< 1 Tessalonikawa 3 >
1 Saboda haka da muka kāsa daurewa, sai muka ga ya fi kyau a bar mu a Atens mu kaɗai.
Když se mi po vás v Aténách stýskalo, rozhodl jsem se poslat Timotea, toho milého bratra a Božího spoluslužebníka. Měl vás navštívit a povzbudit vaši víru,
2 Muka aiki Timoti, wanda yake ɗan’uwanmu da kuma abokin aikin Allah a cikin yaɗa bisharar Kiristi, don yă gina ku yă kuma ƙarfafa ku cikin bangaskiyarku,
3 don kada kowa yă raunana ta wurin waɗannan gwaje-gwajen. Kun sani sarai cewa an ƙaddara mu don waɗannan.
abyste v pronásledování nezakolísali.
4 Gaskiyar ita ce, sa’ad da muke tare da ku, mun sha gaya muku cewa za a tsananta mana. Haka kuwa ya faru, kamar dai yadda kuka sani.
Trpět patří ke křesťanskému údělu; to jsme vám přece říkali už od začátku, a tak nebuďte překvapeni, když k tomu opravdu dochází.
5 Saboda wannan, sa’ad da ban iya jimrewa ba, sai na aika domin in sami labarin bangaskiyarku, da fata kada yă zama mai jarraban nan ya riga ya jarrabce ku, ƙoƙarinmu kuma yă zama banza.
Proto jsem tehdy poslal Timotea k vám, abych se tu nemusel trápit úzkostí, jestli vás protivník přece jen nedostal na svou návnadu a nepřivedl všechnu naši práci vniveč.
6 Amma ga shi yanzu Timoti ya dawo mana daga wurinku ya kuma kawo labari mai daɗi game da bangaskiyarku da kuma ƙaunarku. Ya faɗa mana yadda kullum kuke da tunani mai kyau a kanmu, yadda kuke marmari ku gan mu, kamar dai yadda mu ma muke marmari mu gan ku.
Teď se však právě Timoteus vrátil s dobrými zprávami, že jste ve víře ani v lásce nepolevili, že na nás stále myslíte a toužíte po novém setkání stejně jako my.
7 Saboda haka’yan’uwa, cikin dukan damuwarmu da tsananinmu an ƙarfafa mu game da ku saboda bangaskiyarku.
A tak nás při všech těch trampotách tady potěšily zprávy o vaší věrnosti Pánu. Vydržíme všechno, jen když víme, že s vaší vírou je vše v pořádku.
8 Gama yanzu tabbatacce muna da rai, da yake kuna nan tsaye daram a cikin Ubangiji.
9 Wace irin godiya ce za mu yi wa Allah saboda ku a kan dukan farin cikin da muke da shi a gaban Allahnmu ta dalilinku?
Jak se Bohu odvděčit za všechnu tu radost, jakou z vás máme?
10 Dare da rana muna addu’a da himma domin mu sāke ganinku, mu kuma ba ku abin da kuka rasa a bangaskiyarku.
Dnem i nocí vroucně prosíme, abychom vás mohli znovu spatřit a podle potřeby upevnit vaši víru.
11 Yanzu bari Allahnmu da Ubanmu kansa da kuma Ubangijinmu Yesu yă shirya mana hanya mu zo wurinku.
Přejeme si, aby nám Bůh, náš Otec, a Ježíš, náš Pán, připravili cestu k vám!
12 Ubangiji yă sa ƙaunarku ta ƙaru ta kuma yalwata ga juna da kuma ga kowa, kamar yadda tamu take muku.
Ať dá bohatě růst vaší lásce navzájem i navenek, stejně jako naší lásce k vám.
13 Bari yă ƙarfafa zukatanku har ku zama marasa aibi da kuma tsarkaka a gaban Allahnmu da Ubanmu sa’ad da Ubangijimmu Yesu ya dawo tare da dukan tsarkakansa.
Ať vás vnitřně posílí, abyste se mohli bezúhonní a dokonalí postavit před Boha, našeho Otce, až se náš Pán, Ježíš Kristus, vrátí se všemi svými.