< 2 Tarihi 10 >

1 Rehobowam ya tafi Shekem, gama dukan Isra’ilawa sun je can don su naɗa shi sarki.
Roboam se rendit à Sichem, car tout Israël était venu à Sichem pour l'établir roi.
2 Da Yerobowam ɗan Nebat ya ji wannan (a lokacin yana a Masar, inda ya gudu daga Sarki Solomon ya tafi), sai ya dawo daga Masar.
Quand Jéroboam, fils de Nébat, qui était en Égypte, où il s'était enfui de devant le roi Salomon, l'eut appris, il revint d'Égypte.
3 Saboda haka suka aika a zo da Yerobowam, sai shi da dukan Isra’ila suka je wurin Rehobowam suka ce masa.
Or on l'avait envoyé appeler. Ainsi Jéroboam et tout Israël vinrent et parlèrent à Roboam, en disant:
4 “Mahaifinka ya sa mana kaya masu nauyi a kanmu, amma yanzu ka sauƙaƙa mana aiki mai zafin nan da kuma kaya masu nauyin da ya sa a kanmu, mu kuwa za mu bauta maka.”
Ton père a mis sur nous un joug pesant; allège maintenant cette rude servitude de ton père, et ce joug pesant qu'il nous a imposé, et nous te servirons.
5 Rehobowam ya amsa, “Ku dawo gare ni cikin kwana uku.” Saboda haka mutanen suka watse.
Alors il leur dit: Revenez vers moi dans trois jours. Ainsi le peuple s'en alla.
6 Sai Sarki Rehobowam ya nemi shawarar dattawan da suka yi wa mahaifinsa Solomon hidima a lokacin da yake da rai, ya tambaye suya ce, “Wace shawara za ku ba ni don in amsa wa waɗannan mutane?”
Et le roi Roboam consulta les vieillards qui avaient été auprès de Salomon, son père, pendant sa vie, et il leur dit: Quelle réponse me conseillez-vous de faire à ce peuple?
7 Suka amsa suka ce, “In za ka ji tausayi waɗannan mutane ka kuma gamshe su, ka kuma ba su amsar da ta dace, kullum za su zama bayinka.”
Et ils lui répondirent en ces termes: Si tu es bon envers ce peuple, si tu es bienveillant envers eux, et que tu leur dises de bonnes paroles, ils seront tes serviteurs à toujours.
8 Amma Rehobowam ya ƙi shawarar da dattawa suka ba shi ya kuma nemi shawarar matasan da suka yi girma tare, suke kuma yin masa hidima.
Mais il laissa le conseil que les vieillards lui avaient donné, et il consulta les jeunes gens qui avaient grandi avec lui, et qui se tenaient devant lui.
9 Ya tambaye su ya ce, “Mece ce shawararku? Yaya zan amsa wa waɗannan mutanen da suke ce mini, ‘Ka sauƙaƙa nauyin da mahaifinka ya sa a kanmu’?”
Et il leur dit: Que me conseillez-vous de répondre à ce peuple, qui m'a parlé, et m'a dit: Allège le joug que ton père a mis sur nous?
10 Matasan da suka yi girma tare shi suka amsa, “Faɗa wa mutanen da suke ce maka, ‘Mahaifinka ya sa kaya masu nauyi a kanmu, amma ka sauƙaƙa nauyinmu.’ Ka faɗa musu, ‘Ƙaramin yatsana ya fi ƙugun mahaifina kauri.
Et les jeunes gens qui avaient grandi avec lui, lui répondirent, en disant: Tu diras ainsi à ce peuple qui t'a parlé, et t'a dit: Ton père a mis sur nous un joug pesant, mais toi, allège-le; tu leur répondras ainsi: Mon petit doigt est plus gros que les reins de mon père.
11 Mahaifina ya sa muku kaya masu nauyi; zan ma sa mafi nauyi. Mahaifina ya bulale ku da bulala; zan bulale ku da kunamai.’”
Or, mon père vous a imposé un joug pesant, mais moi, je rendrai votre joug plus pesant encore. Mon père vous a châtiés avec des fouets, mais moi, je vous châtierai avec des fouets garnis de pointes.
12 Bayan kwana uku sai Yerobowam da dukan mutane suka dawo wurin Rehobowam, yadda sarki ya ce, “Ku dawo gare ni cikin kwana uku.”
Trois jours après, Jéroboam avec tout le peuple vint vers Roboam, suivant ce que le roi avait dit: Revenez vers moi dans trois jours.
13 Sarki ya amsa musu da kakkausar murya. Ya ƙi shawarar dattawan,
Mais le roi leur répondit rudement, et le roi Roboam ne suivit point le conseil des vieillards;
14 ya kuma bi shawarar matasan ya ce, “Mahaifina ya sa muku kaya masu nauyi; zan ma sa mafi nauyi. Mahaifina ya bulale ku da bulala; zan bulale ku da kunamai.”
Il leur parla suivant le conseil des jeunes gens, et leur dit: Mon père a mis sur vous un joug pesant; mais moi, j'y ajouterai encore. Mon père vous a châtiés avec des fouets; mais moi, je vous châtierai avec des fouets garnis de pointes.
15 Saboda haka sarki bai saurari mutane ba, gama wannan juyin al’amura daga Allah ne, don a cika maganar Ubangiji da ya yi ga Yerobowam ɗan Nebat ta wurin Ahiya mutumin Shilo.
Le roi n'écouta donc point le peuple; car cela était dispensé de la part de Dieu, afin que l'Éternel ratifiât la parole qu'il avait prononcée par Achija, le Silonite, à Jéroboam, fils de Nébat.
16 Sa’ad da Isra’ila suka ga sarki ya ƙi yă saurare su, sai suka amsa wa sarki, suka ce, “Wanda rabo muke da shi a wurin Dawuda, wanda sashe muke da shi daga ɗan Yesse? Kowa yă koma tentinsa, ya Isra’ila! Ka lura da gidanka, ya Dawuda!” Saboda haka dukan Isra’ilawa suka tafi gida.
Et quand tout Israël vit que le roi ne les écoutait point, le peuple répondit au roi, en disant: Quelle part avons-nous avec David? Nous n'avons point d'héritage avec le fils d'Isaï. Israël, chacun à ses tentes! Maintenant, David, pourvois à ta maison. Ainsi tout Israël s'en alla dans ses tentes.
17 Amma game da Isra’ilawan da suke zama a garuruwan Yahuda kuwa, Rehobowam ya ci gaba da yin mulki a bisansu.
Mais quant aux enfants d'Israël qui habitaient les villes de Juda, Roboam régna sur eux.
18 Sarki Rehobowam ya aiki Hadoram wanda yake lura da aikin dole, amma Isra’ilawa suka jajjefe shi da duwatsu har ya mutu. Sarki Rehobowam kuwa ya gaggauta ya shiga keken yaƙinsa ya gudu zuwa Urushalima.
Alors le roi Roboam envoya Hadoram, qui était préposé aux impôts; mais les enfants d'Israël l'assommèrent à coups de pierres, et il mourut. Et le roi Roboam se hâta de monter sur un char pour s'enfuir à Jérusalem.
19 Ta haka Isra’ila ya kasance cikin tawaye a kan gidan Dawuda har yă zuwa wannan rana.
C'est ainsi qu'Israël s'est rebellé contre la maison de David, jusqu'à ce jour.

< 2 Tarihi 10 >