< 1 Sama’ila 29 >

1 Filistiyawa suka tattara dukan rundunoninsu a Afek. Isra’ila kuwa suka yi sansani kusa da maɓulɓular da take Yezireyel.
Now all the troops of the Philistines were gathered together to Aphec: and Israel also camped by the fountain which is in Jezrahel.
2 Sa’ad da sarakuna Filistiyawa suke wucewa da rundunarsu na mutum ɗari-ɗari da na dubu-dubu. Dawuda da mutanensa suna biye a baya tare da Akish.
And the lords of the Philistines marched with their hundreds and their thousands: but David and his men were in the rear with Achis.
3 Komandodin Filistiyawa suka ce, “Waɗannan Ibraniyawa kuma fa?” Akish ya ce, “Wannan shi ne Dawuda hafsan Shawulu, sarkin Isra’ila. Yana nan tare da ni shekara guda ke nan. Ban kuwa taɓa samunsa da wani lahani ba tun daga ranar da ya bar Shawulu.”
And the princes of the Philistines said to Achis: What mean these Hebrews? And Achis said to the princes of the Philistines: Do you not know David, who was the servant of Saul the king of Israel, and hath been with me many days, or years, and I have found no fault in him, since the day that he fled over to me until this day?
4 Amma komandodin Filistiyawa suka yi fushi, suka ce, “Ka sa mutumin nan yă koma zuwa wurin da ka ba shi yă zauna. Ba zai bi mu zuwa wurin yaƙi ba. Yana iya juya a kanmu lokacin yaƙin. Zai iya yin amfani da wannan zarafi yă ciccire kawunanmu don yă faranta wa maigidansa rai?
But the princes of the Philistines were angry with him, and they said to him: Let this man return, and abide in his place, which thou hast appointed him, and let him not go down with us to battle, lest he be an adversary to us, when we shall begin to fight: for how can he otherwise appease his master, but with our heads?
5 Tuna fa, ba shi ne Dawuda ɗin da ake girmama da rawa da waƙoƙi ana cewa, “‘Shawulu ya kashe dubbai, Dawuda kuwa dubbun dubbai ba’?”
Is not this David, to whom they sung in their dances, saying: Saul slew his thousands, and David his ten thousands?
6 Saboda haka Akish ya kira Dawuda ya ce masa, “Muddin Ubangiji yana a raye, na amince da kai tun daga ranar da ka zo wurina har yă zuwa yau, ban same ka da wani laifi ba, na kuma yi farin ciki in sa ka a cikin sojojina don ka yi mini aiki. Amma masu mulki nawa ba su yarda da kai ba.
Then Achis called David, and said to him: As the Lord liveth, thou art upright and good in my sight: and so is thy going out, and thy coming in with me in the army: and I have not found my evil in thee, since the day that thou camest to me unto this day: but thou pleasest not the lords.
7 Sai ka juya ka koma ka isa lafiya ba tare da ɓata wa masu mulkin Filistiyawa rai ba.”
Return therefore, and go in peace, and offend not the eyes of the princes of the Philistines.
8 Dawuda ya ce wa Akish, “Me na yi? Ka taɓa samun bawanka da laifi tun daga ranar da na zo har zuwa yanzu? Ina dalilin da ba zan tafi tare da kai in yaƙi maƙiyin ranka yă daɗe, sarki ba?”
And David said to Achis: But what have I done, and what hast thou found in me thy servant, from the day that I have been in thy sight until this day, that I may not go and fight against the enemies of my lord the king?
9 Akish ya ce, “A ganina kai marar laifi ne kamar mala’ikan Allah, duk da haka shugabannin sojojin Filistiyawa sun ce, ‘Ba zai tafi yaƙi tare da mu ba.’
And Achis answering said to David: I know that thou art good in my sight, as an angel of God: but the princes of the Philistines have said: He shall not go up with us to the battle.
10 Ka tashi da sassafe, kai da bayin shugabanka da suka zo tare da kai. Da gari ya waye sai ku kama hanya.”
Therefore arise in the morning, thou, and the servants of thy lord, who came with thee: and when you are up before day, and it shall begin to be light, go on your way.
11 Gari na wayewa tun da sassafe Dawuda da mutanensa suka tashi suka kama hanyar komawa ƙasar Filistiyawa. Filistiyawa kuwa suka haura zuwa Yezireyel.
So David and his men arose in the night, that they might set forward in the morning, and returned to the land of the Philistines: and the Philistines went up to Jezrahel.

< 1 Sama’ila 29 >