< 1 Sama’ila 15 >

1 Sama’ila ya ce wa Shawulu, “Ni ne wanda Ubangiji ya aika in shafe ka ka zama sarki bisa mutanensa Isra’ila. Saurara yanzu ka ji saƙo daga wurin Ubangiji.
Samuel said to Saul, “The LORD sent me to anoint you to be king over his people, over Israel. Now therefore listen to the voice of the LORD’s words.
2 Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Zan hori Amalekawa saboda abin da suka yi wa Isra’ila sa’ad da suka ba su wahala yayinda suka fito daga Masar.
The LORD of Armies says, ‘I remember what Amalek did to Israel, how he set himself against him on the way when he came up out of Egypt.
3 Yanzu ka tafi ka yaƙi Amalekawa, ka hallaka kome da yake nasu, kada ka bar su da rai, ka kashe maza, da mata, da yara, da jarirai, da dabbobi, da tumaki, da raƙuma, da kuma jakuna.’”
Now go and strike Amalek, and utterly destroy all that they have, and don’t spare them; but kill both man and woman, infant and nursing baby, ox and sheep, camel and donkey.’”
4 Sai Shawulu ya tattara sojoji, ya ƙidaya su a Telayim, ya sami su dubu ɗari biyu da dubu goma daga Yahuda.
Saul summoned the people, and counted them in Telaim, two hundred thousand footmen and ten thousand men of Judah.
5 Shawulu ya tafi birnin Amalek ya yi kwanto a kwari.
Saul came to the city of Amalek, and set an ambush in the valley.
6 Sai Shawulu ya ce wa Keniyawa, “Ku tashi ku bar Amalekawa don kada in hallaka ku tare da su, saboda kun yi wa dukan Isra’ilawa kirki, lokacin da suka fito daga Masar.” Saboda haka Keniyawa suka tashi suka bar Amalekawa.
Saul said to the Kenites, “Go, depart, go down from amongst the Amalekites, lest I destroy you with them; for you showed kindness to all the children of Israel when they came up out of Egypt.” So the Kenites departed from amongst the Amalekites.
7 Sa’an nan Shawulu ya ci Amalekawa da yaƙi tun daga Hawila har zuwa Shur, a gabashin iyakar Masar.
Saul struck the Amalekites, from Havilah as you go to Shur, which is before Egypt.
8 Ya kama Agag sarkin Amalekawa da rai. Ya kuma hallaka dukan mutanensa da takobi.
He took Agag the king of the Amalekites alive, and utterly destroyed all the people with the edge of the sword.
9 Amma Shawulu da sojojinsa suka bar Agag, da tumaki, da shanu, da’yan maruƙa masu ƙiba da kuma duk abin da yake mai kyau da rai. Waɗannan ba su so su hallaka su gaba ɗaya ba, amma duk abin da ba a so da kuma marar amfani suka hallaka.
But Saul and the people spared Agag and the best of the sheep, of the cattle, of the fat calves, of the lambs, and all that was good, and were not willing to utterly destroy them; but everything that was vile and refuse, that they destroyed utterly.
10 Sai Ubangiji ya yi magana da Sama’ila ya ce,
Then the LORD’s word came to Samuel, saying,
11 “Na damu da na naɗa Shawulu sarki, domin ya juya mini baya, bai kuma bi umarnina ba.” Sama’ila ya damu ƙwarai, ya yi kuka ga Ubangiji dukan dare.
“It grieves me that I have set up Saul to be king, for he has turned back from following me, and has not performed my commandments.” Samuel was angry; and he cried to the LORD all night.
12 Kashegari da sassafe sai Sama’ila ya tashi ya tafi domin yă sadu da Shawulu, amma aka gaya masa cewa Shawulu ya tafi Karmel. A can ya yi wa kansa abin tunawa don yă girmama kansa, daga can kuma ya juya ya gangara zuwa Gilgal.
