< 1 Timoti 2 >
1 Da farko dai, ina gargaɗe ku cewa a yi roƙe-roƙe, ana addu’o’i, ana yin addu’a a madadin waɗansu da kuma a yi godiya saboda kowane mutum
2 da sarakuna da dukan masu mulki, domin mu zauna lafiya, rai kuma kwance, muna bin Allah sosai a cikin natsuwa.
3 Wannan yana da kyau, yakan kuma gamshi Allah Mai Cetonmu,
4 wanda yake so dukan mutane su sami ceto su kuma zo ga sanin gaskiya.
5 Gama Allah ɗaya ne, matsakanci kuma ɗaya tsakanin Allah da mutane, shi ne kuwa Kiristi Yesu,
6 wanda ya ba da kansa fansa domin dukan mutane, shaidar da aka bayar a daidai lokaci.
7 Don haka ne aka sa ni mai wa’azi, da manzo kuma, gaskiya nake faɗa, ba ƙarya ba, na kuma zama malami mai koya wa al’ummai al’amarin bangaskiya da kuma na gaskiya.
8 Ina so maza a ko’ina su ɗaga hannuwansu masu tsarki cikin addu’a, ba tare da fushi ko faɗa ba.
9 Ina kuma so mata su lura su yi wa kansu adon da ya cancanta, da rigunan da suka dace, ba da adon kitso ko sa kayan zinariya ko lu’ulu’u ko kuma tufafi masu tsada ba,
10 sai dai su yi ayyuka masu kyan da suka dace da matan da suke masu bauta wa Allah.
11 Ya kamata mace ta riƙa koyo cikin natsuwa da cikakkiyar biyayya.
12 Ban ba mace izini ta koyar ko tă yi mulki a kan namiji ba; sai dai ta zauna shiru.
13 Gama Adamu ne aka fara halitta, sa’an nan Hawwa’u.
14 Ba kuma Adamu ne aka yaudara ba; macen ce aka yaudara ta kuma zama mai zunubi.
15 Amma mata Za tă sami ceto za su sami ceto ta wurin haihuwa, in suka ci gaba cikin bangaskiya, ƙauna da kuma tsarki tare da halin sanin ya kamata.