< 1 Sama’ila 11 >

1 Nahash mutumin Ammon ya haura ya kewaye Yabesh Gileyad da yaƙi. Dukan mutanen Yabesh suka ce masa, “Ka ƙulla amana da mu, mu kuwa za mu bauta maka.”
ויעל נחש העמוני ויחן על יביש גלעד ויאמרו כל אנשי יביש אל נחש כרת לנו ברית ונעבדך
2 Amma Nahash ya ce, “Zan ƙulla amana da ku kawai a kan sharaɗin cewa zan ƙwaƙulo idon dama na kowannenku, ta haka za a kunyata Isra’ila.”
ויאמר אליהם נחש העמוני בזאת אכרת לכם בנקור לכם כל עין ימין ושמתיה חרפה על כל ישראל
3 Dattawan Yabesh suka ce masa, “Ka ba mu kwana bakwai don mu aika manzanni a dukan ƙasar Isra’ila idan ba mu sami wanda zai cece mu ba, za mu ba da kanmu gare ka.”
ויאמרו אליו זקני יביש הרף לנו שבעת ימים ונשלחה מלאכים בכל גבול ישראל ואם אין מושיע אתנו ויצאנו אליך
4 Da manzannin suka zo Gibeya garin Shawulu, suka gaya wa mutane wannan sharaɗin, suka yi kuka mai zafi.
ויבאו המלאכים גבעת שאול וידברו הדברים באזני העם וישאו כל העם את קולם ויבכו
5 A daidai wannan lokacin kuwa Shawulu yana dawowa daga gona tare da shanunsa na noma, sai ya ce, “Me ya faru, mutane suna kuka haka?” Sai suka faɗa masa abin da mutanen Yabesh suka faɗa musu.
והנה שאול בא אחרי הבקר מן השדה ויאמר שאול מה לעם כי יבכו ויספרו לו--את דברי אנשי יביש
6 Da Shawulu ya ji, sa Ruhun Allah ya sauko a kansa da iko, ya husata ƙwarai.
ותצלח רוח אלהים על שאול בשמעו (כשמעו) את הדברים האלה ויחר אפו מאד
7 Ya ɗauki shanu biyu, ya yayyanka su gunduwa-gunduwa, ya aika da su ko’ina a ƙasar Isra’ila ta wurin manzanni cewa, “Duk wanda bai fita ya bi Shawulu da Sama’ila ba, haka za a yi da shanunsa.” Mutanen suka ji tsoron Ubangiji suka fita gaba ɗaya kamar mutum guda.
ויקח צמד בקר וינתחהו וישלח בכל גבול ישראל ביד המלאכים לאמר אשר איננו יצא אחרי שאול ואחר שמואל כה יעשה לבקרו ויפל פחד יהוה על העם ויצאו כאיש אחד
8 Mutanen Isra’ila sun kai dubu ɗari uku. Mutanen Yahuda kuma dubu talatin, sa’ad da Shawulu ya tara su a Bezek.
ויפקדם בבזק ויהיו בני ישראל שלש מאות אלף ואיש יהודה שלשים אלף
9 Suka ce wa’yan aikan da suka zo, “Ku faɗa wa mutanen Yabesh Gileyad, ‘Gobe, kafin rana tă yi zafi, za ku sami ceto.’” Sa’ad da’yan aikan suka tafi, suka ba da saƙon nan ga mutanen Yabesh, sai suka farin ciki.
ויאמרו למלאכים הבאים כה תאמרון לאיש יביש גלעד מחר תהיה לכם תשועה בחם (כחם) השמש ויבאו המלאכים ויגידו לאנשי יביש--וישמחו
10 Suka ce wa Ammonawa, “Gobe za mu miƙa wuya gare ku, ku kuma yi duk abin da kuka ga dama.”
ויאמרו אנשי יביש מחר נצא אליכם ועשיתם לנו ככל הטוב בעיניכם
11 Gari yana wayewa, sai Shawulu ya raba mutane kashi uku, a sa’a ta ƙarshe na daren sai suka fāɗa wa sansanin Ammonawa, suka kuma karkashe su har lokacin da rana ta yi zafi. Waɗanda suka kuɓuce kuwa suka warwatsu, har babu biyunsu da aka bari tare.
ויהי ממחרת וישם שאול את העם שלשה ראשים ויבאו בתוך המחנה באשמרת הבקר ויכו את עמון עד חם היום ויהי הנשארים ויפצו ולא נשארו בם שנים יחד
12 Sai mutane suka ce wa Sama’ila, “Su wa suka ce, ‘Shawulu zai yi mulkinmu?’ A kawo mana su mu kashe.”
ויאמר העם אל שמואל מי האמר שאול ימלך עלינו תנו האנשים ונמיתם
13 Shawulu ya ce, “Ba wanda zai mutu yau, gama Ubangiji ya kuɓutar da Isra’ila a wannan rana.”
ויאמר שאול לא יומת איש ביום הזה כי היום עשה יהוה תשועה בישראל
14 Sai Sama’ila ya ce wa mutane, “Ku zo mu tafi Gilgal, a can za a yi wankan sarauta.”
ויאמר שמואל אל העם לכו ונלכה הגלגל ונחדש שם המלוכה
15 Don haka dukan mutane suka tafi Gilgal, suka tabbatar da Shawulu sarki a gaban Ubangiji. A can suka miƙa hadaya ta salama a gaban Ubangiji, Shawulu kuwa da dukan Isra’ila suka yi babban liyafa.
וילכו כל העם הגלגל וימלכו שם את שאול לפני יהוה בגלגל ויזבחו שם זבחים שלמים לפני יהוה וישמח שם שאול וכל אנשי ישראל עד מאד

< 1 Sama’ila 11 >