Samuel rose early to meet Saul in the morning; and Samuel was told, saying, “Saul came to Carmel, and behold, he set up a monument for himself, turned, passed on, and went down to Gilgal.”
13 Da Sama’ila ya kai wurinsa, sai Shawulu ya ce, “Ubangiji yă albarkace ka, na aikata umarnin Ubangiji.”
Samuel came to Saul; and Saul said to him, “You are blessed by the LORD! I have performed the commandment of the LORD.”
14 Amma Sama’ila ya ce, “Ashe, waɗannan ba kukan tumaki ke nan nake ji a kunnena ba? Wane kuka shanu ke nan nake ji?”
Samuel said, “Then what does this bleating of the sheep in my ears and the lowing of the cattle which I hear mean?”
15 Shawulu ya amsa ya ce, “Sojoji ne suka kawo su daga Amalekawa. Sun bar tumaki da shanu masu kyau da rai don su yi wa Ubangiji Allahnka hadaya, amma sauran mun hallaka duka.”
Saul said, “They have brought them from the Amalekites; for the people spared the best of the sheep and of the cattle, to sacrifice to the LORD your God. We have utterly destroyed the rest.”
16 Sama’ila ya ce, “Dakata, bari in faɗa maka abin da Ubangiji ya ce mini jiya da dare.” Shawulu ya ce, “Gaya mini.”
Then Samuel said to Saul, “Stay, and I will tell you what the LORD said to me last night.” He said to him, “Say on.”
17 Sama’ila ya ce, “Ko da yake kana ganin kanka kai ba wani abu ne ba, ashe, ba kai ne yanzu shugaban kabilan Isra’ila ba? Ubangiji ya shafe ka ka zama sarkin Isra’ila.
Samuel said, “Though you were little in your own sight, weren’t you made the head of the tribes of Israel? The LORD anointed you king over Israel;
18 Shi kuma ya aika, ya umarce ka cewa, ‘Tafi ka hallaka Amalekawa mugayen mutanen nan duka, ka yaƙe su sai ka share su ƙaf.’
and the LORD sent you on a journey, and said, ‘Go, and utterly destroy the sinners the Amalekites, and fight against them until they are consumed.’
19 Me ya sa ba ka bi umarnin Ubangiji ba? Me ya sa ka sa hannu a ganima, ka kuma yi mugun abu a gaban Ubangiji?”
Why then didn’t you obey the LORD’s voice, but took the plunder, and did that which was evil in the LORD’s sight?”
20 Shawulu ya ce, “Amma na bi umarnin Ubangiji. Na bi saƙon da Ubangiji ya ba ni. Na hallaka Amalekawa, na kuma kamo Agag sarkinsu.
Saul said to Samuel, “But I have obeyed the LORD’s voice, and have gone the way which the LORD sent me, and have brought Agag the king of Amalek, and have utterly destroyed the Amalekites.
21 Sojoji suka kawo tumaki da shanu mafi kyau daga cikin ganimar domin a miƙa hadaya ga Ubangiji Allahnka a Gilgal.”
But the people took of the plunder, sheep and cattle, the best of the devoted things, to sacrifice to the LORD your God in Gilgal.”
22 Amma Sama’ila ya ce, “Ubangiji yana murna da sadaka da hadaya fiye da biyayya ga maganar Ubangiji? Yin biyayya ta fi hadaya a kula kuma ta fi ƙibabbun raguna.
Samuel said, “Has the LORD as great delight in burnt offerings and sacrifices, as in obeying the LORD’s voice? Behold, to obey is better than sacrifice, and to listen than the fat of rams.
23 Gama tawaye yana kama da zunubi na duba, girman kai kuma yana kama da bautar gumaka. Saboda ka ƙi maganar Ubangiji, shi ma ya ƙi ka da zaman sarki.”
For rebellion is as the sin of witchcraft, and stubbornness is as idolatry and teraphim. Because you have rejected the LORD’s word, he has also rejected you from being king.”
