< 1 Sama’ila 14 >
1 Wata rana Yonatan ɗan Shawulu ya ce wa saurayin da yake ɗaukar masa makamai, “Zo mu tafi wajen sansanin Filistiyawa a wancan hayi.” Amma bai gaya wa mahaifinsa ba.
2 Shawulu kuwa na zaune a gindin itacen rumman a bayan garin Gibeya a Migron. Tare da shi akwai mutum wajen ɗari shida.
3 A cikinsu akwai Ahiya sanye da efod. Shi yaron Ikabod ɗan’uwan Ahitub ne, ɗan Finehas, ɗan Eli, firist na Ubangiji a Shilo. Ba wanda ya san cewa Yonatan ya tafi wani wuri.
4 A kowane gefe na mashigin da Yonatan ya so yă bi zuwa wurin Filistiyawa, akwai hawa mai tsawo, ana kira ɗaya Bozez, ɗayan kuma ana kira Senet.
5 Hawan da yake arewa yana fuskantar Mikmash, wanda yake kudu kuma yana fuskantar Geba.
6 Yonatan ya ce wa saurayin mai ɗaukan makamai, “Zo mu haye zuwa mashigin mutane marasa kaciyan nan, wataƙila Ubangiji zai yi aiki a madadinmu. Ba abin da zai iya hana Ubangiji yin aikin ceto ta wurin mutane masu yawa, ko ta wurin mutane kaɗan.”
7 Mai ɗaukan makaman ya ce, “Ka yi duk abin da yake zuciyarka. Ci gaba, ina tare da kai gaba da baya.”
8 Yonatan ya ce, “To, zo mu haye zuwa wajen mutanen, mu sa su gan mu.
9 In suka ce mana, ‘Ku tsaya nan har mu zo wurinku,’ za mu dakata inda muke, ba za mu haura wajensu ba.
10 Amma in suka ce mana, ‘Ku haura wurinmu,’ to, sai mu haura, wannan zai zama mana alama cewa Ubangiji ya bashe su a hannunmu.”
11 Sai suka nuna kansu a sansanin Filistiyawa. Sai Filistiyawa suka ce, “Ku duba ga Ibraniyawa suna fitowa daga cikin ramummuka inda suka ɓuya.”
12 Mutanen da suke sansanin suka kira Yonatan da mai ɗaukan makamansa da babbar murya suka ce, “Ku hauro wajenmu, mu kuwa za mu koya muku hankali.” Sai Yonatan ya ce wa mai ɗaukan makamansa, “Biyo ni, gama Ubangiji ya bashe su a hannun Isra’ila.”
13 Sai Yonatan ya hau dutsen da rarrafe, mai ɗaukan makamansa kuwa yana biye. Yonatan ya yi ta fyaɗa Filistiyawa da ƙasa, mai ɗaukan makamansa kuma ya yi ta karkashe su.
14 A wannan karo na farko Yonatan da mai ɗaukan makamansa suka kashe mutum wajen ashirin a wani fili mai fāɗi rabin kadada.
15 Sai tsoro ya kama dukan sojojin Filistiyawa, waɗanda suke cikin sansanin da waɗanda suke fili, har da waɗanda suke waje, da kuma waɗanda suke kai hari, ƙasa ta girgiza. Allah ne ya kawo wannan rikicewa.
16 Masu gadin Shawulu a Gebiya da take a Benyamin suka duba sai ga rundunar Filistiyawa a warwatsewa ko’ina.
17 Sai Shawulu ya ce wa mutanen da suke tare da shi, “Ku ƙidaya mayaƙa ku ga wane ne ba ya nan.” Da suka ƙirga sai suka tarar Yonatan da mai ɗaukan makamansa ba sa nan.
