< 1 Bitrus 5 >

1 Zuwa ga dattawan da suke cikinku, ina roƙo a matsayin ɗan’uwanku dattijo, mashaidin shan wahalar Kiristi wanda kuma shi ma zai sami rabo cikin ɗaukakar da za a bayyana.
As a fellow elder, a witness of Christ’s sufferings, and a partaker of the glory to be revealed, I appeal to the elders among you:
2 Ku zama makiyayan garken Allah da yake a ƙarƙashin kulawarku, kuna hidima kamar masu kula, ba kan dole ba, sai dai da yardar rai, yadda Allah yake so ku zama; ban da kwaɗayin kuɗi, sai dai marmarin yin hidima;
Be shepherds of God’s flock that is among you, watching over them not out of compulsion, but because it is God’s will; not out of greed, but out of eagerness;
3 ban da nuna iko a kan waɗanda aka danƙa muku amana, sai dai ku zama gurbi ga garken.
not lording it over those entrusted to you, but being examples to the flock.
4 Sa’ad da kuwa Babban Makiyayin ya bayyana, za ku karɓi rawanin ɗaukaka marar koɗewa.
And when the Chief Shepherd appears, you will receive the crown of glory that will never fade away.
5 Samari, ku ma, ku yi biyayya ga waɗanda suka girme ku. Dukanku, ku yafa sauƙinkai ga juna, domin, “Allah yana gāba da mai girman kai, amma yakan yi alheri ga mai sauƙinkai.”
Young men, in the same way, submit yourselves to your elders. And all of you, clothe yourselves with humility toward one another, because, “God opposes the proud, but gives grace to the humble.”
6 Saboda haka, ku ƙasƙantar da kanku a ƙarƙashin hannun Allah mai ƙarfi, don yă ɗaukaka ku a lokacin da ya ga dama.
Humble yourselves, therefore, under God’s mighty hand, so that in due time He may exalt you.
7 Ku danƙa masa dukan damuwarku, domin shi ne yake lura da ku.
Cast all your anxiety on Him, because He cares for you.
8 Ku zama masu kamunkai, ku kuma zauna a faɗake. Abokin gābanku, Iblis yana kewayewa kamar zaki mai ruri, yana neman wanda zai cinye.
Be sober-minded and alert. Your adversary the devil prowls around like a roaring lion, seeking someone to devour.
9 Ku yi tsayayya da shi, kuna tsayawa daram cikin bangaskiya, domin kun san cewa’yan’uwanku ko’ina a duniya suna shan irin wahalolin nan.
Resist him, standing firm in your faith and in the knowledge that your brothers throughout the world are undergoing the same kinds of suffering.
10 Allah mai dukan alheri, wanda ya kira ku ga madawwamiyar ɗaukaka cikin Kiristi, bayan kun sha wahala na ɗan lokaci, shi da kansa zai raya ku, yă kuma sa ku yi ƙarfi, ku kahu, ku kuma tsaya daram. (aiōnios g166)
And after you have suffered for a little while, the God of all grace, who has called you to His eternal glory in Christ, will Himself restore you, secure you, strengthen you, and establish you. (aiōnios g166)
11 Gare shi bari iko yă tabbata har abada abadin. Amin. (aiōn g165)
To Him be the power forever and ever. Amen. (aiōn g165)
12 Da taimakon Sila, wanda na ɗauka a matsayin ɗan’uwa mai aminci, na rubuta muku a taƙaice, ina ƙarfafa ku ina kuma shaida muku cewa wannan shi ne alherin Allah na gaske. Ku tsaya daram a cikinsa.
Through Silvanus, whom I regard as a faithful brother, I have written to you briefly, encouraging you and testifying that this is the true grace of God. Stand firm in it.
13 Ita wadda take a Babilon, zaɓaɓɓiya tare da ku, tana gaishe ku, haka ma ɗana Markus.
The church in Babylon, chosen together with you, sends you greetings, as does my son Mark.
14 Ku gai da juna da sumbar ƙauna. Salama gare ku duka da kuke cikin Kiristi.
Greet one another with a kiss of love. Peace to all of you who are in Christ.

< 1 Bitrus 5 >