< 1 Sama’ila 31 >

1 Filistiyawa suka yi yaƙi da Isra’ilawa, sai Isra’ilawa suka gudu a gaban Filistiyawa, aka kuma karkashe da yawa a dutsen Gilbowa.
Filistejci su zavojštili na Izraelce, a Izraelci su pobjegli pred njima i padali pobijeni po gori Gilboi.
2 Filistiyawa suka abka wa Shawulu da’ya’yansa maza, suka kashe’ya’yan Shawulu. Yonatan da Abinadab da Malki-Shuwa.
Filistejci stisnuše Šaula i njegove sinove i pogubiše Šaulove sinove Jonatana, Abinadaba i Malki-Šuu.
3 Yaƙin ya yi zafi ƙwarai kewaye da Shawulu, har maharba suka ji masa ciwo sosai bayan sun sha ƙarfinsa.
Boj je postao žešći oko Šaula. Iznenadiše ga strijelci s lukovima i on pade teško ranjen od strijelaca.
4 Sai Shawulu ya ce wa mai ɗauka masa makami, “Ka zare takobinka ka soke ni, kada waɗannan marasa kaciya su zo su ci mini mutunci, su kashe ni.” Amma mai ɗaukan makaman bai yarda ba don ya ji tsoro sosai. Sai Shawulu ya zāre takobinsa ya soki kansa.
Šaul tada reče svome štitonoši: “Izvuci svoj mač i probodi me da ne dođu ti neobrezanici i ne narugaju mi se.” Ali se njegov štitonoša prestravi i ne htjede toga učiniti. Zato Šaul uze mač i baci se na nj.
5 Da mai ɗaukar makamai ya ga Shawulu ya mutu, sai shi ma ya zāre takobinsa ya soki kansa ya mutu.
Kad je štitonoša vidio da je Šaul umro, baci se i on na svoj mač i umrije s njim.
6 Shawulu da yaransa uku da mai ɗaukar makamansa da dukan mutanensa suka mutu a rana ɗaya.
Tako onoga dana pogiboše zajedno Šaul, njegova tri sina, njegov štitonoša i svi njegovi ljudi.
7 Sa’ad da Isra’ilawa na bakin kwari da waɗanda suke hayin Urdun suka ga sojojin Isra’ila suna gudu, Shawulu da yaransa uku kuma duk sun mutu, sai suka bar mallakansu suka sheƙa da gudu. Filistiyawa kuwa suka zo suka mamaye wuraren.
Kad Izraelci koji bijahu na drugoj strani doline i na drugoj strani Jordana vidješe da su sinovi Izraelovi pobjegli i da je poginuo Šaul sa sinovima, ostaviše svoje gradove te se razbježaše. Filistejci dođoše i nastaniše se u njima.
8 Kashegari, da Filistiyawa suka zo domin su washe kayan matattun, sai suka tarar Shawulu da’ya’yansa uku duk sun mutu, a dutsen Gilbowa.
Kad su sutradan došli Filistejci da oplijene pobijeđene, nađoše Šaula i njegova tri sina gdje leže na gori Gilboi.
9 Suka sare kansa suka tuɓe makamansa, suka aika manzanni a dukan ƙasar Filistiyawa, su ba da labarin a haikalin allolinsu da cikin mutanensu.
Oni mu odsjekoše glavu i skidoše s njega oružje, koje poslaše po svoj filistejskoj zemlji naokolo, javljajući veselu vijest svojim idolima i narodu.
10 Suka ajiye makaman Shawulu a cikin haikalin gumakan Ashtarot. Suka kafa gawarsa a kan katanga Bet-Shan.
Potom oružje metnuše u Aštartin hram, a Šaulovo mrtvo tijelo pribiše na zid grada Bet Šana.
11 Sa’ad da mutanen Yabesh Gileyad suka sami labarin abin da Filistiyawa suka yi wa Shawulu.
Ali kad oni u Jabešu Gileadskom čuše što su Filistejci učinili od Šaula,
12 Sai dukan jarumawansu suka tashi cikin dare suka tafi Bet-Shan suka saukar da gawar Shawulu da na’ya’yansa daga kan katangan Bet-Shan suka tafi Yabesh inda suka ƙone su.
ustadoše svi hrabri ljudi i, pošto su hodili svu noć, uzeše Šaulovo mrtvo tijelo i tjelesa njegovih sinova sa zida grada Bet Šana pa ih donesoše u Jabeš i ondje spališe.
13 Sai suka kwashi ƙasusuwansu suka binne a gindin itace tsamiya a Yabesh, suka kuma yi azumi kwana bakwai.
Potom uzeše njihove kosti i ukopaše ih pod tamarisom u Jabešu i postiše sedam dana.

< 1 Sama’ila 31 >