< 1 Sama’ila 5 >
1 Bayan Filistiyawa sun ƙwace akwatin alkawarin Allah, sai suka ɗauke shi daga Ebenezer suka kai shi Ashdod.
非利士人將上帝的約櫃從以便以謝抬到亞實突。
2 Sa’an nan suka ɗauki akwatin alkawarin suka kai shi cikin haikalin gunkinsu Dagon, suka ajiye kusa da Dagon.
非利士人將上帝的約櫃抬進大袞廟,放在大袞的旁邊。
3 Kashegari da safe da mutanen Ashdod suka farka sai ga Dagon ya fāɗi a gaban akwatin alkawarin Ubangiji. Sai suka ɗauki Dagon suka ajiye a wurin zamansa.
次日清早,亞實突人起來,見大袞仆倒在耶和華的約櫃前,臉伏於地,就把大袞仍立在原處。
4 Amma kashegari kuma da safe suka farka sai ga Dagon ya fāɗi a ƙasa a gaban akwatin alkawarin Ubangiji! Kansa ya fashe, hannuwansa kuma sun kakkarye sun zube a madogarar ƙofa; jikinsa ne kaɗai ya rage.
又次日清早起來,見大袞仆倒在耶和華的約櫃前,臉伏於地,並且大袞的頭和兩手都在門檻上折斷,只剩下大袞的殘體。(
5 Saboda haka firistocin Dagon da waɗanda suke sujada a haikalin Dagon ba sa taka bakin ƙofar Dagon a Ashdod har wa yau.
因此,大袞的祭司和一切進亞實突、大袞廟的人都不踏大袞廟的門檻,直到今日。)
6 Hannun Ubangiji kuwa ya yi nauyi a bisa Ashdod da kewayenta. Ya kawo hallaka ga dukansu, ya kuma buga su da marurai.
耶和華的手重重加在亞實突人身上,敗壞他們,使他們生痔瘡。亞實突和亞實突的四境都是如此。
7 Da mutanen Ashdod suka ga abin da yake faruwa, sai suka ce, “Lalle Akwatin Alkawarin Allah na Isra’ila ba zai kasance da mu ba, domin hannunsa yana da nauyi a kanmu da bisan Dagon allahnmu.”
亞實突人見這光景,就說:「以色列上帝的約櫃不可留在我們這裏,因為他的手重重加在我們和我們神大袞的身上」;
8 Saboda haka suka kira duka shugabannin Filistiyawa suka tambaye su, suka ce, “Me za mu da akwatin alkawarin Allahn Isra’ila?” Sai suka amsa suka ce, “A ɗauki akwatin alkawarin Allah na Isra’ila a kai shi Gat.” Sai suka ɗauki akwatin alkawarin Allah na Isra’ila.
就打發人去請非利士的眾首領來聚集,問他們說:「我們向以色列上帝的約櫃應當怎樣行呢?」他們回答說:「可以將以色列上帝的約櫃運到迦特去。」於是將以色列上帝的約櫃運到那裏去。
9 Amma bayan sun kai shi can, sai hannun Ubangiji ya yi gāba da birnin, aka jefa shi cikin wani mawuyacin hali. Ya buga mutanen birnin da marurai, babba da yaro.
運到之後,耶和華的手攻擊那城,使那城的人大大驚慌,無論大小都生痔瘡。
10 Sai suka aika da akwatin alkawarin Allah zuwa Ekron. Yayinda akwatin alkawarin Allah yana shiga cikin Ekron, mutanen Ekron suka yi ihu, suka ce, “An kawo mana akwatin alkawarin Allah na Isra’ila domin yă kashe mu da mutanenmu.”
他們就把上帝的約櫃送到以革倫。上帝的約櫃到了,以革倫人就喊嚷起來說:「他們將以色列上帝的約櫃運到我們這裏,要害我們和我們的眾民!」
11 Saboda haka suka kira ga dukan shugabannin Filistiyawa suka ce, “Ku komar da akwatin alkawarin Allah na Isra’ila inda ya fito; in ba haka ba zai kashe mu da mutanenmu.” Gama mutuwa ta cika garin da tsoro. Hannun Allah ya yi nauyi a kansa.
於是打發人去請非利士的眾首領來,說:「願你們將以色列上帝的約櫃送回原處,免得害了我們和我們的眾民!」原來上帝的手重重攻擊那城,城中的人有因驚慌而死的;
12 Waɗanda ba su mutu ba kuwa, sun kamu da marurai. Kukan birnin kuwa ta hau har zuwa sama.
未曾死的人都生了痔瘡。合城呼號,聲音上達於天。