< 1 Timoti 5 >
1 Kada ka tsawata wa dattijo, sai dai ka gargaɗe shi a matsayinka. Ka ɗauki samari a matsayin’yan’uwanka,
Do not rebuke an elder man, but entreat him as a father, younger men as brothers,
2 tsofaffin mata kuwa sai ka ce uwaye,’yan mata kuma a matsayin’yan’uwa da matuƙar tsarki.
elder women as mothers, younger women as sisters, in all purity.
3 Ka girmama gwauraye waɗanda suke cikin bukata ta ainihi.
Support widows, the real widows.
4 Amma in gwauruwa tana da’ya’ya ko jikoki, to, sai su fara koyon yin ayyukan addininsu ga danginsu, ta haka za su sāka wa iyayensu da kakanninsu, gama wannan yakan gamshi Allah.
But if any widow has children or grandchildren, let them first learn to be devoted to their own house, and to give back recompense to their parents, for this is acceptable in the sight of God.
5 Gwauruwa wadda ba ta da kowa da zai taimake ta, za tă sa zuciyarta ga Allah, tana roƙo da addu’o’i dare da rana gare shi don taimako.
But the real widow, and made alone, has hoped in God, and continues in entreaties and prayers night and day.
6 Amma gwauruwar da take zaman jin daɗi, matacciya ce tun tana da rai.
But she who is self-indulgent is dead while she lives.
7 Ka umarce su game da waɗannan abubuwa, don su kasance marasa abin zargi.
And command these things, so that they may be blameless.
8 In wani bai kula da danginsa ba, musamman iyalinsa na kurkusa, ya mūsunta bangaskiya ke nan, ya kuma fi marar ba da gaskiya muni.
But if any man does not provide for his own, and especially those belonging his household, he has denied the faith, and is worse than an infidel.
9 Kada a lasafta gwauruwa cikin jerin gwauraye sai ta wuce shekara sittin, ta kuma yi zaman aminci ga mijinta,
Let no widow be enrolled under sixty years old, having become the wife of one man,
10 aka kuma santa sosai saboda ayyuka masu kyau, kamar renon’ya’ya, da karɓan baƙi, tana yi wa tsarkaka hidima, tana taimakon waɗanda suke cikin wahala tana kuma ba da kanta ga yin kowane aikin mai kyau.
being testified in good works: if she has reared children, if she has been hospitable to strangers, if she has washed the feet of the sanctified, if she has relieved those who are afflicted, if she has followed every good work.
11 Game da gwauraye masu ƙuruciya kuwa, kada ka sa su cikin wannan lissafi. Gama sa’ad da sha’awar jikinsu ta kāsa daurewa game da wa’adin da suka yi da Kiristi, sai su so yin aure.
But refuse younger widows, for when they are sexually aroused, they desire of the Christ to marry,
12 Ta haka suna jawo wa kansu hukunci, saboda sun karya alkawarinsu na farko.
which has condemnation because they have disregarded the original pledge.
13 Ban da haka, sukan koyi zaman banza, suna zirga-zirga gida-gida. Ba kawai sun zama masu zaman banza ba, har ma sun zama masu gulma da masu shisshigi, suna faɗin abubuwan da bai kamata su faɗa ba.
And also at the same time they learn to be idle, roving the houses, and not only idle, but also babbling and meddlesome, speaking things that they ought not.
14 Saboda haka ina ba wa gwauraye masu ƙuruciya shawara su yi aure, su sami’ya’ya, su lura da gidajensu kada kuwa su ba abokin gāba zarafin ɓata suna.
I desire therefore the younger women to marry, to bear children, to manage house, to give not one occasion to him who opposes on account of slander.
15 Waɗansu dai sun riga sun bauɗe sun bi Shaiɗan.
For some have already turned aside after Satan.
16 In mace mai bi tana da gwauraye a iyalinta, ya kamata tă taimake su, kada tă bar wa ikkilisiya wannan nauyi, domin ikkilisiya ta sami zarafin taimakon gwaurayen da suke da bukata ta ainihi.
If any believing man or believing woman has widows, let them relieve them, and let not the congregation be burdened, so that it may relieve the real widows.
17 Dattawan da suka bi da al’amuran ikkilisiya da kyau sun cancanci girmamawa ninki biyu, musamman waɗanda aikinsu wa’azi ne da kuma koyarwa.
Let the elders who rule well be regarded worthy of double compensation, especially those who labor in the word and in teaching.
18 Gama Nassi ya ce, “Kada ka sa wa bijimi takunkumi yayinda yake sussukar hatsi,” da kuma, “Ma’aikaci ya cancanci hakkinsa.”
For the scripture says thou shall not muzzle an ox that is threshing. And the workman is worthy of his wage.
19 Kada ka saurari ƙara game da dattijo sai da shaidu biyu ko uku.
Accept no accusation against an elder, except at two or three witnesses.
20 Amman waɗannan dattawa waɗanda suke yin zunubi kuwa sai ka kwaɓe su a gaban jama’a, don saura su ji tsoro.
Those who sin, rebuke in the sight of all, so that the others may also have fear.
21 Na gama ka da Allah, da Kiristi Yesu, da kuma zaɓaɓɓun mala’iku, ka kiyaye waɗannan abubuwa ƙwarai da gaske, kada ka nuna bambanci.
I solemnly testify before God, and the Lord Jesus Christ, and the chosen agents, that thou keep these things without prejudice, doing nothing from partiality.
22 Kada ka yi garajen ɗibiya hannuwa, kada kuma ka yi tarayya a cikin zunuban waɗansu. Ka kiyaye kanka da tsarki.
Lay hands hastily on no man, nor contribute to other sins. Keep thyself pure.
23 Ka daina shan ruwa kaɗai, yi amfani da ruwan inabi kaɗan saboda cikinka da kuma yawan rashin lafiyarka.
No longer drink water, but use a little wine because of thy stomach and thy frequent weaknesses.
24 Zunuban waɗansu mutane a fili suke, suna shan gabansu zuwa hukunci; zunuban waɗansu kuwa sukan bi su a baya.
The sins of some men are evident, leading to judgment, but also for some they follow after.
25 Haka ma ayyuka nagari a fili suke, ko ba ma a fili suke ba, ba a iya ɓoye su.
Likewise also good works are evident, and those faring otherwise cannot be hid.