18 Shawulu ya ce wa Ahiya, “Kawo akwatin alkawarin Allah.” (A lokacin akwatin alkawarin yana tare da Isra’ilawa.)
19 Yayinda Shawulu yake magana da firist kuwa, harguwa ya yi ta ƙaruwa a sansanin Filistiyawa. Sai Shawulu ya ce wa firist, “Janye hannunka.”
20 Sa’an nan Shawulu da dukan mutanensa suka taru suka tafi yaƙi. Suka tarar Filistiyawa sun ruɗe suna yaƙi da juna da takubansu.
21 Ibraniyawan da suke tare da Filistiyawa a dā, waɗanda suka bi Filistiyawan zuwa sansanin yaƙinsu, suka juya, suka goyi bayan Shawulu da Yonatan sa’ad da yaƙin ya taso.
22 Sa’ad da dukan Isra’ilawan da suka ɓuya a duwatsu a ƙasar Efraim suka ji labari cewa Filistiyawa suna gudu, sai suka fito suka fafare su.
23 Haka Ubangiji ya kuɓutar da Isra’ila a wannan rana. Yaƙin kuwa ya ci gaba har gaba da Bet-Awen.
24 A wannan rana, Isra’ilawa suka sha wahala ƙwarai domin Shawulu ya sa mutane suka yi rantsuwa cewa, “La’ananne ne mutumin da ya ci abinci kafin fāɗuwar rana, kafin in ɗauki fansa a kan abokan gābana.” Don haka ba mutumin da ya ɗanɗana abinci.
25 Dukan rundunar ta shiga kurmi, sai ga zuma a ƙasa.
26 Da suka shiga ciki kurmin, suka ga zuma tana zubowa, duk da haka ba wanda ya sa yatsansa ya lasa saboda tsoron rantsuwar da suka yi.
27 Yonatan bai san cewa mahaifinsa ya sa mutane suka yi rantsuwa ba. Sai ya sa gindin sandan da yake hannunsa a saƙar zuma, ya kai bakinsa. Nan da nan sai ya ji ƙarfin jiki ya zo masa.
28 Sai wani soja ya gaya masa cewa, “Mahaifinka ya sa kowa ya yi rantsuwa cewa, ‘La’ananne ne mutumin da ya ci abinci kafin fāɗuwar rana!’ Shi ya sa duk sojojin ba su da ƙarfi.”
29 Yonatan ya ce, “Mahaifina ya jefa ƙasar cikin matsala. Duba yadda na ji ƙarfin jiki sa’ad da na ɗanɗana wannan’yar zuma mana.
30 Da yaya zai kasance ke nan da a ce an bar sojoji suka ci abincin da suka ƙwace daga abokan gābansu? Ai, da gawawwakin Filistiyawan da aka kashe sun fi haka.”
31 A ranan nan Isra’ilawa suka yi ta kashe Filistiyawa daga Mikmash har zuwa Aiyalon. Bayan haka gajiya ta kama su sosai saboda yunwa.
32 Sai suka yi warwason ganima, suka kwashe tumaki, da shanu, da maruƙa, suka yayyanka su, suka ci naman ɗanye.
33 Sai wani mutum ya ce wa Shawulu, “Duba, ga mutane suna zunubi ga Ubangiji, suna cin nama da jini.” Shawulu ya ce, “Kun ci amana. Ku mirgino babban dutse zuwa wurina nan da nan.”
34 Sa’an nan ya ce, “Ku tafi ku faɗa wa jama’a duka, su kawo shanu da tumaki a nan, su yayyanka, su ci a nan, don kada su yi wa Ubangiji zunubi da cin nama ɗanye.” Haka nan kowa ya kawo saniyarsa a daren, ya yanka a can.
35 Sa’an nan Shawulu ya gina wa Ubangiji bagade. Wannan ne bagade na farkon da ya gina.
36 Shawulu ya ce, “Mu bi gangara mu fafare Filistiyawa da dare mu washe su har gari yă waye, mu kuma karkashe kowannensu, kada mu bar wani da rai.” Suka ce, “Ka yi duk abin da ka ga ya fi maka kyau.” Amma firist ya ce, “Bari mu nemi nufin Allah tukuna.”