24 Sai Shawulu ya ce wa Sama’ila, “Na yi zunubi, na ƙi bin umarnin Ubangiji, na kuma ƙi bin maganarka. Na ji tsoron mutane ne shi ya sa na bi maganarsu.
Saul said to Samuel, “I have sinned; for I have transgressed the commandment of the LORD and your words, because I feared the people and obeyed their voice.
25 Yanzu fa, ina roƙonka ka yafe mini zunubina, ka koma tare da ni, domin in yi wa Ubangiji sujada.”
Now therefore, please pardon my sin, and turn again with me, that I may worship the LORD.”
26 Amma Sama’ila ya ce, “Ba zan koma tare da kai ba. Ka ƙi maganar Ubangiji, Ubangiji kuma ya ƙi ka da zama sarki a bisa Isra’ila.”
Samuel said to Saul, “I will not return with you; for you have rejected the LORD’s word, and the LORD has rejected you from being king over Israel.”
27 Da Sama’ila ya juya zai tafi, sai Shawulu ya kama bakin rigarsa, sai rigar ta yage.
As Samuel turned around to go away, Saul grabbed the skirt of his robe, and it tore.
28 Sama’ila ya ce masa, “Ubangiji ya yage masarautar Isra’ila daga gare ka yau, ya ba wa wani daga cikin maƙwabtanka wanda ya fi ka.
Samuel said to him, “The LORD has torn the kingdom of Israel from you today, and has given it to a neighbour of yours who is better than you.
29 Shi wanda yake Ɗaukakar Isra’ila ba ya ƙarya ko yă canja zuciyarsa, gama shi ba mutum ba ne da zai canja zuciyarsa.”
Also the Strength of Israel will not lie nor repent; for he is not a man, that he should repent.”
30 Shawulu ya ce, “Na yi zunubi. Amma ina roƙonka ka ba ni girma a gaban dattawan mutanena da kuma a gaban Isra’ila, ka koma tare da ni domin in yi wa Ubangiji Allahnka sujada.”
Then he said, “I have sinned; yet please honour me now before the elders of my people and before Israel, and come back with me, that I may worship the LORD your God.”
31 Saboda haka sai Sama’ila ya koma tare da Shawulu, Shawulu kuwa ya yi wa Ubangiji sujada.
So Samuel went back with Saul; and Saul worshipped the LORD.
32 Sa’an nan Sama’ila ya ce, “Kawo mini Agag sarkin Amalekawa.” Agag kuwa ya zo wurinsa daure da sarƙa, yana tunani cewa, “Tabbatacce zancen mutuwa dai ya wuce.”
Then Samuel said, “Bring Agag the king of the Amalekites here to me!” Agag came to him cheerfully. Agag said, “Surely the bitterness of death is past.”
33 Amma Sama’ila ya ce, “Yadda takobinka ya sa mata suka rasa’ya’ya, haka mahaifiyarka za tă zama marar’ya’ya a cikin mata.” Sama’ila kuwa ya kashe Agag a Gilgal a gaban Ubangiji.
Samuel said, “As your sword has made women childless, so your mother will be childless amongst women!” Then Samuel cut Agag in pieces before the LORD in Gilgal.
34 Sai Sama’ila ya tafi Rama, amma Shawulu ya haura zuwa gidansa a Gibeya na Shawulu.
Then Samuel went to Ramah; and Saul went up to his house to Gibeah of Saul.
35 Daga wannan rana Sama’ila bai ƙara saduwa da sarki Shawulu ba, har rasuwar Sama’ila, amma ya yi baƙin ciki sosai a kan Shawulu. Ubangiji kuwa ya damu da ya sa Shawulu ya zama Sarkin Isra’ila ba.
Samuel came no more to see Saul until the day of his death, but Samuel mourned for Saul. The LORD grieved that he had made Saul king over Israel.

< 1 Sama’ila 15 >