< 1 Sama’ila 3 >

1 Yaron nan Sama’ila ya yi hidima a gaban Ubangiji a ƙarƙashin Eli. A waɗannan kwanaki kuwa jin magana daga wurin Ubangiji ba safai ba, babu kuma wahayi da yawa.
L'enfant Samuel fait le service de Yahvé devant Eli. La parole de Yahvé était rare en ce temps-là. Il n'y avait pas beaucoup de visions, alors.
2 Wata rana da dare Eli da idanunsa sun kusa makancewa har ba ya iya gani sosai yana kwance a inda ya saba.
En ce temps-là, comme Éli était couché à sa place (ses yeux avaient commencé à s'affaiblir, de sorte qu'il ne voyait plus),
3 Fitilar Allah kuwa tana ci, ba tă mutu ba tukuna, Sama’ila kuma na kwance a haikali na Ubangiji inda akwai akwatin Allah.
et que la lampe de Dieu ne s'était pas encore éteinte, et que Samuel s'était couché dans le temple de Yahvé, là où se trouvait l'arche de Dieu,
4 Sai Ubangiji ya kira Sama’ila. Sama’ila ya amsa ya ce, “Ga ni.”
Yahvé appela Samuel. Il dit: « Me voici. »
5 Sai ya ruga wajen Eli ya ce, “Ga ni, gama ka kira ni.” Eli ya ce, “Ɗana ban kira ba, je ka kwanta”. Saboda haka ya tafi ya kwanta.
Il courut vers Eli et dit: « Me voici, car tu m'as appelé. » Il a dit: « Je n'ai pas appelé. Allonge-toi à nouveau. » Il alla se coucher.
6 Ubangiji ya sāke kiransa ya ce, “Sama’ila!” Sama’ila ya tashi kuma ya je wurin Eli ya ce, “Ga ni, gama ka kira ni.” Amma Eli ya ce, “Ban kira ka ba, ɗana koma ka kwanta.”
Yahvé appela de nouveau: « Samuel! » Samuel se leva, alla vers Eli et dit: « Me voici, car tu m'as appelé. » Il a répondu: « Je n'ai pas appelé, mon fils. Recouche-toi. »
7 Sama’ila dai bai riga ya san Ubangiji ba tukuna. Ba a kuma taɓa bayyana maganar Ubangiji a gare shi ba tukuna ba.
Or Samuel ne connaissait pas encore Yahvé, et la parole de Yahvé ne lui avait pas encore été révélée.
8 Ubangiji ya kira Sama’ila sau na uku, Sama’ila kuma ya tashi ya tafi wurin Eli, “Ga ni, gama ka kira ni.” Sai Eli ya gane cewa Ubangiji ne ke kira yaron.
Yahvé appela Samuel pour la troisième fois. Il se leva, alla vers Eli et dit: « Me voici, car tu m'as appelé. » Eli comprit que Yahvé avait appelé l'enfant.
9 Saboda haka, Eli ya gaya wa Sama’ila cewa, “Je ka kwanta, in kuma ya kira ka, ka ce masa, ‘Ya Ubangiji ka yi magana gama bawanka yana saurara.’” Sama’ila ya koma ya kwanta a wurin kwanciyarsa.
Alors Éli dit à Samuel: « Va te coucher. S'il t'appelle, tu diras: « Parle, Yahvé, car ton serviteur entend. » Samuel alla donc se coucher à sa place.
10 Ubangiji kuma ya zo ya tsaya a wurin, yana kira ya ce, “Sama’ila, Sama’ila!” Kamar yadda ya kira a lokutan baya. Sai Sama’ila ya ce, “Yi magana gama bawanka yana saurara.”
Yahvé vint, se tint debout et appela comme les autres fois: « Samuel! Samuel! » Alors Samuel dit: « Parle, car ton serviteur entend. »
11 Ubangiji ya ce wa Sama’ila, “Duba ina dab da yin wani abu a Isra’ila da zai sa kunne kowa da yake ji, yă ji tsoro.
Yahvé dit à Samuel: « Voici, je vais faire en Israël une chose à laquelle les deux oreilles de tous ceux qui l'entendront vibreront.
12 A ranar zan cika dukan maganar da na yi game da Eli da iyalinsa, daga farko har ƙarshe.
En ce jour-là, j'accomplirai contre Eli tout ce que j'ai dit au sujet de sa maison, depuis le début jusqu'à la fin.
13 Gama na gaya masa zan hukunta gidansa har abada saboda zunubin da yake sane da shi;’ya’yansa sun wulaƙantar da kansu, shi kuma bai tsawata musu ba.
Car je lui ai dit que je jugerai sa maison pour toujours, à cause de l'iniquité qu'il a connue, parce que ses fils ont attiré la malédiction sur eux, et qu'il ne les a pas retenus.
14 Saboda haka na rantse a kan gidan Eli, ‘Ba za a taɓa shafe laifin gidan Eli da hadaya ko baiko ba.’”
C'est pourquoi j'ai juré à la maison d'Eli que l'iniquité de la maison d'Eli ne sera pas effacée à jamais par un sacrifice ou une offrande. »
15 Sama’ila kuwa ya kwanta har safe, sa’an nan ya buɗe ƙofofin gidan Ubangiji. Ya ji tsoro yă gaya wa Eli wahayin,
Samuel resta couché jusqu'au matin, puis il ouvrit les portes de la maison de Yahvé. Samuel avait peur de montrer la vision à Eli.
16 amma Eli ya kira shi ya ce, “Sama’ila, ɗana.” Sama’ila ya ce, “Ga ni.”
Alors Eli appela Samuel et dit: « Samuel, mon fils! » Il a dit: « Je suis là. »
17 Eli ya ce, mene ne ya ce maka? Kada ka ɓoye mini. Allah ya yi da kai har ma fiye in ka ɓoye mini kome da ya ce maka.
Il dit: « Quelle est la chose qu'il t'a dite? Ne me la cachez pas, je vous prie. Que Dieu te fasse ainsi, et plus encore, si tu me caches quoi que ce soit de tout ce qu'il t'a dit. »
18 Don haka sai Sama’ila ya gaya masa kome bai ɓoye masa kome ba. Sa’an nan Eli ya ce, “Shi ne Ubangiji bari yă yi abin da ya yi kyau a gare shi.”
Samuel lui raconta tout, et ne lui cacha rien. Il a dit: « C'est Yahvé. Qu'il fasse ce qui lui semble bon. »
19 Ubangiji kuwa yana tare da Sama’ila har girmansa bai kuma bar ko ɗaya daga maganarsa ta kāsa cika ba.
Samuel grandissait, et l'Éternel était avec lui; il ne laissait tomber à terre aucune de ses paroles.
20 Dukan Isra’ila daga Dan har Beyersheba suka shaida amincin Sama’ila annabi ne na Ubangiji.
Tout Israël, depuis Dan jusqu'à Beersheba, savait que Samuel avait été établi comme prophète de Yahvé.
21 Ubangiji kuwa ya dinga bayyana a Shilo, a nan ya bayyana kansa ga Sama’ila ta wurin maganarsa.
Yahvé apparut de nouveau à Silo, car Yahvé s'était révélé à Samuel à Silo par la parole de Yahvé.

< 1 Sama’ila 3 >