< 1 Sama’ila 8 >

1 Da Sama’ila ya tsufa, sai ya naɗa’ya’yansa maza su zama alƙalan Isra’ila.
ויהי כאשר זקן שמואל וישם את בניו שפטים לישראל
2 Sunan ɗansa na fari Yowel, na biyu kuwa Abiya. Suka yi alƙalanci a Beyersheba.
ויהי שם בנו הבכור יואל ושם משנהו אביה--שפטים בבאר שבע
3 Amma’ya’yansa ba su bi hanyar mahaifinsu ba. Suka mai da hankalinsu ga neman kuɗi da cin hanci, suna kuma danne gaskiya.
ולא הלכו בניו בדרכו ויטו אחרי הבצע ויקחו שחד--ויטו משפט
4 Sai dukan shugabannin Isra’ila suka taru suka zo wurin Sama’ila a Rama.
ויתקבצו כל זקני ישראל ויבאו אל שמואל הרמתה
5 Suka ce masa, “Ka tsufa,’ya’yanka kuma ba sa bin hanyarka, saboda haka sai ka naɗa sarkin da zai bi da mu kamar yadda sauran ƙasashe suke da su.”
ויאמרו אליו הנה אתה זקנת ובניך לא הלכו בדרכיך עתה שימה לנו מלך לשפטנו--ככל הגוים
6 Amma Sama’ila bai ji daɗi sa’ad da suka ce, “Ka ba mu sarki da zai bi da mu.” Sai ya yi addu’a ga Ubangiji.
וירע הדבר בעיני שמואל כאשר אמרו תנה לנו מלך לשפטנו ויתפלל שמואל אל יהוה
7 Ubangiji kuwa ya ce masa, “Ka saurari dukan maganganun da mutanen suke gaya maka. Ai, ba kai ba ne suka ƙi, ni ne suka ƙi in zama sarkinsu.
ויאמר יהוה אל שמואל שמע בקול העם לכל אשר יאמרו אליך כי לא אתך מאסו כי אתי מאסו ממלך עליהם
8 Haka suka yi daga tun daga ranar da na fitar da su daga Masar har zuwa yau, suka ƙi ni, suka bauta wa waɗansu alloli, haka ma suke yi maka.
ככל המעשים אשר עשו מיום העלתי אותם ממצרים ועד היום הזה ויעזבני ויעבדו אלהים אחרים--כן המה עשים גם לך
9 Yanzu ka saurare su amma ka yi musu kashedi sosai, ka sa su san abin da sarkin da zai bi da su zai yi.”
ועתה שמע בקולם אך כי העד תעיד בהם והגדת להם משפט המלך אשר ימלך עליהם
10 Sama’ila kuwa ya ce wa mutanen da suke roƙo yă naɗa musu sarki dukan abin da Ubangiji ya faɗa.
ויאמר שמואל את כל דברי יהוה אל העם השאלים מאתו מלך
11 Ya ce musu, “Ga abin da sarkin da zai yi mulkinku zai yi. Zai kwashe’ya’yanku yă sa su yi aiki da kekunan yaƙi da dawakansa, waɗansu za su riƙa gudu a gaban keken yaƙinsa.
ויאמר--זה יהיה משפט המלך אשר ימלך עליכם את בניכם יקח ושם לו במרכבתו ובפרשיו ורצו לפני מרכבתו
12 Zai sa waɗansu su zama shugabannin mutum dubu-dubu da kuma na hamsin-hamsin. Waɗansu za su yi masa noma da girbi. Waɗansu za su ƙera masa makaman yaƙi da kayayyaki don keken yaƙinsa.
ולשום לו שרי אלפים ושרי חמשים ולחרש חרישו ולקצר קצירו ולעשות כלי מלחמתו וכלי רכבו
13 Zai sa’ya’yanku mata yin aikin turare da dafe-dafe da kuma toye-toye.
ואת בנותיכם יקח לרקחות ולטבחות ולאפות
14 Zai karɓi gonakinku mafi kyau da gonakin inabinku da gonakin zaitunku yă ba wa ma’aikatansa.
ואת שדותיכם ואת כרמיכם וזיתיכם הטובים--יקח ונתן לעבדיו
15 Zai kuma karɓi zakan hatsinku da na inabinku yă ba shugabannin fadarsa da sauran masu hidimarsa.
וזרעיכם וכרמיכם יעשר ונתן לסריסיו ולעבדיו
16 Zai ƙwace bayinku maza da mata, da shanunku, da jakunanku mafi kyau domin su yi masa aiki.
ואת עבדיכם ואת שפחותיכם ואת בחוריכם הטובים ואת חמוריכם--יקח ועשה למלאכתו
17 Zai karɓi zakan dabbobinku, ku kanku za ku zama bayinsa.
צאנכם יעשר ואתם תהיו לו לעבדים
18 Sa’ad da ranar ta zo, za ku yi kuka ku nemi a fishe ku daga sarkin da kuka zaɓa, Ubangiji kuwa ba zai ji ku ba.”
וזעקתם ביום ההוא מלפני מלככם אשר בחרתם לכם ולא יענה יהוה אתכם ביום ההוא
19 Amma mutanen suka ƙi jin Sama’ila, sai suka ce, “A’a, mu dai, muna son sarki yă bi da mu.”
וימאנו העם לשמע בקול שמואל ויאמרו לא כי אם מלך יהיה עלינו
20 Ta haka za mu zama kamar sauran ƙasashe, mu kasance da sarkin da zai bi da mu, yă tafi tare da mu zuwa yaƙe-yaƙe.
והיינו גם אנחנו ככל הגוים ושפטנו מלכנו ויצא לפנינו ונלחם את מלחמתנו
21 Da Sama’ila ya ji duk maganganun da mutanen suka faɗa, sai ya mayar wa Ubangiji.
וישמע שמואל את כל דברי העם וידברם באזני יהוה
22 Ubangiji kuwa ya ce, “Ka saurare su, ka naɗa masu sarki.” Sa’an nan Sama’ila ya ce wa mutanen Isra’ila, “Kowa yă koma garinsa.”
ויאמר יהוה אל שמואל שמע בקולם והמלכת להם מלך ויאמר שמואל אל אנשי ישראל לכו איש לעירו

< 1 Sama’ila 8 >