< 1 Sama’ila 13 >
1 Shawulu yana da shekara talatin sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi sarautar Isra’ila shekara arba’in da biyu.
Saul was thirty years old when he became king, and he reigned over Israel forty-two years.
2 Sai ya zaɓi sojoji dubu uku daga jama’ar Isra’ila. Ya keɓe dubu biyu su kasance tare da shi a Mikmash da kuma a tuddan yankin Betel. Ya kuma bar dubu ɗaya tare da ɗansa Yonatan a Gibeya a yankin zuriyar Benyamin. Sauran sojojin kuwa Shawulu ya sallame su su koma gidajensu.
He chose for himself three thousand men of Israel: Two thousand were with Saul at Michmash and in the hill country of Bethel, and a thousand were with Jonathan in Gibeah of Benjamin. And the rest of the troops he sent away, each to his own home.
3 Yonatan ya kai wa Filistiyawa hari a Geba, sai Filistiyawa suka sami labarin. Sai Shawulu ya sa aka busa ƙaho ko’ina a ƙasar ya ce, “Bari Ibraniyawa su ji!”
Then Jonathan attacked the Philistine outpost at Geba, and the Philistines heard about it. So Saul blew the ram’s horn throughout the land, saying, “Let the Hebrews hear!”
4 Haka kuwa dukan Isra’ila suka ji labari cewa, “Shawulu ya kai hari a ƙasar Filistiyawa, yanzu Isra’ila ta zama abin ƙi ga Filistiyawa.” Aka kira mutane su haɗu da Shawulu a Gilgal.
And all Israel heard the news: “Saul has attacked an outpost of the Philistines, and now Israel has become a stench to the Philistines!” Then the people were summoned to join Saul at Gilgal.
5 Sai Filistiyawa suka taru don su yi yaƙi da Isra’ilawa. Suka fito da kekunan-dawakan yaƙi dubu talatin, da masu hawan dawakai dubu shida, da sojoji masu yawa kamar yashi a bakin teku. Suka tafi Mikmash a gabashin Bet-Awen, suka kafa sansani a can.
Now the Philistines assembled to fight against Israel with three thousand chariots, six thousand horsemen, and troops as numerous as the sand on the seashore. They went up and camped at Michmash, east of Beth-aven.
6 Sa’ad da Filistiyawa suka fāɗa wa Isra’ilawa da yaƙi mai tsanani, suka sa su cikin wani hali mai wuya, sai Isra’ilawa suka ɓuya a kogwanni, da ciyayi, da duwatsu, da ramummuka, da rijiyoyi.
Seeing that they were in danger because their troops were hard-pressed, the men of Israel hid in caves and thickets, among the rocks, and in cellars and cisterns.
7 Waɗansunsu ma suka haye Urdun zuwa ƙasar Gad da Gileyad. Shawulu ya zauna Gilgal, dukan ƙungiyoyi sojojin da suke tare da shi suka yi rawan jiki don tsoro.
Some Hebrews even crossed the Jordan into the land of Gad and Gilead. Saul, however, remained at Gilgal, and all his troops were quaking in fear.
8 Ya jira har kwana bakwai bisa ga lokacin da Sama’ila ya bayar. Amma Sama’ila bai zo Gilgal ba, mutanen Shawulu suka fara watsewa.
And Saul waited seven days for the time appointed by Samuel, but Samuel did not come to Gilgal, and the troops began to desert Saul.
9 Sai ya ce, “Ku kawo mini hadaya ta ƙonawa da hadaya ta salama.” Sai Shawulu ya miƙa hadaya ta ƙonawa.
So he said, “Bring me the burnt offering and the peace offerings.” And he offered up the burnt offering.
10 Daidai yana gama miƙa hadaya ke nan sai Sama’ila ya iso. Shawulu kuma ya fito domin yă yi masa maraba.
Just as he finished offering the burnt offering, Samuel arrived, and Saul went out to greet him.
