< 1 Tessalonikawa 5 >

1 To,’yan’uwa, game da lokuta da ranaku, ba ma bukata mu rubuta muku,
But concerning the times and the seasons, brothers, you have no need that anything be written to you.
2 gama kun sani sarai cewa ranar Ubangiji za tă zo kamar ɓarawo da dare.
For you yourselves know well that the day of the Lord comes like a thief in the night.
3 Yayinda mutane suke cewa, “Akwai salama da zaman lafiya,” hallaka za tă auko musu farat ɗaya, kamar yadda naƙuda take kama mace mai ciki, ba za su kuwa tsira ba.
Now when they are saying, "Peace and safety," then sudden destruction will come on them, like birth pains on a pregnant woman; and they will in no way escape.
4 Amma ku,’yan’uwa, ba kwa cikin duhu da wannan rana za tă zo muku ba zato kamar ɓarawo.
But you, brothers, are not in darkness, that the day should overtake you like a thief.
5 Dukanku’ya’yan haske ne da kuma’ya’yan rana. Mu ba mutanen dare ko na duhu ba ne.
You are all sons of light, and sons of the day. We do not belong to the night, nor to darkness,
6 Saboda haka fa, kada mu zama kamar saura, waɗanda suke barci, sai dai mu zama masu tsaro da masu kamunkai.
so then let us not sleep, as the rest do, but let us watch and be sober.
7 Gama masu barci, da dad dare suke barci, masu sha su bugu kuwa, da dad dare suke buguwa.
For those who sleep, sleep in the night, and those who are drunk are drunk in the night.
8 Amma da yake mu na rana ne, bari mu zama masu kamunkai, sanye da bangaskiya da ƙauna kamar sulke, begen cetonmu kuma kamar hular kwano.
But let us, since we belong to the day, be sober, putting on the breastplate of faith and love, and, for a helmet, the hope of salvation.
9 Gama Allah bai naɗa mu don mu sha fushi ba, sai dai mu sami ceto ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi.
For God did not appoint us to wrath, but to the obtaining of salvation through our Lord Jesus Christ,
10 Ya mutu saboda mu domin, ko muna a faɗake ko muna barci, mu kasance tare da shi.
who died for us, that, whether we wake or sleep, we should live together with him.
11 Saboda haka ku ƙarfafa juna ku kuma gina juna, kamar dai yadda kuke yi.
Therefore exhort one another, and build each other up, even as you also do.
12 To, muna roƙonku,’yan’uwa, ku girmama waɗanda suke aiki sosai a cikinku, waɗanda suke bisanku cikin Ubangiji da kuma waɗanda suke yin muku gargaɗi.
But we ask you, brothers, to recognize those who labor among you, and are over you in the Lord, and admonish you,
13 Ku riƙe su da mutunci sosai cikin ƙauna saboda aikinsu. Ku yi zaman lafiya da juna.
and to respect and honor them in love for their work's sake. Be at peace among yourselves.
14 Muna kuma gargaɗe ku,’yan’uwa, ku gargaɗe waɗanda suke zaman banza, ku ƙarfafa masu raunanar zuciya, ku taimaki marasa ƙarfi, ku yi haƙuri da kowa.
We exhort you, brothers, admonish the disorderly, encourage the fainthearted, support the weak, be patient toward all.
15 Ku tabbata cewa kada kowa yă rama mugunta da mugunta, sai dai kullum ku yi ƙoƙarin yin wa juna alheri da kuma dukan mutane.
See that no one returns evil for evil to anyone, but always seek what is good both for each other and for all.
16 Ku riƙa farin ciki kullum;
Rejoice always.
17 ku ci gaba da yin addu’a;
Pray without ceasing.
18 ku yi godiya cikin kowane hali, gama wannan shi ne nufin Allah dominku cikin Kiristi Yesu.
In everything give thanks, for this is the will of God in Christ Jesus toward you.
19 Kada ku danne aikin Ruhu.
Do not quench the Spirit.
20 Kada ku rena annabci,
Do not treat prophecies with contempt,
21 amma ku gwada kome, ku riƙe abin da yake mai kyau,
but test all things; hold firmly that which is good.
22 ku ƙi kowace mugunta.
Abstain from every form of evil.
23 Bari Allah da kansa, Allah na salama, yă tsarkake ku sarai. Bari dukan ruhunku, ranku, da kuma jikinku su zama marar aibi a dawowar Ubangijinmu Yesu Kiristi.
May the God of peace himself sanctify you completely. May your whole spirit, soul, and body be preserved blameless at the coming of our Lord Jesus Christ.
24 Wannan wanda ya kira ku mai aminci ne zai kuwa aikata.
He who calls you is faithful, who will also do it.
25 ’Yan’uwa, ku yi mana addu’a.
Brothers, pray for us also.
26 Ku gaggai da dukan’yan’uwa da sumba mai tsarki.
Greet all the brothers with a holy kiss.
27 Na gama ku da Ubangiji ku sa a karanta wannan wasiƙa ga dukan’yan’uwa.
I solemnly command you by the Lord that this letter be read to all the holy brothers.
28 Alherin Ubangijinmu Yesu Kiristi yă kasance tare da ku.
The grace of our Lord Jesus Christ be with you.

< 1 Tessalonikawa 5 >