< 2 Tarihi 11 >

1 Sa’ad da Rehobowam ya iso Urushalima, ya tattara mayaƙa dubu ɗari takwas daga gidan Yahuda da Benyamin, don su yi yaƙi da Isra’ila su sāke mai da mulki wa Rehobowam.
Došavši u Jeruzalem, skupi sav dom Judin i Benjaminov, sto i osamdeset tisuća vrsnih ratnika, da udare na Izraela i da Roboamu vrate kraljevstvo.
2 Amma wannan maganar Ubangiji ta zo ga Shemahiya mutumin Allah.
Ali dođe Jahvina riječ Božjem čovjeku Šemaji:
3 “Faɗa wa Rehobowam ɗan Solomon sarkin Yahuda da kuma dukan Isra’ilawan da suke a Yahuda da Benyamin,
“Kaži Salomonovu sinu Roboamu, judejskomu kralju, i svim Izraelcima u Judinu i Benjaminovu plemenu:
4 ‘Ga abin da Ubangiji ya ce kada ku haura don ku yi yaƙi da’yan’uwanku. Ku tafi gida kowannenku, gama wannan yi na ne.’” Saboda haka suka yi biyayya ga maganar Ubangiji suka kuma koma daga takawa don yaƙi da Yerobowam.
Ovako veli Jahve: 'Ne idite se tući s braćom! Neka se svatko vrati svojoj kući, jer je ovo poteklo od mene.'” I oni poslušaše riječ Jahvinu, vratiše se i ne udariše na Jeroboama.
5 Rehobowam ya zauna a Urushalima ya kuma gina garuruwa don kāriya a cikin Yahuda.
Roboam, stolujući u Jeruzalemu, poče dizati tvrde gradove po Judeji.
6 Betlehem, Etam, Tekowa,
Tako je sagradio Betlehem, Etam, Tekou,
7 Bet-Zur, Soko, Adullam,
Bet Sur, Sokon, Adulam,
8 Gat, Maresha, Zif,
Gat, Maresu, Zif,
9 Adorayim, Lakish, Azeka,
Adorajim, Lakiš, Azeku,
10 Zora, Aiyalon da Hebron. Waɗannan su ne garuruwan katanga a cikin Yahuda da Benyamin.
Soru, Ajalon i Hebron, tvrde gradove u Judinu i Benjaminovu plemenu.
11 Ya ƙarfafa kāriyarsu ya kuma sa shugabannin mayaƙa a cikinsu, tare da tanadin abinci, man zaitun da kuma ruwan inabi.
Utvrdivši gradove, postavi im zapovjednike i dovuče zalihe hrane, ulja i vina;
12 Ya sa garkuwoyi da māsu a cikin dukan biranen, ya kuma sa suka zama da ƙarfi. Saboda haka Yahuda da Benyamin suka zama nasa.
u svaki pojedini grad stavi štitova i kopalja i utvrdi ih vrlo jako. Tako je on imao Judino i Benjaminovo pleme.
13 Firistoci da Lawiyawa daga dukan yankuna ko’ina a Isra’ila suka haɗa kai da shi.
Svećenici i leviti, koji su bili po svem Izraelu, pristupiše k njemu iz svih krajeva.
14 Lawiyawa suka ma bar makiyayansu da mallakarsu, suka zo Yahuda da Urushalima domin Yerobowam da’ya’yansa maza sun ƙi su a matsayin firistocin Ubangiji.
Leviti ostaviše pašnjake i posjed te otiđoše u Judeju i Jeruzalem, jer ih je bio odbacio Jeroboam i njegovi sinovi da ne obavljaju svećeničku službu Jahvi,
15 Yerobowam ya naɗa firistocinsa domin masujadan kan tudu da kuma domin gumakan nan na akuya da maraƙin da ya yi.
a postavio je svećenike za uzvišice, za jarce i za telad koju je napravio.
16 Waɗanda suke daga kowane kabilar Isra’ila waɗanda suka sa zuciya a kan neman Ubangiji, Allah na Isra’ila, suka bi Lawiyawa zuwa Urushalima don su miƙa hadayu ga Ubangiji Allah na kakanninsu.
Za njima su iz svih izraelskih plemena dolazili u Jeruzalem da žrtvuju Jahvi, Bogu svojih otaca, oni koji su srcem tražili Jahvu, Boga Izraelova.
17 Suka ƙarfafa mulkin Yahuda suka kuma goyi bayan Rehobowam ɗan Solomon shekaru uku, suna tafiya a hanyoyin Dawuda da Solomon a wannan lokaci.
Tako su utvrdili judejsko kraljevstvo i osokolili Salomonova sina Roboama za tri godine, jer su tri godine živjeli poput Davida i Salomona.
18 Rehobowam ya auri Mahalat,’yar Yerimot ɗan Dawuda wadda Abihayil’yar Eliyab ɗan Yesse ta haifa.
Roboam je sebi uzeo za žemu Mahalatu, kćer Davidova sina Jerimota, i Abihajilu, kćer Jišajeva sina Eliaba,
19 Ta haifa masa’ya’ya maza. Yewush, Shemariya da Zaham.
koja mu rodi sinove: Jeuša, Šemarju i Zahama.
20 Sa’an nan ya auri Ma’aka’yar Absalom, wadda ta haifa masa Abiya, Attai, Ziza da kuma Shelomit.
A poslije nje oženio se Abšalomovom kćerju Maakom, koja mu rodi Abiju, Etaja, Zizu i Šelomita.
21 Rehobowam ya ƙaunaci Ma’aka’yar Absalom fiye da sauran matansa da ƙwarƙwaransa. Duka-duka dai ya auri mata goma sha takwas da ƙwarƙwarai sittin, yana da’ya’ya maza ashirin da takwas da’ya’ya mata sittin.
Roboam je ljubio Abšalomovu kćer Maaku više od svih svojih žena i inoča, iako je uzeo osamnaest žena i šezdeset inoča i rodio dvadeset i osam sinova i šezdeset kćeri.
22 Rehobowam ya naɗa Abiya ɗan Ma’aka yă zama babba yerima a cikin’yan’uwansa, don dai yă naɗa shi sarki.
I Roboam postavi Maakina sina Abiju za poglavara i kneza nad njegovom braćom, jer ga je naumio postaviti za kralja.
23 Ya yi hikima, ya watsar da waɗansu’ya’yansa a dukan yankunan Yahuda da Benyamin, da kuma a dukan birane masu katanga. Ya ba su tanadi mai yawa ya kuma aurar musu mata masu yawa.
I, mudro radeći, razmjesti sinove po svim judejskim i Benjaminovim krajevima, po svim tvrdim gradovima, davši im hrane izobila i poženivši ih sa mnogo žena.

< 2 Tarihi 11 >