< 1 Sama’ila 6 >

1 Lokacin da akwatin alkawarin Ubangiji ya kai wata bakwai a ƙasar Filistiyawa.
The LORD’s ark was in the country of the Philistines seven months.
2 Filistiyawa suka kira firistoci da bokaye suka ce, “Me za mu yi da akwatin alkawarin Ubangiji? Ku gaya mana yadda za mu komar da shi inda ya fito.”
The Philistines called for the priests and the diviners, saying, “What shall we do with the LORD’s ark? Show us how we should send it to its place.”
3 Suka ce, in za ku komar da akwatin alkawarin Allah na Isra’ila kada ku komar da shi hannu wofi; amma ku tabbata kun aika da hadaya don laifi zuwa wurinsa. Sa’an nan za ku warke ku kuma san dalilin da ya sa bai cire hannunsa a kanku ba.
They said, “If you send away the ark of the God of Israel, don’t send it empty; but by all means return a trespass offering to him. Then you will be healed, and it will be known to you why his hand is not removed from you.”
4 Filistiyawa suka ce, “Wace irin hadaya don laifi za mu aika masa?” Suka ce, “Marurai biyar na zinariya da ɓeraye biyar na zinariya bisa ga yawan sarakunan Filistiyawa. Saboda annoba iri ɗaya ce ta buga ku da shugabanninku.
Then they said, “What should the trespass offering be which we shall return to him?” They said, “Five golden tumours and five golden mice, for the number of the lords of the Philistines; for one plague was on you all, and on your lords.
5 Ku yi siffofin marurai da na ɓeraye da suke hallaka gari, ku ba da girma ga Allah na Isra’ila. Wataƙila zai ɗauke hukuncinsa daga gare ku da allolinku da kuma ƙasarku.
Therefore you shall make images of your tumours and images of your mice that mar the land; and you shall give glory to the God of Israel. Perhaps he will release his hand from you, from your gods, and from your land.
6 Me ya sa kun taurare kanku kamar yadda Masarawa da Fir’auna suka yi? Da ya ba su matsanancin wahala, ba su bar Isra’ilawa suka tafi hanyarsu ba?
Why then do you harden your hearts as the Egyptians and Pharaoh hardened their hearts? When he had worked wonderfully amongst them, didn’t they let the people go, and they departed?
7 “Yanzu fa ku shirya sabon keken shanu da shanu biyu masu ba wa’ya’yansu nono, waɗanda ba a taɓa sa musu karkiya ba. Ku daure keken shanu wa shanun, amma ku tsare’yan maruƙansu a gida.
“Now therefore take and prepare yourselves a new cart and two milk cows on which there has come no yoke; and tie the cows to the cart, and bring their calves home from them;
8 Ku ɗauki wani akwati ku sa siffofin zinariyan nan a ciki, waɗanda za su zama kyautai na shafen laifi, ku ajiye kusa da Akwati na UBANGIJI. Bayan haka sai ku sa keken shanun da akwatin a hanya, ku bar shi yă tafi.
and take the LORD’s ark and lay it on the cart. Put the jewels of gold, which you return him for a trespass offering, in a box by its side; and send it away, that it may go.
9 Amma ku zuba ido ku ga in ya haura zuwa yankinsa, zuwa Bet-Shemesh, to, Ubangiji ne ya kawo mana babban masifar a kanmu. Amma in bai bi ta nan ba, za mu san cewa ba shi ne ya buge mu ba, tsautsayi ne kawai.”
Behold, if it goes up by the way of its own border to Beth Shemesh, then he has done us this great evil; but if not, then we shall know that it is not his hand that struck us. It was a chance that happened to us.”
10 Suka yi haka. Suka ɗauki shanun tatsa guda biyu suka ɗaura musu keken shanu, suka tsare’yan maruƙansu a gida.
The men did so, and took two milk cows and tied them to the cart, and shut up their calves at home.
11 Suka aza akwatin alkawarin Ubangiji a bisa keken shanun tare da akwatin siffofin ɓerayen zinariya da siffofin maruran.
They put the LORD’s ark on the cart, and the box with the golden mice and the images of their tumours.