11 Sama’ila ya ce, “Me ke nan ka yi?” Shawulu ya ce, “Sa’ad da na ga mutane suna watsewa, kai kuwa ba ka zo cikin lokaci ba, ga Filistiyawa kuma suna taruwa a Mikmash,
“What have you done?” Samuel asked. And Saul replied, “When I saw that the troops were deserting me, and that you did not come at the appointed time and the Philistines were gathering at Michmash,
12 sai na yi tunani cewa, ‘Yanzu Filistiyawa za su gangaro su fāɗa mini a Gilgal, ga ni kuma ban riga na nemi nufin Ubangiji ba.’ Shi ya sa ya zama mini tilas in miƙa hadaya ta ƙonawa.”
I thought, ‘Now the Philistines will descend upon me at Gilgal, and I have not sought the favor of the LORD.’ So I felt compelled to offer the burnt offering.”
13 Sama’ila ya ce, “Ka yi wauta da ba ka bi umarnin da Ubangiji Allahnka ya ba ka ba. Da ka yi haka da Ubangiji ya tabbatar maka da sarautar Isra’ila har abada.
“You have acted foolishly,” Samuel declared. “You have not kept the command that the LORD your God gave you; if you had, the LORD would have established your kingdom over Israel for all time.
14 Amma yanzu, masarautarka ba za tă dawwama ba, Ubangiji ya riga ya sami wani wanda zuciyarsa ke ƙauna, ya naɗa shi shugaban mutanensa gama ba ka bi umarnin Ubangiji ba.”
But now your kingdom will not endure; the LORD has sought a man after His own heart and appointed him ruler over His people, because you have not kept the command of the LORD.”
15 Sama’ila ya tashi daga Gilgal ya tafi Gibeya a ƙasar Benyamin. Shawulu kuma ya ƙidaya mutanen da suke tare da shi, yawansu ya kai wajen mutum ɗari shida.
Then Samuel set out from Gilgal and went up to Gibeah in Benjamin. And Saul numbered the troops who were with him, about six hundred men.
16 Shawulu da ɗansa Yonatan da mutanen da suke tare da shi suka zauna a Geba ta Benyamin. Sa’an nan Filistiyawa suka yi sansani a Mikmash.
Now Saul and Jonathan his son and the troops with them were staying in Geba of Benjamin, while the Philistines camped at Michmash.
17 Rundunar mayaƙa uku suka fito daga sansani Filistiyawa. Ɗaya ta nufi Ofra, zuwa ƙasar Shuwal.
And raiders went out of the Philistine camp in three divisions. One headed toward Ophrah in the land of Shual,
18 Runduna guda kuma ta nufi Bet-Horon, ɗayan kuwa ta nufi iyakar da take fuskantar Kwarin Ziboyim wajen jeji.
another toward Beth-horon, and the third down the border road overlooking the Valley of Zeboim facing the wilderness.
19 Ba a sami maƙeri ɗaya a dukan ƙasar Isra’ila ba domin Filistiyawa sun ce, “In ba haka ba Ibraniyawa za su ƙera wa kansu takuba ko māsu.”
And no blacksmith could be found in all the land of Israel, because the Philistines had said, “The Hebrews must not be allowed to make swords or spears.”
20 Saboda haka dukan Isra’ila sukan gangara zuwa wajen Filistiyawa domin su gyara bakin garemaninsu, da fartanansu, da gaturansu, da kuma laujunansu.
Instead, all the Israelites would go down to the Philistines to sharpen their plowshares, mattocks, axes, and sickles.
21 Duk lokacin da za su gyara bakin garmansu da fartanyarsu sai sun biya tsabar azurfa biyu. Haka ma idan za su gyara gatari ko bakunan abin korar shanun noma sai sun biya tsabar azurfa ɗaya.
The charge was a pim for sharpening a plowshare or mattock, a third of a shekel for sharpening a pitchfork or an axe, and a third of a shekel for repointing an oxgoad.
22 A ranar da yaƙi ya tashi, ba a sami wanda yake da takobi ko māshi ba a cikin mutanen da suke tare da Shawulu da Yonatan. Sai dai Shawulu da ɗansa Yonatan kaɗai.
So on the day of battle not a sword or spear could be found in the hands of the troops with Saul and Jonathan; only Saul and his son Jonathan had weapons.
23 Ana nan sai sojojin Filistiyawa suka fita zuwa mashigin Mikmash.
And a garrison of the Philistines had gone out to the pass at Michmash.