< 1 Tessalonikawa 2 >

1 Kun sani,’yan’uwa, cewa ziyararmu a gare ku ba tă zama a banza ba.
Domin ku da kanku kun sani, 'yan'uwa, cewa zuwan mu gareku, ba a banza yake ba.
2 Mun riga mun sha wahala, aka kuma zage mu a Filibbi, kamar yadda kuka sani, amma da taimakon Allahnmu muka yi ƙarfin hali muka sanar muku bishararsa duk da matsananciyar gāba.
Kun kuma san yadda aka wulakantar damu, aka kuma kunyatar damu a Filibi, kamar yadda kuka sani. Muna nan kuwa da karfin zuciya cikin Allahnmu domin yi maku bisharar Allah cikin fama da yawa.
3 Gama roƙon da muke yi bai fito daga kuskure ko munafunci ba, ba kuwa ƙoƙari muke yi mu yaudare ku ba.
Domin kuwa gargadinmu zuwa a gare ku ba gurbatacciya bace, ko cikin rashin tsarki, ba kuma ta yaudara bace.
4 A maimako haka, muna magana ne kamar mutanen da Allah ya amince yă danƙa musu amanar wannan bishara. Ba ma ƙoƙari mu gamshi mutane sai dai Allah, mai auna zukatanmu.
A maimako, kamar yadda Allah ya amince damu, ya kuma damka mana amanar bishararsa, haka kuma muke yin magana. Muna maganar ba domin mu gamshi mutane ba, amma domin mu gamshi Allah. Domin shi ne yake gwada zuciyarmu.
5 Kun san ba ma taɓa yin daɗin baki ko mu yi ƙoƙarin kasance da halin kwaɗayin da muke ɓoyewa, Allah shi ne shaidarmu.
Domin bamu taba yi maku dadin baki ba, ko sau daya, kamar yadda kuka sani, ko kwadayi a asirce, kamar yadda Allah shine shaidar mu.
6 Ba ma neman yabo daga wurin mutane, ko a gare ku, ko ga waɗansu. A matsayinmu na manzannin Kiristi da mun so, da mun nawaita muku,
Bamu kuma nemi daukaka daga mutane ko daga gare ku ko kuma wadansu ba. Da mun so da mun mori ikonmu a matsayin manzannin Almasihu.
7 amma muka kasance masu sauƙinkai a cikinku, kamar yadda mahaifiya take lura da ƙananan’ya’yanta.
A maimakon haka, mun kaskantar da kanmu a tsakanin ku kamar yadda uwa take ta'azantar da 'ya'yan ta.
8 Muka ƙaunace ku ƙwarai har muka ji daɗin bayyana muku, ba bisharar Allah kaɗai ba amma har rayukanmu ma, domin kun zama ƙaunatattu a gare mu.
Don haka muna da kauna domin ku, ba bisharar Allahnmu kadai muke jin dadin yi maku ba, amma harda bada rayukan mu domin ku. Domin kun zama kaunatattu ne a garemu,
9 Ba shakka kuna iya tunawa,’yan’uwa, famarmu da kuma wahalarmu; mun yi aiki dare da rana don kada mu zama nauyi wa wani yayinda muke muku wa’azin bisharar Allah.
Kufa tuna, 'yan'uwa, game da aikinmu da famarmu. Dare da rana muna aiki sosai domin kada mu nawaita wa kowane dayan ku. A lokacin da muke yi maku bisharar Allah.
10 Ku shaidu ne, haka ma Allah, na yadda muka yi zaman tsarki, adalci da kuma marar aibi a cikinku, ku da kuka ba da gaskiya.
Ku shaidu ne, haka ma Allah, yadda muka yi rayuwar tsarki da kuma adalci da rashin abin zargi a wajenku wadanda kuka bada gaskiya.
11 Gama kun san cewa mun bi da kowannenku yadda mahaifi yakan yi da’ya’yansa,
Don haka kun kuma sani yadda muka rika yi da kowannenku, kamar uba da 'ya'yansa, yadda muka yi ma ku garadi da kuma karfafa ku, mun kuma shaida.