37 Saboda haka Shawulu ya tambayi Allah ya ce, “Mu bi bayan Filistiyawa? Za ka bashe su a hannun Isra’ila?” Amma Allah bai ba shi amsa a ranar ba.
38 Saboda haka Shawulu ya ce, “Ku zo nan dukanku shugabannin rundunoni, mu bincika mu san zunubin da ya kawo rashin amsan nan yau.
39 Muddin Ubangiji wanda ya ceci Isra’ila yana raye, ko da ɗana Yonatan ne ya yi zunubin, dole yă mutu.” Amma ba ko ɗaya daga cikinsu da ya ce uffam.
40 Sai Shawulu ya ce wa dukan Isra’ilawa, “Ku tsaya a can, ni kuma da Yonatan ɗana mu tsaya a nan.” Mutanen suka ce, “Ka yi abin da ya fi maka kyau.”
41 Sa’an nan Shawulu ya yi addu’a ga Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce, “Me ya sa ba ka amsa mini addu’ata a yau ba? Idan wannan laifina ne, ko kuwa na ɗana, Yonatan, ka nuna mana ta wurin Urim, amma idan laifin mutanen ne ka amsa ta wurin Tummim.” Ba a sami mutane da laifi ba, amma ƙuri’a ta fāɗa a kan Yonatan da Shawulu.
42 Shawulu ya ce, “Ku jefa ƙuri’a tsakanina da ɗana Yonatan.” Sai ƙuri’ar ta fāɗa a kan Yonatan.
43 Sai Shawulu ya ce wa Yonatan, “Gaya mini mene ne ka yi.” Yonatan ya ce masa, “Na ɗanɗana zuma kaɗan daga gindin sandanta. Yanzu kuwa dole in mutu!”
44 Shawulu ya ce, “Bari hukunci mai tsanani na Allah yă kasance a kaina, in ba ka mutu ba, Yonatan.”
45 Amma mutane suka ce wa Shawulu, “A ce Yonatan yă mutu bayan shi ya kawo babban nasara a Isra’ila? Faufau, muddin Ubangiji yana raye, ko gashin kansa ɗaya ba zai fāɗi a ƙasa ba, gama abin da ya yi yau, Allah ne yana tare da shi.” Ta haka mutane suka ceci Yonatan daga mutuwa.
46 Sai Shawulu ya daina bin Filistiyawa, suka koma ƙasarsu.
47 Bayan Shawulu ya hau karagar mulkin Isra’ila, ya yi yaƙi da abokan gābansu ta kowane gefe. Mowabawa, Ammonawa, mutanen Edom, sarakunan Zoba, da kuma Filistiyawa. Duk wurin da ya juya, ya hore su.
48 Ya yi jaruntaka sosai, ya ci Amalekawa da yaƙi, ya kuma ceci Isra’ila daga hannuwan waɗanda suka ƙwace musu kaya.
49 ’Ya’yan Shawulu maza su ne, Yonatan, Ishbi, da Malki-Shuwa. Sunan babban’yarsa ita ce Merab, ƙaramar kuma Mikal.
50 Sunan matarsa kuwa Ahinowam,’yar Ahimawaz. Sunan shugaban ƙungiyar sojan Shawulu kuwa Abner ne ɗan Ner, shi Ner kuwa ɗan’uwan mahaifin Shawulu ne.
51 Mahaifin Shawulu, Kish da kuma Ner mahaifin Abner,’ya’yan Abiyel ne.
52 Dukan kwanakin Shawulu sun kasance na yaƙe-yaƙe da Filistiyawa ne. Duk lokacin da Shawulu ya ga ƙaƙƙarfan mutum ko jarumi, sai yă ɗauke shi aikin sojansa.