< 1 Tessalonikawa 4 >

1 A ƙarshe,’yan’uwa, mun umarce ku yadda za ku yi rayuwa domin ku gamshi Allah, kamar yadda kuke yi. Yanzu muna roƙonku muna kuma gargaɗe ku a cikin Ubangiji Yesu ku yi haka sau da sau.
As to what remains, then, brethren, we beseech and exhort you by the Lord Jesus, that as you have received from us, how you ought to walk, and please God, you would more abound in it.
2 Gama kun san umarnan da muka ba ku ta wurin ikon Ubangiji Yesu.
For you know what commandments we gave you by the Lord Jesus;
3 Nufin Allah ne a tsarkake ku, cewa ku guje wa fasikanci;
for this is the will of God, even your sanctification, that you should abstain from whoredom--
4 don kowannenku yă koya yadda zai ƙame kansa a hanyar da take mai tsarki, mai mutunci kuma,
that every one of you should know how to possess his own body in sanctification and honor--
5 ba cikin muguwar sha’awa kamar ta marasa bangaskiya, waɗanda ba su san Allah ba;
not in the passion of lust, even as the Gentiles who know not God.
6 cikin wannan al’amari kuwa kada wani yă yi wa ɗan’uwansa laifi ko yă cuce shi. Ubangiji zai hukunta mutane saboda dukan irin waɗannan zunubai, kamar yadda muka riga muka gaya muku, muka kuma yi muku gargaɗi.
That no man should go beyond bounds, or defraud his brother in this matter, because the Lord is an avenger of all such;
7 Gama Allah bai kira mu ga zaman marasa tsarki ba, sai dai ga zaman tsarki.
for God has not called us to impurity, but to holiness.
8 Saboda haka, duk wanda ya ƙi wannan umarni ba mutum ne ya ƙi ba sai ko Allah, wanda ya ba ku Ruhunsa Mai Tsarki.
Therefore, indeed, he who despises not man, but God, who certainly has given to us his Holy Spirit.
9 Yanzu kuwa game da ƙaunar’yan’uwa, ba ma bukata mu rubuta muku, gama ku kanku Allah ya riga ya koya muku ku ƙaunaci juna.
But, concerning brotherly love, you have no need that I write to you, for you yourselves are taught of God to love one another.
10 Gaskiyar kuwa ita ce, kuna ƙaunar dukan’yan’uwa ko’ina a Makidoniya. Duk da haka muna ƙara gargaɗe ku,’yan’uwa, ku yi haka sau da sau.
And, indeed, you do it toward all the brethren who are in all Macedonia: but we exhort you, brethren, still to abound,
11 Ku mai da wannan burinku na yi natsattsiyar rayuwa, kuna mai da hankali ga sha’anin da yake gabanku, kuna kuma yin aiki da hannuwanku, kamar dai yadda muka gaya muku,
and earnestly study to be quiet; and to mind your own affairs, and to work with your own hands, as we commanded you:
12 don rayuwanku ta kullum ta zama da mutunci ga waɗanda suke na waje don kuma kada ku dogara a kan kowa.
that you may walk decently toward them who are without, and may have need of nothing.
13 ’Yan’uwa, ba ma so ku kasance cikin jahilci game da waɗanda suka yi barci, ko kuwa ku yi baƙin ciki kamar sauran mutanen da ba su da bege.
Now, I would not have you ignorant, brethren, concerning them who sleep; that you may not be grieved, even as the others, who have no hope.
14 Mun gaskata cewa Yesu ya mutu ya tashi kuma daga matattu, ta haka muka gaskata cewa Allah zai kawo waɗanda suka yi barci a cikinsa tare da Yesu.
For if we believe that Jesus died and rose again; so, also, them who sleep, will God, through Jesus, bring with him.
15 Bisa ga maganar Ubangiji kansa, muna gaya muku cewa mu da muke raye har yanzu, waɗanda aka bari har dawowar Ubangiji, tabbatacce ba za mu riga waɗanda suka yi barci tashi ba.
Besides, this we affirm to you, by the word of the Lord, that we, the living, who remain at the coming of the Lord, shall not anticipate them who are asleep:
16 Gama Ubangiji kansa zai sauko daga sama, da umarni mai ƙarfi, da muryar babban mala’ika da kuma busar ƙahon Allah, waɗanda suka mutu kuwa cikin Kiristi za su tashi da farko.
for the Lord himself will descend from heaven, with a shout, with the voice of the Arch Angel, and with the trumpet of God. And the dead in Christ shall rise first;
17 Bayan haka, mu da muke da rai da aka bari, za a ɗauke mu tare da su a cikin gizagizai don mu sadu da Ubangiji a sararin sama. Ta haka za mu kasance tare da Ubangiji har abada.
afterward we, the living, who remain, shall, at the same time with them, be instantly taken up in clouds, to join the Lord in the air; and so we shall be for ever with the Lord.
18 Saboda haka ku ƙarfafa juna da waɗannan kalmomi.
Wherefore, comfort one another with these words.

< 1 Tessalonikawa 4 >