12 Sai shanun suka miƙe zuwa Bet-Shemesh. Suka bi hanya daidai, ba su juya dama ko hagu ba. Shugabannin Filistiyawa suka bi har zuwa iyakar ƙasar Bet-Shemesh.
The cows took the straight way by the way to Beth Shemesh. They went along the highway, lowing as they went, and didn’t turn away to the right hand or to the left; and the lords of the Philistines went after them to the border of Beth Shemesh.
13 A lokacin kuwa mutanen Bet-Shemesh suna girbin alkamansu a kwari da suka ɗaga ido suka hangi akwatin alkawarin Ubangiji, sai suka yi farin ciki ganinsa.
The people of Beth Shemesh were reaping their wheat harvest in the valley; and they lifted up their eyes and saw the ark, and rejoiced to see it.
14 Keken shanun ya zo filin Yoshuwa a Bet-Shemesh ya tsaya a gefen wani babban dutse. Mutanen suka faskare keken shanun suka miƙa shanun hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji.
The cart came into the field of Joshua of Beth Shemesh, and stood there, where there was a great stone. Then they split the wood of the cart and offered up the cows for a burnt offering to the LORD.
15 Lawiyawa suka saukar da akwatin alkawarin Ubangiji tare da babban akwati mai siffofin zinariya na ɓeraye da marurai suka ajiye su a kan ƙaton dutse. A wannan rana mutanen Bet-Shemesh suka miƙa hadaya ta ƙonawa da waɗansu hadayu ga Ubangiji.
The Levites took down the LORD’s ark and the box that was with it, in which the jewels of gold were, and put them on the great stone; and the men of Beth Shemesh offered burnt offerings and sacrificed sacrifices the same day to the LORD.
16 Shugabanni biyar na Filistiyawan nan suka ga duk abin da ya faru, suka koma zuwa Ekron a ranar.
When the five lords of the Philistines had seen it, they returned to Ekron the same day.
17 Waɗannan su ne siffofi marurai na zinariya waɗanda Filistiyawa suka aika domin miƙa hadaya don laifi ga Ubangiji, ɗaya domin Ashdod, ɗaya domin Gaza, ɗaya domin Ashkelon, ɗaya domin Gat, ɗaya kuma domin Ekron.
These are the golden tumours which the Philistines returned for a trespass offering to the LORD: for Ashdod one, for Gaza one, for Ashkelon one, for Gath one, for Ekron one;
18 Filistiyawa kuma suka aika da siffofin ɓeraye biyar na zinariya. Yawan ɓerayen sun yi daidai da yawan garuruwan sarakunan nan biyar na Filistiyawa. Garuruwan sun ƙunshi waɗanda aka gina katangar birni kewaye da su, da kuma ƙauyukansu. Babban dutsen da suka ajiye akwatin alkawarin Ubangiji, ya zama shaida har wa yau a filin Yoshuwa a Bet-Shemesh.
and the golden mice, according to the number of all the cities of the Philistines belonging to the five lords, both of fortified cities and of country villages, even to the great stone on which they set down the LORD’s ark. That stone remains to this day in the field of Joshua of Beth Shemesh.
19 Amma Allah ya kashe waɗansu mutum saba’in na mutanen Bet-Shemesh domin sun leƙa cikin akwatin alkawarin Ubangiji. Mutane kuwa suka yi makoki domin Ubangiji ya hallaka mutane da yawa.
He struck of the men of Beth Shemesh, because they had looked into the LORD’s ark, he struck fifty thousand and seventy of the men. Then the people mourned, because the LORD had struck the people with a great slaughter.
20 Mutanen Bet-Shemesh suka yi tambaya suka ce, wa zai iya tsaya a gaban Ubangiji Allah Mai Tsarki? Wurin wa akwatin alkawari zai je daga nan?
The men of Beth Shemesh said, “Who is able to stand before the LORD, this holy God? To whom shall he go up from us?”
21 Sai suka aiki manzanni zuwa Kiriyat Yeyarim suka ce, “Filistiyawa sun komo da akwatin alkawarin Ubangiji, ku zo ku ɗauka ku kai wajenku.”
They sent messengers to the inhabitants of Kiriath Jearim, saying, “The Philistines have brought back the LORD’s ark. Come down and bring it up to yourselves.”

< 1 Sama’ila 6 >