律法,已經好久了;
4 Amma cikin wahalarsu suka juya ga Ubangiji, Allah na Isra’ila, suka kuma neme shi, suka kuwa same shi.
但他們在急難的時候歸向耶和華-以色列的上帝,尋求他,他就被他們尋見。
5 A waɗancan kwanaki akwai hatsari a yin tafiye-tafiye, gama dukan mazaunan ƙasashe suna cikin babbar damuwa.
那時,出入的人不得平安,列國的居民都遭大亂;
6 Wata ƙasa takan murƙushe wata, wani birni kuma yakan murƙushe wani, domin Allah ya wahalshe su da kowace irin damuwa.
這國攻擊那國,這城攻擊那城,互相破壞,因為上帝用各樣災難擾亂他們。
7 Amma game da ku, ku ƙarfafa kada ku fid da zuciya, gama za a ba ku ladan aikinku.”
現在你們要剛強,不要手軟,因你們所行的必得賞賜。」
8 Sa’ad da Asa ya ji waɗannan kalmomin da annabcin Azariya ɗan Oded annabi ya faɗa, sai ya sami ƙarfi hali. Ya kawar da gumaka masu banƙyama daga dukan ƙasar Yahuda da Benyamin da kuma daga garuruwan da ya ci da yaƙi a ƙasar tudu ta Efraim. Ya gyaggyara bagaden Ubangiji da yake a gaban shirayin haikalin Ubangiji.
亞撒聽見這話和俄德兒子先知亞撒利雅的預言,就壯起膽來,在猶大、便雅憫全地,並以法蓮山地所奪的各城,將可憎之物盡都除掉,又在耶和華殿的廊前重新修築耶和華的壇;
9 Sa’an nan ya tattara dukan Yahuda da Benyamin da kuma mutane daga Efraim, Manasse da Simeyon waɗanda suke zaune a cikinsu, gama jama’a mai girma ta zo wurinsa daga Isra’ila sa’ad da suka ga cewa Ubangiji Allahnsa yana tare da shi.
又招聚猶大、便雅憫的眾人,並他們中間寄居的以法蓮人、瑪拿西人、西緬人。有許多以色列人歸降亞撒,因見耶和華-他的上帝與他同在。
10 Suka taru a Urushalima a wata na uku na shekara ta goma sha biyar ta mulkin Asa.
亞撒十五年三月,他們都聚集在耶路撒冷。
11 A lokacin suka miƙa hadaya bijimai ɗari bakwai da tumaki da kuma awaki dubu bakwai ga Ubangiji daga ganimar da suka dawo da ita.
當日他們從所取的擄物中,將牛七百隻、羊七千隻獻給耶和華。
12 Suka yi alkawari don su nemi Ubangiji Allah na kakanninsu, da dukan zuciyarsu da kuma dukan ransu.
他們就立約,要盡心盡性地尋求耶和華-他們列祖的上帝。
13 Aka kashe dukan waɗanda ba su nemi Ubangiji, Allah na Isra’ila ba, ko ƙarami ko babba, namiji ko ta mace.
凡不尋求耶和華-以色列上帝的,無論大小、男女,必被治死。
14 Suka yi rantsuwa ga Ubangiji da babbar murya, da ihu da garayu da ƙahoni.
他們就大聲歡呼,吹號吹角,向耶和華起誓。
15 Dukan Yahuda suka yi farin ciki game da rantsuwar domin sun yi rantsuwar gabagadi. Suka nemi Allah da gaske, suka kuma same shi. Saboda haka Ubangiji ya ba su hutu a kowane gefe.
猶大眾人為所起的誓歡喜;因他們是盡心起誓,盡意尋求耶和華,耶和華就被他們尋見,且賜他們四境平安。
16 Sarki Asa ya tuɓe mahaifiyar mahaifiyarsa daga matsayinta na mahaifiyar sarauniya, domin ta gina ginshiƙin banƙyama na Ashera. Asa ya rurrushe shi, ya farfasa shi ya kuma ƙone shi a Kwarin Kidron.
亞撒王貶了他祖母瑪迦太后的位,因她造了可憎的偶像亞舍拉。亞撒砍下她的偶像,搗得粉碎,燒在汲淪溪邊。
17 Ko da yake bai kawar da masujadan kan tudu daga Isra’ila ba, zuciyar Asa ta cika da bin Ubangiji dukan kwanakinsa.
只是邱壇還沒有從以色列中廢去,然而亞撒的心一生誠實。
18 Ya kawo azurfa da zinariya da kayayyaki a haikalin Allah waɗanda shi da mahaifinsa suka keɓe.
亞撒將他父所分別為聖、與自己所分別為聖的金銀和器皿都奉到上帝的殿裏。
19 Ba a ƙara yin yaƙi ba sai a shekara ta talatin da biyar ta mulkin Asa.
從這時直到亞撒三十五年,都沒有爭戰的事。

< 2 Tarihi 15 >