< 1 Timoti 1 >
1 Bulus, manzon Kiristi Yesu ta wurin umarnin Allah Mai Cetonmu da kuma na Yesu Kiristi begenmu,
Paul, an apostle of Jesus Christ, according to the appointment of God our Savior, and the Lord Jesus Christ our hope,
2 Zuwa ga Timoti ɗana na gaske cikin bangaskiya. Alheri, jinƙai da kuma salama daga Allah Uba da Kiristi Yesu Ubangijinmu, su kasance tare da kai.
to Timothy, my true son in the faith; grace, mercy, peace from God our Father, and Christ Jesus our Lord.
3 Kamar yadda na gargaɗe ka sa’ad da zan je Makidoniya, ka zauna can Afisa domin ka umarci waɗansu mutane kada su koyar da ƙa’idodin ƙarya nan gaba
As, on going into Macedonia, I besought you to remain in Ephesus, that you might charge some that they teach no other thing,
4 ko su ba da kansu ga tatsuniyoyi da ƙididdigar asali marar iyaka. Waɗannan suna kawo faɗa a maimakon aikin Allah wanda yake ta wurin bangaskiya.
nor give heed to fables and endless genealogies, which produce disputes rather than godly edification, which is in faith;
5 Maƙasudin wannan umarnin dai ƙauna ce, wadda take zuwa daga zuciya mai tsabta da lamiri mai kyau da kuma sahihiyar bangaskiya.
(Now the end of the commandment is love out of a pure heart, and out of a good conscience, and out of faith unfeigned:
6 Waɗansu sun bauɗe daga waɗannan al’amura, suka koma ga maganganu marasa ma’ana.
which things some not having aimed at, have turned aside to idle disputation,
7 So suke su zama malaman doka, ba tare da fahimtar abin da suke faɗa ba, balle abubuwan da suke ta nacewa a kai.
desiring to be teachers of law, though understanding neither what they say nor of what they boldly affirm.
8 Mun san cewa doka tana da kyau in an yi amfani da ita yadda ya kamata.
But we know that the law is good, if any one use it lawfully;
9 Mun kuma san cewa an yi doka ba domin masu adalci ba sai dai masu tawaye, da marasa biyayya, da marasa bin Allah, da masu zunubi, da marasa tsarkaka, da masu saɓon Allah, da masu kashe iyaye maza da mata, da masu kisankai,
knowing this, that law is not made for a righteous man, but for the lawless and disobedient, for the ungodly and for sinners, for the unholy and for scorners, for murderers of fathers and murderers of mothers, for man-slayers,
10 da masu zina da kuma da maza masu kwana da maza, ko mata masu kwana da mata, da masu cinikin bayi da masu ƙarya da kuma masu shaidar ƙarya, da kuma duk wani abin da ya saɓa wa sahihiyar koyarwa,
for lewd persons, for sodomites, for men-stealers, for liars, for perjured persons, and for whatever other thing is opposed to sound teaching,
11 da take bisa ga bishara mai ɗaukaka ta Allah mai albarka, wadda ya danƙa mini.
according to the glorious gospel of the blessed God, which has been intrusted to me.
12 Na gode wa Kiristi Yesu Ubangijinmu, wanda ya ba ni ƙarfi, saboda ya amince da ni, har ya sa ni aikinsa.
And I thank Christ Jesus our Lord, who has given me power, because he counted me faithful, and put me into the ministry;
13 Ko da yake a dā ni mai saɓo da mai tsanantawa da kuma mai rikici ne, aka nuna mini jinƙai saboda na yi haka cikin jahilci ne da kuma rashin bangaskiya.
me, I say, who before was a reviler and a persecutor and an overbearing man. But I obtained mercy, because I did it ignorantly in unbelief:
14 An zubo mini alherin Ubangijinmu a yalwace, tare da bangaskiya da ƙaunar da take cikin Kiristi Yesu.
and the grace of our Lord was very abundant with faith, and love which is in Christ Jesus.
15 Ga wata magana tabbatacciya wadda ta cancanci cikakkiyar karɓa. Kiristi Yesu ya zo duniya domin ceton masu zunubi, wanda nake mafi muni a cikinsu.
Assuredly true and worthy of all acceptation is this saying: that Christ Jesus came into the world to save sinners, of whom I am chief.
16 Amma saboda wannan dalilin ne aka nuna mini jinƙai domin ta wurina, mafi zunubi duka, Kiristi Yesu yă iya bayyana matuƙar haƙurinsa a matsayin misali ga waɗanda za su gaskata shi su kuma sami rai madawwami. (aiōnios )
But for this reason I obtained mercy, that in me first Jesus Christ might show all long-suffering, for an example to those who might afterward believe on him in order to life eternal. (aiōnios )
17 Bari girma da ɗaukaka su tabbata har abada abadin ga Sarki madawwami, wanda ba ya mutuwa, wanda ba a ganinsa, wanda kuma shi ne kaɗai Allah! Amin. (aiōn )
Now to the King of the ages, the incorruptible, invisible, only wise God, be honor and glory from age to age. Amen.) (aiōn )
18 Timoti, ɗana, na ba ka wannan umarni bisa ga annabce-annabcen da aka yi a dā game da kai, domin ta wurin binsu ka iya yin yaƙi mai kyau,
This charge I commit to you, son Timothy, in accordance with the preceding prophecies concerning you, that by them you may war the good warfare,
19 kana riƙe da bangaskiya da kuma lamiri mai kyau. Gama waɗansu mutane, saboda ƙin kasa kunne ga lamirinsu, suka lalatar da bangaskiyarsu.
holding faith and a good conscience, which some having thrust from them, as it respects faith have made shipwreck; of whom are Hymenæus and Alexander,
20 Cikinsu kuwa akwai Himenayus da Alekzanda, waɗanda na miƙa ga Shaiɗan don su horo su bar yin saɓo.
whom I have delivered to Satan, that they may learn not to revile.