12 muna ƙarfafa ku, muna ta’azantar da ku, muna kuma gargaɗe ku ku yi rayuwar da za tă cancanci Allah, wanda ya kira ku zuwa mulkinsa da kuma ɗaukakarsa.
Domin ku yi tafiya a hanyar da ta dace ga Allah, wanda ya kira ku zuwa ga mulkinsa da kuma daukakarsa.
13 Muna kuma gode wa Allah ba fasawa domin, sa’ad da kuka karɓi maganar Allah, wadda kuka ji daga gare mu, kun karɓe ta ba kamar maganar mutane ba, sai dai kamar yadda take, maganar Allah wadda take aiki a cikinku ku da kuka ba da gaskiya.
Domin wannan dalili ne yasa muke yi wa Allah godiya a koyaushe. Domin a lokacin da kuka karbi maganar Allah daga wurinmu wadda kuka ji, kun karbeta da gaske ba kamar maganar mutum ba. A maimako, kuka karbeta da gaskiyarta, kamar yadda take, maganar Allah. Wannan kalma kuma ita ce ke aiki a cikin ku wadanda kuka yi bangaskiya.
14 Gama ku,’yan’uwa, kun zama masu koyi da ikkilisiyoyin Allah a Yahudiya waɗanda suke cikin Kiristi Yesu. Kun sha wahala a hannun mutanen ƙasarku kamar yadda ikkilisiyoyin nan ma suka sha a hannun Yahudawa,
Domin ku 'yan'uwa, kun zama masu koyi da ikilisiyoyin Allah da ke Yahudiya cikin Almasihu Yesu. Domim kuma kun sha wahala irin tamu daga wurin mutanen kasarku kamar yadda suma suka sha a hannun Yahadawa.
15 waɗanda suka kashe Ubangiji Yesu da annabawa suka kuma kore mu. Ba sa yin aikin da Allah yake so, masu gāba ne kuwa da dukan mutane
Yahudawane suka kashe Ubangiji Yesu da sauran Annabawa, kuma Yahudawane suka koro mu, Basu gamshi Allah ba. A maimako, suna hamayya da dukkan mutane.
16 suna ƙoƙarin hana mu yin magana ga Al’ummai don kada su sami ceto. Ta haka kullum suke ƙara tara tsibin zunubansu. Fushin Allah ya aukar musu a ƙarshe.
Sun kuma haramta mana yin magana da Al'ummai domin su sami ceto. Sakamakon haka kuwa kullum suna cika zunubansu. Fushi kuma ya afko kansu daga karshe.
17 Amma,’yan’uwa, sa’ad da aka raba mu da ku na ɗan lokaci (a jiki, ba a tunani ba), daga cikin marmarinmu mai tsanani mun yi duk abin da muke iya yi mu gan ku.
Mu kuma, 'yan'uwa, mun rabu daku na karamin lokaci, a zahiri, ba a zuciya ba, mun kuma yi iyakar kokarinmu da marmarin ganin fuskarku.
18 Gama mun so mu zo wurinku, tabbatacce ni, Bulus, na yi ƙoƙari sau da sau, amma Shaiɗan ya hana mu.
Domin mun yi maramarin zuwa gareku. Ni, Bulus, ba sau daya ba, amma Shaidan ya hanamu.
19 Gama mene ne begenmu, farin cikinmu, ko kuma rawanin da zai zama mana abin ɗaukaka a gaban Ubangijinmu Yesu sa’ad da ya dawo? Ba ku ba ne?
To menene begenmu a gaba, ko murnarmu ko rawanin alfahari, a gaban Ubangijinmu Yesu a ranar zuwansa? Ko ba ku bane, da kuma sauran jama'a?
20 Tabbatacce, ku ne ɗaukakarmu da kuma farin cikinmu.
Don kuwa kune daukakarmu da kuma farin cikinmu.

< 1 Tessalonikawa 2 >