< 1 Sama’ila 7 >

1 Mutanen Kiriyat Yeyarim suka ɗauki akwatin alkawarin Ubangiji. Suka kai a gidan Abinadab da ke kan tudu, suka keɓe Eleyazar ɗansa yă lura da akwatin alkawarin Ubangiji.
The men of Kiriath Jearim came and took up the ark of Jehovah and brought it into the house of Abinadab, which was on the hill, and sanctified Eleazar his son to keep the ark of Jehovah.
2 Akwatin Alkawarin ya daɗe a Kiriyat Yeyarim ya kai shekara ashirin cif. Sai dukan mutanen Isra’ila suka yi makoki suka nemi Ubangiji.
It happened, from the day that the ark stayed in Kiriath Jearim, that the time was long; for it was twenty years: and all the house of Israel lamented after Jehovah.
3 Saboda haka Sama’ila ya yi magana da dukan gidan Isra’ila ya ce, in har da zuciya ɗaya kuke juyowa ga Ubangiji sai ku raba kanku da baƙin alloli da gunkin nan Ashtarot, ku ba da kanku ga Ubangiji. Ku yi masa bauta shi kaɗai, zai kuɓutar da ku daga hannun Filistiyawa.
Samuel spoke to all the house of Israel, saying, "If you do return to Jehovah with all your heart, then put away the foreign gods and the Ashtaroth from among you, and direct your hearts to Jehovah, and serve him only; and he will deliver you out of the hand of the Philistines."
4 Sai Isra’ilawa suka rabu da gumakan Ba’al da Ashtarot suka bauta wa Ubangiji kaɗai.
Then the children of Israel removed the Baals and the Ashtaroth, and served Jehovah only.
5 Sama’ila ya ce, “Ku tattara dukan Isra’ila a Mizfa, ni kuwa zan yi addu’a ga Ubangiji dominku.”
Samuel said, "Gather all Israel to Mizpah, and I will pray for you to Jehovah."
6 Sa’ad da suka taru a Mizfa, suka kawo ruwa suka zuba a gaban Ubangiji. A wannan rana suka yi azumi suka tuba, suka ce, “Mun yi wa Ubangiji zunubi!” Sama’ila kuwa ya zauna a Mizfa ya yi mulkin Isra’ilawa.
They gathered together to Mizpah, and drew water, and poured it out before Jehovah, and fasted on that day, and said, "We have sinned against Jehovah." Samuel judged the children of Israel in Mizpah.
7 Da Filistiyawa suka ji cewa Isra’ila sun taru a Mizfa, sai shugabanninsu suka zo don su yaƙe Isra’ila. Da Isra’ilawa suka ji labarin, sai suka tsorata saboda Filistiyawa.
When the Philistines heard that the children of Israel were gathered together at Mizpah, the lords of the Philistines went up against Israel. When the children of Israel heard it, they were afraid of the Philistines.
8 Suka ce wa Sama’ila, “Kada ka fasa kai kukanmu ga Ubangiji Allahnmu saboda mu, don yă cece mu daga hannun Filistiyawa.”
The children of Israel said to Samuel, "Do not cease to cry to Jehovah your God for us, that he will save us out of the hand of the Philistines."
9 Sama’ila ya kama ɗan rago ya miƙa shi ɗungum hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji. Ya yi roƙo ga Ubangiji a madadin Isra’ila, Ubangiji kuwa ya amsa addu’arsa.
Samuel took a suckling lamb, and offered it for a whole burnt offering to Jehovah: and Samuel cried to Jehovah for Israel; and Jehovah answered him.
10 Lokacin da Sama’ila yana miƙa hadaya ta ƙonawa, Filistiyawa suka matso kusa don su yi yaƙi da Isra’ila. A ranar Ubangiji ya sa babban tsawa ya ruɗar da Filistiyawa har suka gudu a gaban Isra’ilawa.
As Samuel was offering up the burnt offering, the Philistines drew near to battle against Israel; but Jehovah thundered with a great thunder on that day on the Philistines, and confused them; and they were struck down before Israel.
11 Isra’ilawa suka fito a guje daga Mizfa suka fafari Filistiyawa suka yi ta karkashe su a hanya har kwarin Bet-Kar.
The men of Israel went out of Mizpah, and pursued the Philistines, and struck them, as far as below Beth Kar.
12 Sa’an nan Sama’ila ya ɗauki dutse ya kafa tsakanin Mizfa da Shen, ya sa masa suna, Ebenezer ma’ana, “Har zuwa wannan lokaci Ubangiji ya taimake mu.”
Then Samuel took a stone, and set it between Mizpah and Jashan, and called its name Ebenezer, saying, "Jehovah helped us until now."
13 Ta haka Isra’ilawa suka ci Filistiyawa. Daga ranan Filistiyawa ba su ƙara yin nasara a kan Isra’ila ba. Ubangiji ya yi gāba da Filistiyawa har ƙarshen zamanin Sama’ila.
So the Philistines were subdued, and they came no more within the territory of Israel. The hand of Jehovah was against the Philistines all the days of Samuel.
14 Filistiyawa suka mayar wa Isra’ila da garuruwan da suka ƙwato, wato, daga Ekron zuwa Gat, dukan yankin ƙasarsu da yake ƙarƙashin ikon Filistiyawa. Aka kuma sami zaman lafiya tsakanin Isra’ilawa da Amoriyawa.
The cities which the Philistines had taken from Israel were restored to Israel, from Ekron even to Gath; and Israel recovered its territory out of the hand of the Philistines. There was peace between Israel and the Amorites.
15 Sama’ila kuwa ya ci gaba da mulkin Isra’ila dukan rayuwarsa.
Samuel judged Israel all the days of his life.
16 Shekara-shekara Sama’ila yakan fita rangadi zuwa Betel, da Gilgal da Mizfa inda yakan yi musu shari’a.
He went from year to year in circuit to Bethel and Gilgal, and Mizpah; and he judged Israel in all those places.
17 Amma yakan komo Rama inda gidansa yake, a nan yakan yi wa Isra’ila shari’a. A nan ne kuma ya gina wa Ubangiji bagade.
His return was to Ramah, for there was his house; and there he judged Israel: and he built there an altar to Jehovah.

< 1 Sama’ila 7 >