< 1 Timoti 6 >

1 Duk waɗanda suke ƙarƙashin bauta, ya kamata su ɗauki iyayengijinsu a kan sun cancanci girmamawa matuƙa, don kada a ɓata sunan Allah da kuma koyarwarmu.
くびきの下にある奴隷は、自分の主人を十分に尊敬すべき人だと考えなさい。それは神の御名と教えとがそしられないためです。
2 Waɗanda suke da iyayengiji masu bi, to, kada su yi musu reni domin su’yan’uwa ne. A maimako, sai ma su fi bauta musu, saboda waɗanda suke cin moriyar hidimarsu masu bi ne, ƙaunatattu ne kuma a gare su. Waɗannan su ne abubuwan da za ka koya musu ka kuma gargaɗe su.
信者である主人を持つ人は、主人が兄弟だからといって軽く見ず、むしろ、ますますよく仕えなさい。なぜなら、その良い奉仕から益を受けるのは信者であり、愛されている人だからです。あなたは、これらのことを教え、また勧めなさい。
3 In wani yana koyarwar ƙarya bai kuma yarda da sahihiyar koyarwar Ubangijinmu Yesu Kiristi da kuma koyarwa ta tsoron Allah ba,
違ったことを教え、私たちの主イエス・キリストの健全なことばと敬虔にかなう教えとに同意しない人がいるなら、
4 yana cike da girman kai bai kuma san kome ba. Yana da mugun halin son gardama da muhawwara game da kalmomin da suke kawo kishi, rikici, maganar ƙeta, da mugayen zace-zace
その人は高慢になっており、何一つ悟らず、疑いをかけたり、ことばの争いをしたりする病気にかかっているのです。そこから、ねたみ、争い、そしり、悪意の疑りが生じ、
5 da yawan tankiya tsakanin mutane masu mugun hali, waɗanda aka raba su da gaskiya, suke kuma tsammani cewa bin Allah wata hanya ce ta samun kuɗi.
また、知性が腐ってしまって真理を失った人々、すなわち敬虔を利得の手段と考えている人たちの間には、絶え間のない紛争が生じるのです。
6 Amma bin Allah da gamsuwa riba ce mai yawa.
しかし、満ち足りる心を伴う敬虔こそ、大きな利益を受ける道です。
7 Gama ba mu zo duniya da kome ba, ba kuwa za mu fita daga cikinta da kome ba.
私たちは何一つこの世に持って来なかったし、また何一つ持って出ることもできません。
8 In dai muna da abinci da sutura, ai, sai mu gamsu da su.
衣食があれば、それで満足すべきです。
9 Mutanen da suke son yin arziki sukan fāɗi cikin jarraba, su fāɗa a tarko, suna mugayen sha’awace-sha’awace iri-iri na wauta da cutarwa, irin waɗanda suke dulmuyar da mutane, su kai ga lalacewa da hallaka.
金持ちになりたがる人たちは、誘惑とわなと、また人を滅びと破滅に投げ入れる、愚かで、有害な多くの欲とに陥ります。
10 Gama son kuɗi shi ne tushen kowane irin mugun abu. Waɗansu mutane, don tsananin son kuɗi, sun bauɗe daga bangaskiya suka kuma jawo wa kansu da baƙin ciki iri-iri.
金銭を愛することが、あらゆる悪の根だからです。ある人たちは、金を追い求めたために、信仰から迷い出て、非常な苦痛をもって自分を刺し通しました。
11 Amma kai, mutumin Allah, ka guji duk wannan, ka kuma nemi adalci, tsoron Allah, bangaskiya, ƙauna, jimrewa da kuma hankali.
しかし、神の人よ。あなたは、これらのことを避け、正しさ、敬虔、信仰、愛、忍耐、柔和を熱心に求めなさい。
12 Ka yi fama, kyakkyawar fama ta bangaskiya. Ka riƙi rai madawwamin nan, wanda aka kira saboda shi, sa’ad da ka yi kyakkyawar shaida a gaban shaidu masu yawa. (aiōnios g166)
信仰の戦いを勇敢に戦い、永遠のいのちを獲得しなさい。あなたはこのために召され、また、多くの証人たちの前でりっぱな告白をしました。 (aiōnios g166)
13 Na umarce ka, a gaban Allah mai ba da rai ga kome, da kuma Kiristi Yesu wanda yayinda yake ba da shaida a gaban Buntus Bilatus ya yi kyakkyawar shaida,
私は、すべてのものにいのちを与える神と、ポンテオ・ピラトに対してすばらしい告白をもってあかしされたキリスト・イエスとの御前で、あなたに命じます。
14 ka kiyaye wannan umarni ba tare da wani aibi ko abin zargi ba har yă bayyanuwar Ubangijinmu Yesu Kiristi,
私たちの主イエス・キリストの現われの時まで、あなたは命令を守り、傷のない、非難されるところのない者でありなさい。
15 wanda Allah zai kawo a daidai lokaci, Allah, mai albarka wanda yake kaɗai Mai Mulki, Sarkin sarakuna da Ubangijin iyayengiji,
その現われを、神はご自分の良しとする時に示してくださいます。神は祝福に満ちた唯一の主権者、王の王、主の主、
16 wanda shi kaɗai ne marar mutuwa wanda kuma yake zaune cikin hasken da ba ya kusatuwa, wanda babu wanda ya taɓa gani ko zai iya gani. A gare shi girma da iko su tabbata har abada. Amin. (aiōnios g166)
ただひとり死のない方であり、近づくこともできない光の中に住まわれ、人間がだれひとり見たことのない、また見ることのできない方です。誉れと、とこしえの主権は神のものです。アーメン。 (aiōnios g166)
17 Ka umarci waɗanda suke da arziki a wannan duniya kada su ɗaga kai ko su sa begensu a kan dukiyar da ba ta da tabbaci, sai dai su sa begensu ga Allah, wanda yake ba mu kome a yalwace don jin daɗinmu. (aiōn g165)
この世で富んでいる人たちに命じなさい。高ぶらないように。また、たよりにならない富に望みを置かないように。むしろ、私たちにすべての物を豊かに与えて楽しませてくださる神に望みを置くように。 (aiōn g165)
18 Ka umarce su su yi nagarta, su wadatu cikin ayyuka nagari, su kuma zama masu bayarwa hannu sake da kuma masu niyyar yin taimako.
また、人の益を計り、良い行ないに富み、惜しまずに施し、喜んで分け与えるように。
19 Ta haka za su ajiye wa kansu dukiya a matsayin tushen mai ƙarfi don tsara mai zuwa, don su riƙi rai wanda yake na tabbatacce.
また、まことのいのちを得るために、未来に備えて良い基礎を自分自身のために築き上げるように。
20 Timoti, ka lura da abin da aka danƙa maka amana. Ka yi nesa da masu maganganun rashin tsoron Allah da kuma yawan mūsu da ake ƙarya, ake ce da shi ilimi,
テモテよ。ゆだねられたものを守りなさい。そして、俗悪なむだ話、また、まちがって「霊知」と呼ばれる反対論を避けなさい。
21 wanda waɗansu suka furta kuma ta yin haka suka bauɗe daga bangaskiya. Alheri yă kasance tare da ku.
これを公然と主張したある人たちは、信仰からはずれてしまいました。 恵みが、あなたがたとともにありますように。

< 1 Timoti 6 >