< 1 Timoti 1 >

1 Bulus, manzon Kiristi Yesu ta wurin umarnin Allah Mai Cetonmu da kuma na Yesu Kiristi begenmu,
奉我們的救主天主,和作我們希望的基督耶穌的命,作基督耶穌宗徒的保祿,
2 Zuwa ga Timoti ɗana na gaske cikin bangaskiya. Alheri, jinƙai da kuma salama daga Allah Uba da Kiristi Yesu Ubangijinmu, su kasance tare da kai.
致書給在信德上作我真子的弟茂德。願恩寵、仁慈與平安,由天主父和我們的主基督耶穌賜與你!
3 Kamar yadda na gargaɗe ka sa’ad da zan je Makidoniya, ka zauna can Afisa domin ka umarci waɗansu mutane kada su koyar da ƙa’idodin ƙarya nan gaba
當我往馬其頓去的時候,曾請救你留在厄弗所,為的是要你訓令某些人,不要講異端道理,
4 ko su ba da kansu ga tatsuniyoyi da ƙididdigar asali marar iyaka. Waɗannan suna kawo faɗa a maimakon aikin Allah wanda yake ta wurin bangaskiya.
也不要探求無稽的傳說,以及無窮的祖譜,因為這些事只會激起爭辯,對於天主所立的那基於信德的救世計劃,都毫無益處。
5 Maƙasudin wannan umarnin dai ƙauna ce, wadda take zuwa daga zuciya mai tsabta da lamiri mai kyau da kuma sahihiyar bangaskiya.
這訓令的目的就是愛,即由純潔的心,光明磊落的良心和真誠信仰所發出的愛;
6 Waɗansu sun bauɗe daga waɗannan al’amura, suka koma ga maganganu marasa ma’ana.
但有些人離開這些而轉向了空談;
7 So suke su zama malaman doka, ba tare da fahimtar abin da suke faɗa ba, balle abubuwan da suke ta nacewa a kai.
願意充當法學士,卻不明白自己所主張的是什麼事。
8 Mun san cewa doka tana da kyau in an yi amfani da ita yadda ya kamata.
我們知道法律原是好的,只要人用的合法;
9 Mun kuma san cewa an yi doka ba domin masu adalci ba sai dai masu tawaye, da marasa biyayya, da marasa bin Allah, da masu zunubi, da marasa tsarkaka, da masu saɓon Allah, da masu kashe iyaye maza da mata, da masu kisankai,
我們也知道法律不是為善人立的,而是為叛逆和不服從的,為不敬神和顣瀆聖的,為弒父母的,為殺人的,
10 da masu zina da kuma da maza masu kwana da maza, ko mata masu kwana da mata, da masu cinikin bayi da masu ƙarya da kuma masu shaidar ƙarya, da kuma duk wani abin da ya saɓa wa sahihiyar koyarwa,
為犯奸淫的,為行男色的,另為拐賣人口的,為說謊言的,為發虛誓的,並為其它相反建全道理的事而立的;
11 da take bisa ga bishara mai ɗaukaka ta Allah mai albarka, wadda ya danƙa mini.
這道理是按著真福的天主所托給我的光榮福音而宣講的。
12 Na gode wa Kiristi Yesu Ubangijinmu, wanda ya ba ni ƙarfi, saboda ya amince da ni, har ya sa ni aikinsa.
我感謝那賜與我能力的我們的主基督耶穌,因為衪認為我忠信,就派定了我服役。
13 Ko da yake a dā ni mai saɓo da mai tsanantawa da kuma mai rikici ne, aka nuna mini jinƙai saboda na yi haka cikin jahilci ne da kuma rashin bangaskiya.
原先我是個褻瀆者、迫害者和施暴者;但是我蒙受了憐憫,因為我當時是在不信之中,出於無認識而做了那些事。
14 An zubo mini alherin Ubangijinmu a yalwace, tare da bangaskiya da ƙaunar da take cikin Kiristi Yesu.
然而我們主的恩寵對我特別豐厚,使我在耶穌基督內有了信和愛。
15 Ga wata magana tabbatacciya wadda ta cancanci cikakkiyar karɓa. Kiristi Yesu ya zo duniya domin ceton masu zunubi, wanda nake mafi muni a cikinsu.
這話是確實的,值得完全接納;就是基督耶穌到世界上來,是為拯救罪人;而我就是其中的魁首。
16 Amma saboda wannan dalilin ne aka nuna mini jinƙai domin ta wurina, mafi zunubi duka, Kiristi Yesu yă iya bayyana matuƙar haƙurinsa a matsayin misali ga waɗanda za su gaskata shi su kuma sami rai madawwami. (aiōnios g166)
但是我所以蒙受了憐憫,是為使基督耶穌在我這個魁首身上,顯示衪的完全堅忍,為給將來信任衪而獲永生的人一個榜樣。 (aiōnios g166)
17 Bari girma da ɗaukaka su tabbata har abada abadin ga Sarki madawwami, wanda ba ya mutuwa, wanda ba a ganinsa, wanda kuma shi ne kaɗai Allah! Amin. (aiōn g165)
願尊榮和光榮歸於萬世的君王,那不死不滅,不可見的惟一天主,於無窮之世,阿們。 (aiōn g165)
18 Timoti, ɗana, na ba ka wannan umarni bisa ga annabce-annabcen da aka yi a dā game da kai, domin ta wurin binsu ka iya yin yaƙi mai kyau,
我兒弟茂德,我根據以前指著你所說過的那些預言,把這訓令委詑給你,為叫你藉此打這埸好仗,
19 kana riƙe da bangaskiya da kuma lamiri mai kyau. Gama waɗansu mutane, saboda ƙin kasa kunne ga lamirinsu, suka lalatar da bangaskiyarsu.
保持信德和良心純潔;有些人竟擯棄了良心,而在信德上遭了船破之災,
20 Cikinsu kuwa akwai Himenayus da Alekzanda, waɗanda na miƙa ga Shaiɗan don su horo su bar yin saɓo.
其中有依默納約和亞歷山大,我已把他們交給撒殫,為叫他們學習不再褻瀆。

< 1 Timoti 1 >