< 1 Sama’ila 1 >
1 Akwai wani mutum daga Ramatayim, mutumin Zuf daga ƙasar tuddan Efraim, sunansa Elkana, ɗan Yeroham, shi jikan Elihu ɗan Tohu, tattaɓa kunnen Zuf, mutumin Efraim.
2 Yana da mata biyu, ɗaya sunanta Hannatu, ɗayan kuwa ana kiranta Feninna. Ita Feninna tana da’ya’ya, amma Hannatu ba ta da’ya’ya.
3 Shekara-shekara wannan mutum yakan haura daga garinsa zuwa Shilo domin yin sujada da miƙa hadayu ga Ubangiji Maɗaukaki. A can kuwa’ya’yan Eli maza biyu, Hofni da Finehas su ne firistoci na Ubangiji.
4 Duk sa’ad da rana ta kewayo don Elkana yă miƙa hadaya, yakan ba da kashin nama ga matarsa Feninna da dukan’ya’yanta maza da mata.
5 Amma Hannatu kuwa sai yă ba ta babban rabo gama yana ƙaunarta ko da yake Ubangiji ya kulle mahaifarta.
6 Saboda Ubangiji ya kulle mahaifarta, sai kishiyarta ta dinga tsokanarta don tă ba ta haushi.
7 Wannan ya ci gaba shekara da shekaru. Duk lokacin da Hannatu ta haura zuwa haikalin Ubangiji, sai kishiyarta tă tsokane ta har tă yi ta kuka tă kuma ƙi cin abinci.
8 Elkana mijinta kuwa yakan ce mata, “Hannatu don me kike kuka? Me ya sa ba za ki ci abinci ba? Don me kika karaya? Ashe, ban fi’ya’ya goma a gare ki ba?”
9 Wata rana sa’ad da suka gama ci da sha a Shilo, Hannatu ta miƙe tsaye. Eli firist kuwa yana zaune a kujera a bakin ƙofar haikalin Ubangiji.
10 A cikin baƙin ciki, Hannatu ta yi kuka mai zafi ta yi addu’a ga Ubangiji.
11 Ta yi ta cewa, “Ya Ubangiji Maɗaukaki. In har ka dubi baƙin cikin baiwarka, ka tuna da ni, ba ka kuma manta da baiwarka ba, amma ka ba ta ɗa, ni ma zan miƙa shi ga Ubangiji dukan rayuwarsa, aska kuwa ba za tă taɓa kansa ba.”
12 Yayinda take addu’a ga Ubangiji, Eli ya lura da bakinta.
13 Hannatu tana addu’a a zuci, ba a jin muryarta, sai leɓunanta ne kawai suna motsi. Eli kuwa ya yi tsammani ta bugu ne.
14 Sai ya ce mata, “Har yaushe za ki ci gaba da maye? Ki daina shan ruwan inabi.”
15 Hannatu ta ce, “Ba haka ba ne, ranka yă daɗe, ni mace ce da take cikin matsala ƙwarai da gaske. Ban sha ruwan inabi ba, ko wani abu mai sa maye, ina dai faɗa wa Ubangiji abin da yake damuna ne.
16 Kada ka yi zato baiwarka’yar iska ce. Ina addu’a a nan saboda yawan azaba da baƙin cikin da nake ciki.”
17 Eli ya ce, “In haka ne, to, ki sauka lafiya, Allah na Isra’ila kuma yă ba ki abin da kika roƙa daga gare shi.”
18 Ta ce, bari baiwarka tă sami tagomashi a idonka. Sai ta yi tafiyarta ta je ta ci wani abu, fuskarta kuwa ba tă ƙara kasance da baƙin ciki ba.
19 Kashegari da sassafe suka tashi suka yi sujada a gaban Ubangiji, sai suka koma garinsu a Rama. Elkana kuwa ya kwana da matarsa Hannatu, Ubangiji kuma ya tuna da ita.
20 Ana nan sai Hannatu ta yi ciki, ta kuma haifi ɗa. Ta ba shi suna Sama’ila; tana cewa, “Domin na roƙe shi daga wurin Ubangiji.”
21 Da shekara ta kewayo, sai Elkana da iyalinsa suka sāke tafi Shilo domin su yi hadaya ga Ubangiji, yă kuma cika alkawarin da ya yi.
22 Hannatu kuwa ba tă bi su ba. Ta gaya wa mijinta cewa, “Sai bayan na yaye yaron, zan kai shi in miƙa shi a gaban Ubangiji, yă kuma kasance a wurin koyaushe.”
23 Elkana mijinta ya ce mata, “Ki yi abin da kika ga ya fi miki kyau. Ki jira har sai bayan kin yaye shi. Ubangiji dai ya cika maganarsa.” Saboda haka matar ta tsaya a gida, ta yi ta renon ɗanta har ta yaye shi.
24 Bayan ta yaye shi, sai ta ɗauki yaron tare da bijimi bana uku, da mudun gari, da salkan ruwan inabi, ta kawo su a gidan Ubangiji a Shilo.
25 Bayan an yanka bijimin, sai suka kawo yaron wurin Eli.
26 Sai ta ce masa, “Ranka yă daɗe, ba ka gane ni ba? Ai, ni ce matar da ta taɓa tsayawa a gabanka, tana addu’a ga Ubangiji.
27 Wannan yaron ne na roƙa daga wurin Ubangiji, ya kuwa ba ni abin da na roƙa daga gare shi.
28 Saboda haka, na ba da shi ga Ubangiji muddin ransa, zai zama na Ubangiji.” A can kuwa ya yi wa Ubangiji sujada.